rabsyn's Reading List
4 dzieła
MAH~NOOR🌹 autorstwa AfricanQueen300
MAH~NOOR🌹
AfricanQueen300
  • Odsłon 93,895
  • Głosy 8,260
  • Części 43
Free book I grew up with this, I had best friends became enemies and then best friends again. I love it now, bc no one is perfect
MAIMAITA TARIHI (DANDANO) autorstwa ummyasmeen
MAIMAITA TARIHI (DANDANO)
ummyasmeen
  • Odsłon 130,010
  • Głosy 6,316
  • Części 14
***Wannan labarin somin tabi ne. Za a iya samun cikakken labarin akan manhajar Okada cikin watan Janairu, 2021. In sha Allah*** *** #1 aure 9th 01 2021 Tarihi yana kunshe da fuskoki da dama. Banda na wucewar abunda ya shude harda kasantuwar abunda ya shude a rayuwarmu ta yanzu. Sannan a duk lokacin da aka Maimaita tarihi, farashin yana karuwa ne fiye da kima. Hakan ne ya faru da Maryama-Siddiqa a lokacin da ta dauki alwashin bazata bari ta maimaita tarihi ba duk da kasancewa dukkan alamu sun nuna hakan ne yake shirin faruwa. Bayan zaman aure na tsawon shekaru ashirin tare da mijinta Sufyaan Barkindo Sajoh, sun gamu da kalubale wanda ya sa Sufyaan tono abunda ya dade da burnewa yayinda Siddiqah ta jajirce wurin neman 'yancinta daga rayuwar da ta samu kanta a ciki. Sai dai komai ya kwabe musu a lokacin da suka samu masu kalubalantar matakin da suka dauka. Siddiqa ta gamu da abokan hamayyar da suke neman rayuwarta wadanda bazasu tsaya ba har sai sun ga karshenta. Shin zata zakulo kanta daga wannan kangin, ta samu rayuwar da ta yi karfin halin mafarki wa kanta, ko kuwa za a maimaita tarihi ne? Shin wani bangare Sufyan zai zaba idan tura ta kai bango? ***
DUKKAN TSANANI  autorstwa Jeeddahtou
DUKKAN TSANANI
Jeeddahtou
  • Odsłon 118,101
  • Głosy 9,592
  • Części 71
Yunwa da ƙishirwar da suka addabe ni ne suka sanya ni kasa bacci ina yi ina farkawa sbd yunwa ta riga da tayi min illah, haka ma innata baccin kawai take yi amma na fahimci ita ma tana jin irin radadin da nake ji, don na lura sosai tunda ta kwanta take juyi. Agogon da ke manne a dakin mu na duba ƙarfe goma dai-dai na dare, har na share na hakura saboda na san matukar na fito diban abinci xan iya samun matsala da innah salamatu, har na hakura naji abin ba mai yiwuwa bane matuƙar muka wayi gari a haka zamu iya samun matsala. daurewa nayi na tashi na don samo mana abinda zamu kai bakin salati, ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar korar mu daga gidan gaba daya. A hankali na lallabo na fito daga dakin innata saboda bana so ita kanta tasan zan fita, indai ta sani sai ta dakatar da ni saboda bata son abinda zai bata mata rai. Kasancewar innata mace ce mai saukin kai bata fiye son abinda zai kawo tashin hankali ba, wannan dalilin ya sanya aka mayar da ita bora saboda hakuri da kawar da kai irin nata. Inna salamatu da yayanta su suke juya gidan duk a abinda suke so shi ake yi. Bakin murhu na nufa a hankali na bude tukunya, tuwo miyar kuka na gani, ba karamin dad'i naji ba saboda rabon da na sanya wani abu a bakina tun abincin safe. tsugunnawa nayi tare da yin bismillah na fara cin tuwon, kafin kace me tuni naci rabinsa, daga nesa na hango ana haskani da fitila a raxane na mike tare da boye hannuna a bayana, sai da ta karaso daf da ni sannan na ga ashe innah salamatu ce, wani kallo ta sakar min wanda ya sanya jikina rawar ɗari, kafin tace min wani abu tuni hawaye sun cika idona, don na san na taro kwai tara tsinana, na janyo wa kaina da innata masifar da Allah ne ya san ƙarshen ta, tsungunawa nayi tare da rokonta ta yafe min
ZATO...!  autorstwa pinkylady222
ZATO...!
pinkylady222
  • Odsłon 24,682
  • Głosy 3,705
  • Części 48
Acikin talatainin daren bakajin motsin komai sai kukan k'wari akai akai.Takowa take ahankali, sai dai duk sa'ilin data dauke kafarta tanajin kamar akwai mai maye gurbin sawun nata Danashi takon, k'okarin kauda tunanin hakan tadingayi sakamakon fitsarin da takejin inta k'ara cikakken minti d'aya batayishi ba zai xubone da kanshi......