KhadeejahRabiu's Reading List
3 stories
SOORAJ !!! (completed) by fatymasardauna
fatymasardauna
  • WpView
    Reads 909,283
  • WpVote
    Votes 71,730
  • WpPart
    Parts 59
Zanen ƙaddaransa yana cikin zuciyarta, kamar yanda zanen nata ƙaddan ke cikin tasa zuciyar. Idan zuciyoyi suka haɗe waje guda akan samu wata irin zazzafan ƙauna. Ako da yaushe jinsa yake kamar wani baƙon halitta, RAUNI DAMUWA sune abun da sukayi tasiri wajen cika rayuwarsa, yasani kowani bawa da irin tasa ƙaddaran Amma shitasa Ƙaddaran takasance me girma ne agareshi.... *** hearttouching and destiny!!!
RAYUWAR BADIYYA ✅  by Aishatuh_M
Aishatuh_M
  • WpView
    Reads 278,041
  • WpVote
    Votes 21,591
  • WpPart
    Parts 61
"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanji dadin rayuwata, babu yadda na iya haka na biyoki inda kika doro mani karan tsana, kullum sai kin zage kin dukeni, sunan mahaifiyata kuwa ya zama abun zagi a gareki a koda yaushe, kin hanani abinci, kin sakani wanka da ruwan sanyi lokacinda ake matukar sanyi, kin cuceni iya cutuwa, a haka Allah ya rayani. Sai ke yau dan rana daya kince zakici uwata nace nima zanci taki shine zakiyi kukan munafurci? Ni kin taba laakari da irin kukan danake cikin dare kullun? Dukda mahaifiyata ta rasu hakan bai hanaki zaginta ba. To na fada da babbar murya, wallahi duk kika kara cewa zakici uwata to sai naci taki uwar nima, and that's final!" Zuwa yanzu duk bakin cikin dake zuciyar Badiyya saida ya fito, kuka take kamar ranta zai fita, mahaifiyarta kawai takeda bukata, bakin ciki ya mata yawa, batada wanda zai saka ranta yayi sanyi bayan Momynta, amma tayi mata nisan da yakeda wuyar isa. Ta buda baki zatayi magana kenan Ahmad ya wanke ta da marika kyawawa guda biyu, ta dama da haggu, rike wajen tayi tana kallonshi. Magana ya fara cikin tsananin bacin rai, "Yanzu Badiyya a gabana kike cewa zakici uwarta? Uwata kenan fa Badiyya! To ko Yaya kika zaga bazan kyaleki ba balle wadda ban taba gani ba, dan haka wallahi zakiyi mugun dana sani," ya fada cikeda tsananin fushi, yana kara kai mata mazga saman kai. Kukane ya kara kwace mata "Kai kenan da baka taba ganin taka ba, nifa? Nifa Dady?! Na taba ganinta, nasanta, nasan dadin uwa, amma haka wani azzalumin ya raba ni da ita, sannan kai da nake tunanin zaka share min hawaye kaine kake kara sakani kuka, me na maka? Me Momyna ta maka?" Ta tambaya tana kureshi da idanu. _______ Me zai faru a rayuwar yarinya yar shekara goma data rasa mahaifiyarta? Wace irin rayuwa zatayi a gidan yayar mahaifinta?
MURADIN ZUCIYA by UmmAsghar
UmmAsghar
  • WpView
    Reads 39,824
  • WpVote
    Votes 2,597
  • WpPart
    Parts 20
'yan biyu ne masu tsananin kama ďaya masu mabambanta halaye. Maryam ta kasance miskila marar ďaukar raini, yayinda Mariya ta kasance mai son mutane da saurin sabo, tana da saurin fushi amma kuma tana da saurin sauka. Imran yaya ne a wurin Maryam da Mariya haka nan kuma daďaďďan saurayi a wurin Maryam wanda suka yiwa juna alkawarin aure. Me zai faru idan Maryam ta gano shakikiyar 'yaruwar da bata da kamarta a faďin duniyarta ta faďa tsundum a cikin son Imran. Zata hakura ta sadaukar mata da soyayyarta ne ko kuwa zata jajirce wajen ganin cewa bata rasa abin kaunarta ba. Ku biyoni cikin labarin sarkakkiyar soyayyar dake tsakanin Imran, Maryam da kuma Mariya.