shonaff's Reading List
6 stories
RAINA (The beautiful princess) by Aysha2017
Aysha2017
  • WpView
    Reads 40,663
  • WpVote
    Votes 1,734
  • WpPart
    Parts 30
Raina yarinyace data fito daga gidan saurauta amma daga bisani aka dauketa cik saboda wasu manufofi idan kuka biyoni zakuji tsantsar madaran labarin.
❤MAHBUBI❤ by aishaganyu
aishaganyu
  • WpView
    Reads 64,889
  • WpVote
    Votes 2,284
  • WpPart
    Parts 30
Labari akan rayuwar Amna da Adil da yadda suka tsinci kansu... ku biyo mu kusha labari...
♡MAFARIN SO♡ by Rerbeeart_sk
Rerbeeart_sk
  • WpView
    Reads 118,151
  • WpVote
    Votes 5,958
  • WpPart
    Parts 41
ƙaddarace ke yawan haɗasu, kuma a kowanne lokaci suka haɗu sai sunyi faɗa a tsakaninsu, a haka har tsautsayin da yayi dalilin aurensu ya faru, ko ya zaman nasu zai kasance?
SOYAYYA CE by MaryamerhAbdul
MaryamerhAbdul
  • WpView
    Reads 30,112
  • WpVote
    Votes 1,315
  • WpPart
    Parts 12
"Zan dawo miki pretty, Elmansoor is yours, yours alone, banson kukan nan kina karya min zuciya in kinayi, let's be strong, ba'a tab'a samun abu meh kyau sai ansha wahala. Zan tafi in baki sararin yin duk yanda kikeso dan bazan iya ganinki haka ba Aisha, bazan iya jurewa ba". B'angaren zuciyarsa ya d'aura hannunsa akai ya furta can ciki, muryarsa cike da rauni. "A nan nake jin duk kukan nan da kikeyi, bana son in mutu ban samu Aisha ba, bana son in tafi ban samu damar kasancewa da farin cikina cikin inuwa guda ba, you mean everything to me, ina sonki fiye da yanda kike zato".
FAIROOZ LITTAFI NA FARKO  by ashnurpyaar
ashnurpyaar
  • WpView
    Reads 14,378
  • WpVote
    Votes 1,201
  • WpPart
    Parts 25
Tana tab'awa kuwa sai taji ta zuuuuuuuuuuu....Gaba ɗayanta hasken yazu k'ota zuwa cikin littafin, ma 'ana ta shige cikin littafin datake kallon hotuna cikinsa. Ga mamakin maryam sai ta ganta ta ɓullo cikin wata sabuwar duniya daban, da irin wacce muke ciki, domin dai inda ta tsinci kanta da ta duba sararin samaniyan-sa saita gansa kore da blue(shuɗi) sharrrr...." wannan wace irin duniya ce kuma" ? Maryam ta duba inda take gaba da baya! Gabas da yamma bataga kowa ba, daga can gefe guda kuma ta hango littafin da take kallo yana nan kamar yanda yake bai canza daga pagin data buɗe ba. "Ikon Allah! taya akayi nazo nan kuma?" lokaci ɗaya tsoro ya ziyarci zuciyarta, Nan take tafara karanto addu'oi a bakinta, bakin nata har rawa yakeyi saboda tsoro da firgico..... Tafiya tafara zuwa inda littafin yake, ta kai hannu domin ta d'auka, sai littafin ya matsa daga inda yake, tasake kai hannu karo na biyu nan ma littafin yasake matsawa, batareda kuma taga wanda yake taɓa littafin ba, zuwa yanzu Maryam taji tsoro yayi k'aura daga zuciyarta, dan haka sai ta cigaba dabin littafin, babban burinta shine: tasamu damar rik'e littafin ko da ta hakan Allah zai sa taga hanyar da zata maida ita duniyar data baro. Ash'nur pyar mera dil.
KE NAKE SO by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 182,970
  • WpVote
    Votes 12,533
  • WpPart
    Parts 19
#1 sacrifice 21/08/2020 #5 in romance 27/09/2016 "Malam, ka yi kuskure, idan ka na tunanin zaka canza min ra'ayina a minti biyar". "Ko za ki gwada ki gani?" Ya tambaya, yana murmushi, ita ta rasa ma yadda aka yi ya iya murmushi, da dai ba ta ganin hakan a tare da shi. Ta kan dauka shi haka Allah ya halitto shi, duk lokacin da ta samu ganinsa a rayuwarta, sau daya ta taba ganin murmushinsa, ko ba da ita ba, idan tana wurin, baya yin murmushi da kowa. Ta danne zuciyarta, sannan ta zauna, don ita ko ganinsa ma ba ta son yi, bayan abin da ya yi jiya. "Tambaya na ke son na miki. Shin Alhaji Yusuf da ki ke son ki aura, kin tabbata ya damu da farin cikin ki, ko kuwa bacin ranki?" "Wace irin tambaya ce wannan?" Kallonta yake yi kamar zai hadiyeta "Ki amsa min, me ya sani game dake?" Kafin ta ba shi amsa ya ci-gaba. "Shin ya san cewa ba ki son turare mai karfi, saboda ki na da Allergy, ko kuwa ya san idan kin sha ruwan sanyi ciwon Agalawarki na tashi? Ko kuwa kin fi son kasancewa cikin mutane ki yi walwala. Ya san da cewa ba ki amfani da Salary dinki, sai dai ki yi hidima wa wadanda ki ke so?" Ya numfasa cikin murya kasa-kasa ya-ce. "Ya san cewa ba kya son shi?" This is the limit. Ya kai ta makura. "Yaya aka yi ka san duk wannnn a tare da ni?" "Saboda Jidda, na sanki. Na san komai game dake every. Little. Detail. na sani". Ya fada cikin wani yanayi mai tsinka jiyoyin jikin mai saurare. "Well, abinda ba ka sani ba, shi ne ka bata kan batun Alhaji Yusuf, domin kuwa SHI NA KE SO!