BANYI ZATO BA
Bayan gamayin dinner d'insu suka balle da hira, sosai suka tattauna da juna a inda Hakeem yayi ta bashi baki akan yazamo mai yarda da qaddara abisa laluran data sameshi. Yunus cike da annashuwa yayi ta godiya game da kulawansa akan laluranshi ganin yarda bai kyamace shi ba sam.