Saayi13's Reading List
2 stories
ƘWAI cikin ƘAYA!! by BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    Reads 1,502,664
  • WpVote
    Votes 121,602
  • WpPart
    Parts 106
Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wasu a cikin matsalolin zuminci, gidajen aurenmu, Tsaro, rikita-rikita, harma da ruguntsumi. Kai lamarinfa ba'a cewa komai, mai karatune kawai zai banbance tsakanin aya da tsakkuwar zancena bayan mun tsunduma cikin labarin tsundum
KUƊIN ZOBE by Autan-Eloquence
Autan-Eloquence
  • WpView
    Reads 529
  • WpVote
    Votes 50
  • WpPart
    Parts 4
Tarin Ƴan Jaridu ne ke gewaye da Ƴan Sandan da suke a tsaitsaye a bakin katafaren gate na Luxury Hotel ɗin da ke birnin Maiduguri, gaba ɗaya Ƴan Jaridun sun gama hargitsa ilahirin wajen da hayaniyar su ta watsa labaran ji-da-gani kai-tsaye a ƙafafan yaɗa labarai. Daga cikin harabar Hotel ɗin kuwa, Sufeta Hassan ne da Sajen Gambo tare da wasu ma'aikatan Asibiti ke tsaye a jikin motar ɗaukan marasa lafiya ta General Hospital Maiduguri. A gaban su kuma gawarwaki ne guda Uku jere a ƙasa lulluɓe da fararen ƙyallaye, wanda tuni jinin da ke ɓul-ɓula daga jikin gawarwakin ya gama sauya musu launi daga asalin kalar su ta farare.