iyanhouse's Reading List
7 stories
TSAKANINMU by LubnaSufyan
LubnaSufyan
  • WpView
    Reads 2,325
  • WpVote
    Votes 114
  • WpPart
    Parts 1
Su uku suka kulla yarjejeniyar, sirri ne da ya kamata ya tsaya a tsakanin su ukun kawai, ko da ta kama zaren ta ja shi, ta hange shi da tsayin da ta kasa ganin karshen shi, burinta ne mafarin, yarjejeniyar da sirrin duk a tsakiya suke, karshen kuma sai ta dauka cikar burinta ne, shi tayi hasashe, shi ta shiryawa zuciyarta karba, ko a mugun mafarki bata hango burinta zai ci karo da kaddarar da ta dauketa tayi sama da ita, ta girgiza kafin ta tikota da kasa ba, faduwar da tayita akan sirrin da take ta riritawa, data mike kuma sai ya koma sama kafin tayi wani yunkuri ya dawo ya binneta da ranta!
ALKALAMIN KADDARA.  by LubnaSufyan
LubnaSufyan
  • WpView
    Reads 45,621
  • WpVote
    Votes 2,110
  • WpPart
    Parts 14
Karka nuna dan yatsa akan kalar rubutun da Alkalamin kaddara yaima waninka. Baya tsallake kowa, naka a rubuce yake tun kamun samuwarka. Karkace zakai dariya akan kalar shafin rubutun Alkalamin kaddarar wani, a duk minti daya na rayuwarka sabon shafi yake budewa, waya san ko cikin shafukanka akwai rubutun dayafi nashi muni. Karka saki jiki da yawa, komai zai iya canzawa. Zuwa yanzun kowa yasan ban yarda da Happily ever after ba, idan har shi kake buqata, ALKALAMIN KADDARA ba littafin ka bane ba. Yan gidan Tafeeda da Shettima zasu taba rayuwarku kaman yanda suka taba tawa. Bance akwai sauqi a cikin tasu tafiyar ba. Banda tabbas akan abubuwan da zakuci karo dashi in kuka biyoni a wannan tafiyar. Tabbaci daya nake dashi, ba zaku taba dana sani ba IN SHA ALLAH. #AnaTare #VOA #FWA #TeamAK
Zanen Dutse Complete✓ by Aysha-Shafiee
Aysha-Shafiee
  • WpView
    Reads 185,244
  • WpVote
    Votes 25,414
  • WpPart
    Parts 35
#1 in Aure 19/09/2020 #1 in Sarauta 19/09/2020 #2 in Halal Romance 19/09/2020 Ta riga ta san duk wata tarin ma'ana ta k'addara, walau mai kyau ko akasinta. Kamar kowa abinda bata sani ba shine... Me cece tata k'addarar? Yaushe zata fuskance ta? A wane yanayi zata zo? Mai kyau? Ko akasin haka? Wad'annan tambayoyin suke yawo kullum cikin kanta, da su take kwana take tashi, cikin tsumayin lokacin da alk'alami ya bushe akansa. Don wata k'addarar tamkar ZANEN DUTSE ce... Babu wani abu da ya isa ya canja ta!
RAI DA KADDARA by LubnaSufyan
LubnaSufyan
  • WpView
    Reads 78,127
  • WpVote
    Votes 7,816
  • WpPart
    Parts 59
Daada, Ku saka mata Munawwara, ku kira ta da Madina. Watakila albarkacin sunayen biyu rayuwar da bata da zabi a kanta ta zo mata da sauki ko yaya ne. Zan so kaina a karo na biyu, ku fada mata mahaifiyarta ta sota a watanni taran zamanta a cikinta, ko ba zata yarda ba Daada ki fada mata ta yafe mun, ki bata hakuri na yanda zata kare sauran kwanakin ta a duniya tana biyan zunuban mahaifanta. Kuma ku fada mata sunan baban ta Kabiru, yanayin haihuwar ta ba zai canza cewa ita din jinin shi bace ko da bata da gadon shi. Ke ma ki yafe mun, kiyi mun addu'a ko da rayuwa ba zata sake hada fuskokin mu ba. Yelwa.
ABDULKADIR by LubnaSufyan
LubnaSufyan
  • WpView
    Reads 377,320
  • WpVote
    Votes 31,684
  • WpPart
    Parts 38
"Banbancin kowacce rana na tare da yanda take sake kusantani da ganinki" #Love #Family #Military #LubnaSufyan
ƘWAI cikin ƘAYA!! by BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    Reads 1,503,520
  • WpVote
    Votes 121,604
  • WpPart
    Parts 106
Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wasu a cikin matsalolin zuminci, gidajen aurenmu, Tsaro, rikita-rikita, harma da ruguntsumi. Kai lamarinfa ba'a cewa komai, mai karatune kawai zai banbance tsakanin aya da tsakkuwar zancena bayan mun tsunduma cikin labarin tsundum