Uwaish
58 stories
Zanen Dutse Complete✓ by Aysha-Shafiee
Aysha-Shafiee
  • WpView
    Reads 185,090
  • WpVote
    Votes 25,414
  • WpPart
    Parts 35
#1 in Aure 19/09/2020 #1 in Sarauta 19/09/2020 #2 in Halal Romance 19/09/2020 Ta riga ta san duk wata tarin ma'ana ta k'addara, walau mai kyau ko akasinta. Kamar kowa abinda bata sani ba shine... Me cece tata k'addarar? Yaushe zata fuskance ta? A wane yanayi zata zo? Mai kyau? Ko akasin haka? Wad'annan tambayoyin suke yawo kullum cikin kanta, da su take kwana take tashi, cikin tsumayin lokacin da alk'alami ya bushe akansa. Don wata k'addarar tamkar ZANEN DUTSE ce... Babu wani abu da ya isa ya canja ta!
KAMBUN SADAUKANTAKA by MSKutama87
MSKutama87
  • WpView
    Reads 6,302
  • WpVote
    Votes 258
  • WpPart
    Parts 6
labari ne akan wani gwarzon jarumi fasa taro wanda yake da burin dauko kayan yakin wata mashahuriyar bokanya domin yazama sadaukin sadaukan duniya amma sai dai kash duk da ya samu damar dauko wannan kaya bai samu damar daukar kambun sadaukan duniya ba sakamakon cin karo da yayi da wata bakuwar jaruma ma'abociyar sabon addini😁
A JINI NA TAKE by Aishatuh_M
Aishatuh_M
  • WpView
    Reads 69,904
  • WpVote
    Votes 3,092
  • WpPart
    Parts 12
Labari ne daya kunshi masarautu biyu; Masarautar Katsina, wacce take cikin Nigeria da kuma Masarautar Damagaran, wacce take cikin Kasar Niger. Labarin yayi duba ne da rayuwar Yarima Bilal, wanda rashin magana da miskilanci ya kanja ya shiga tarun matsaloli, wanda hakan yake haifar mashi da auren Zeenah Kabir Muhammad. Diyar Bafade da kuma baiwa. Me zai faru a rayuwar auren da aka hada miskili da kuma masifaffiya? Wanda dama tun farkon haduwarsu da masifa aka fara har yakai ga ya kure hakurinta ta sharara mashi maruka biyu? Shin ko zasu samu zaman lafiya kuwa? Bilal wanda ya kasance zuciyarshi a kulle take tun bayan rasuwar mahaifiyarshi zai bude ma Zeenah ita? Ya rayuwa zata basu bayan Zeenah ta fada soyayyarshi sai kwatsam Juwairiyya ta kunno kai? Wane hali Bilal zai shiga a lokacin da Fulani ta bankado wani tsohon sirri dake tsakaninsu? Fulani fah? Wacce take uwar gida kuma mai kula da hidimomin Masarautar Katsina gaba daya? Zata rufe sirrin data gano tsakanin Zeenah da Bilal dan gujewa tarwatsewar farin cikinsu? Abu daya ne zai kai ga na biyu, wanda har Bilal zai tsinci kanshi an mashi shamaki da Masarautar Katsina, hakan zai dangantashi da Masarautar Damagaran! Ku biyo Yar Malumfashi domin jin yadda labarin zai kasance.
..... Tun Ran Zane  by Gimbiya229
Gimbiya229
  • WpView
    Reads 97,379
  • WpVote
    Votes 7,989
  • WpPart
    Parts 42
No 1 in General Fiction on 21 September. A lokaci guda duniya ta yi mata juyi mai zafin gaske. A lokacin rayuwa ta kawo mata zabi mai cike da hatsari da nadama. Ta yi watsi da duk wata fata, ta dakatar da duk wani mafarki....tun da dama ai mafarki na wadan da suka yi barci ne. Duk da hakan, Hindu ba ta cire rai ga samun Rahamar Allah (SWT) ba, ko da kuwa zai zo ne a sigar kyakkyawan mutumin da zai kara jijjiga duniyar ta sannan ya dasa kaunar sa cikin zuciyar ta a lokacin da ita kan ta ta yanke kauna ga samun hakan. Daga ranar da ta amince son sa ya shige ta ta san ba makawa, tun ran gini, ran zane!
Kudiri by Gimbiya229
Gimbiya229
  • WpView
    Reads 170,523
  • WpVote
    Votes 12,629
  • WpPart
    Parts 39
Hausa story of love, commitment and sacrifice. Yusuf and Asiya belong to different classes with nothing in common. Well, except for humanity. An incident had occurred which brought them together. Will their shared sacrifice bring them happiness and perhaps, everlasting love?
Akan So by LubnaSufyan
LubnaSufyan
  • WpView
    Reads 333,958
  • WpVote
    Votes 27,149
  • WpPart
    Parts 51
"Tun daga ranar da ka shigo rayuwata komai ya dai daita" Da murmushi a fuskarshi yace "Bansan akwai abinda na rasa a tawa rayuwar ba sai da na mallake ki"
AMAREN BANA by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 143,748
  • WpVote
    Votes 9,338
  • WpPart
    Parts 17
#9 in romance on 05/09/2016 "Wai ina son ki fada min, me yake damun ki ne, da za ki haddasa irin wannan fitina, sannan ki zauna lafiya, kamar ba abinda ya faru?" Dubansa ta yi a sanyaye, sannan ta-ce. "Ina da dalilina." "Wane irin dalili ne, zai sa ki na ji, ki na gani auren iyayenki ya mutu? Idan banda irin gurguwar tunani irin naki? Ashe ki na da halin yin gyara a wannan al'amari, ba za ki yi ba?" Mikewa ya yi daga kan kujerar zai tafi, da sauri ta kamo bakin rigarsa, ya tsaya, ganin zai saurareta, ya sa ta sakar masa riga. "An fada maka ni ma ina jin dadin ganinsu da na ke yi a haka ne? Sam, ba son raina bane, amma na daure na kauda kaina, saboda mu kawar da gagarumar matsalar da ta fi wannan. Na san halin Momi, tana da fada, tana da rashin son gaskiya, amma kuma haka tana da saurin nadama, na san za ta nemi afuwa, kuma Abba zai saurareta. Sai dai wannan tafiyar, dole ka taimaka ka ba ni goyon baya, don mu shawo kan al'amarin nan tare." Kallonta ya yi, ita ma duk ta jikkata, ta jejjeme ta zama wata iri, tabbas yadda take ji haka yake ji, koma fiye, don bayan baya sonta, ya tsani uwarta, sannan yana mutuwar son Meena. "Ki yi hakuri, amma ba zan iya aurenki ba." Ranta ya baci kwarai, har ya juya zai fita ta-ce. "Saboda me ya sa ba za ka iya aure na ba? Saboda me ya sa ban kai matsayin na zamo matarka ba?" "Ki fada min, ta yaya zan iya zama dake, alhali ki na matsayin 'yar matar da na tashi da tsanarta a zuciyata?" "Wane irin dalili zai sa maka tsanar mahaifiyata, har da zai sa ni ba za ka iya aurena ba?" Shiru ta yi don ta ji dalilin wannan tsanar.
BAN SAN SHI BA PART 1. Part 2 Of The Book Is On Okadabooks.com  by Deejahabdul
Deejahabdul
  • WpView
    Reads 132,573
  • WpVote
    Votes 4,799
  • WpPart
    Parts 37
Part 2 of the book is on okadabooks.com #1 in Mystery/Thriller 5 February,2017 #2 in Mystery/Thriller 24 july,2017 NO JUMPING, NO TRANSLATING THIS BOOK INTO ANY LANGUAGE, NO COPYING AND SHARING MY STORY. ANY SORT OF PLAGIARISM IS NOT ALLOWED ON MY STORY. DOING SO WILL LEAD TO THE BANNING OF THE STORY FROM WATTPAD COMPLETELY. HOPE ZA'A KIYAYE. BANYARDA A KWASHE KO A JUYAMIN LABARI TA KOWACCE HANYA BA. BANYARDA AMIN SHARING LABARI A KO'INA BA. YIN HAKAN ZAISA NA TSAYARDA LABARIN KUMA NA CIRESHI GABAD'AYA DAGA WATTPAD. HOPE ZA'A KIYAYE.
KE NAKE SO by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 183,061
  • WpVote
    Votes 12,551
  • WpPart
    Parts 19
#1 sacrifice 21/08/2020 #5 in romance 27/09/2016 "Malam, ka yi kuskure, idan ka na tunanin zaka canza min ra'ayina a minti biyar". "Ko za ki gwada ki gani?" Ya tambaya, yana murmushi, ita ta rasa ma yadda aka yi ya iya murmushi, da dai ba ta ganin hakan a tare da shi. Ta kan dauka shi haka Allah ya halitto shi, duk lokacin da ta samu ganinsa a rayuwarta, sau daya ta taba ganin murmushinsa, ko ba da ita ba, idan tana wurin, baya yin murmushi da kowa. Ta danne zuciyarta, sannan ta zauna, don ita ko ganinsa ma ba ta son yi, bayan abin da ya yi jiya. "Tambaya na ke son na miki. Shin Alhaji Yusuf da ki ke son ki aura, kin tabbata ya damu da farin cikin ki, ko kuwa bacin ranki?" "Wace irin tambaya ce wannan?" Kallonta yake yi kamar zai hadiyeta "Ki amsa min, me ya sani game dake?" Kafin ta ba shi amsa ya ci-gaba. "Shin ya san cewa ba ki son turare mai karfi, saboda ki na da Allergy, ko kuwa ya san idan kin sha ruwan sanyi ciwon Agalawarki na tashi? Ko kuwa kin fi son kasancewa cikin mutane ki yi walwala. Ya san da cewa ba ki amfani da Salary dinki, sai dai ki yi hidima wa wadanda ki ke so?" Ya numfasa cikin murya kasa-kasa ya-ce. "Ya san cewa ba kya son shi?" This is the limit. Ya kai ta makura. "Yaya aka yi ka san duk wannnn a tare da ni?" "Saboda Jidda, na sanki. Na san komai game dake every. Little. Detail. na sani". Ya fada cikin wani yanayi mai tsinka jiyoyin jikin mai saurare. "Well, abinda ba ka sani ba, shi ne ka bata kan batun Alhaji Yusuf, domin kuwa SHI NA KE SO!
UMM ADIYYA (Read Full Book On okada) by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 109,710
  • WpVote
    Votes 2,946
  • WpPart
    Parts 7
#6 in Romance 14/04/2017 Tunda take bata taba ganin mugun mutum marar kunya irin Zaid Abdurrahman ba. Ta so ta juya amma ganin su Maami yasa ta fasa ta shigo falon ta gaishe su sama-sama don tare suke da yayanta Saadiq. Har ma yana tambayarta "Ummu A. da fatan dai wadannan basu baki wahala a wurin aikin?" Murmushi tayi har sai da kumatunta ya loba sannan tace "Mutanen da suka bini har da roko saboda na musu aiki ba sau daya ba ba sau biyu ba, ai kaga bazasuyi garajen bani wahala ba, don haka ina aikina cikin kwanciyar hankali with full amenities. Ko ba haka ba?" Ta fada cikin dai murmushinta hade da harde hannayenta saman kirjinta. Idanunsa ya zuba mata tamkar mai karantar duk wani motsi da ruhinta yakeyi, "Saadiq, dole mu kula da Adiyya, saboda ko ba komai ta san yanda take amfani da kwakwalwarta, she's very smart." Ya kare maganarsa cikin murmushi. Tsumewa tayi hade da aika masa kallon banza, "Dole kace kuna kula da Adiyya, banda dan karan wuyar da kuke bani me kuke yi? kullum nayi aiki sai an kwakulo kuskure a ciki, ko me ya kaishi daukana aikin ma tun farko oho." Barin falon tayi zuwa kicin inda tayi zamanta a can taci abincinta. Bata sake bi ta kan falon ba bare ta san lokacin tafiyarsa. Tana kwance kan gado sai aikin sake-sake takeyi abu daya ke yawo a kwakwalwarta, kuma hanya dayace da zata bi don magance wannan damuwar- itace ta bar aiki a AZ IT consultants. A karo na uku! Ko su kadai suke daukan ma'aikatan da suka karanta fagenta ta yafe wannan aikin da irin ukubar da take shiga kullum wayewar gari, "To ma wai aikin dole ne?" Ummu Adiyya ta tambayi kanta, ba tare da sanin dalili ba ta samu kanta tana tsiyayar hawaye. "Duk harda laifin Abba ma yaya za ayi bayan na fada masa komai kuma yace na ci gaba da aiki dasu?" ******