Mi work
3 stories
Juyayi by Fatima_writes_
Fatima_writes_
  • WpView
    Reads 571
  • WpVote
    Votes 64
  • WpPart
    Parts 6
"Dija kin san na hadu da Amin din nan da ke turo min messages yau? Kin ga hotonsa. " Ta fada tana nuna wa 'kanwar tata hotonsa a wayarta.Bata lura da yanayin da suka shiga ba ,ko da yake ba za ta lura ba saboda Dija ta yi saurin goge hawayenta yayin Abbansu da dawowarsa kenan ya saki labulen parlourn ya nufi motarsa cikin mamaki da tsananin tashin hankali. ***** "Beautiful boy ba zan iya rayuwa ba, na kusa mutuwa in barku... " Ya yi saurin toshe mata baki yana fadin "Handsome girl ki daina fadin haka Amin na ki ne na miki alkawari" Kakanta ya fada cikin rarrashi da kwantar da hankali. "Ba za ka gane ba Handsome boy yayata ke sanshi ta ina zan sameshi ?Ko mutuwa zan yi sau dubu dole zan kyale mata shi ta yi min komai a rayuwa. " Itama ba su lura da ita ba, haka ta saki labulen ba tara da ta gaisa da prince din nata ba duk ko da 'dokin da take idan har zai kawo musu ziyara. Abinda da take ji a yanzu ya fi karfin gaisawa da kakan nata.
Najma da Mahir by Fatima_writes_
Fatima_writes_
  • WpView
    Reads 10,231
  • WpVote
    Votes 600
  • WpPart
    Parts 19
"Ga wannan sunanshi 'Dan aike' domin ko in ya je dawowa ya ke, an hadashi ne da majinar damisa mai mura,jelar'beran da bai taba satar daddawa ba,da kuma hakorin muzuru mai kimanin kwana cassa'in, ya yarda ke tun bai san miye yarda ba,a coffee za ki 'diga, 'digo biyu ina jaddadawa!!!, ki bawa Anisa ita zata hada ta kai masa, ba so ba ko zuciyarshi ce a jikanta ba zai aure ta ba, Anisa zai aura,amma duk ranar da Najma ta furta mai da kanta tana son shi ki Kuka da kanki don babu Ruwan Boka Mugu" Ya fada yana zare idonshi da ya sha farin kwalli. *** Gishiri ya ji a bakinshi mai hade da ruwa, lokacin ne ya gane ba ita take bu'katar handkerchief din da ya bata ba shi ke bukata, yaushe rabon da ya yi kuka? Tun ranar da ta yi wani ciwon ciki mai cike da azaba, ya bawa kanshi amsa yana goge majinar da ta samu damar zubo masa, zuciyar sa ce ta kuma tarwatsewa a karo na ba adadi jin kalaman da ke fitowa daga bakinta dukda cewa a wurinshi sun fi kama da aman wuta mai zafi, so yake ya ce mata 'I love you ' kalmomin da tun bata fahimtar magana yake fada mata saidai yau ya kasa,wani abu mai kama da Zuma rock ya danne masa harshensa da zuciyarshi kuma sai bitarsu yake kamar almajiri ya rike allonsa. Dumm zuciyarshi ta buga a karo na uku tun bayan da ta fara magana,bakin shi ya bude wanda ya yi sanadiyyar zubowar yawun da bai san da shi ba a yayinda ya cigaba da kallonta kamar wanda ya ga Tinkiya da'Ture ka ga tsiya' daurin yan mata masu ji da kansu. *** "Haba Yayana 'dan baki!Ya kake so in yi da rayuwata ne?Na san ba Anisa kake so ba ni kake so ba sai ka fada min ba wallahi na sani, amma ka ki ka nemi aurena tun tuni? Mai kake jira? Hmmm, Ya Mir me ya sa ka canza min gaba daya? na yi ta kokarin in jure na kasa saboda zuciyata ba zata iya ba,Nisanta kanka da kake yi da ni 'kara tarwatsa min zuciya yake, Ka yi sake har Abbu ya hada aurena da Ya Jamil,gobe za a daura tunda haka ka zaba you have 24 freaking hours to decide, abinda na sani shi ne I LOVE YOU WALLAHI DA GASKE..."
Zara by Fatima_writes_
Fatima_writes_
  • WpView
    Reads 2,251
  • WpVote
    Votes 337
  • WpPart
    Parts 21
Her? Oh how he missed her. He thought life was perfectly perfect when he met her, alas, it was an illusion,a freaking perfect one. She was Allah's gift to him that he would forever cherish. Alhamdulillah. He was shattered,yet she picked him piece by piece. He was broken,but she revived him. He was bored,and she entertained him. He was doomed,but being a twinkling shining star, she shone his way. He was lost, and she found him. He was hopeless but she gave him hope. He locked his heart but she got the key. He was distressed and he found solace in her. He got problems,she solved them. All in Allah SWT's will It's all about Zara