Abdurahim98's Reading List
5 stories
ZAMAN 'YA'YANA by AishaAbuTurab
AishaAbuTurab
  • WpView
    Reads 854
  • WpVote
    Votes 67
  • WpPart
    Parts 3
wannan littafin yana magana akan zaman aure wanda mata suke cikin kunci mai yawa...Matan da suka zauna a cikin hantara,zagi da wulakanci a karkashin mazajen su..
WANI GIDA...! by jeeedorhh
jeeedorhh
  • WpView
    Reads 130,411
  • WpVote
    Votes 12,237
  • WpPart
    Parts 31
Tana shiga cikin dakin, taji an janyo hannunta anyi gefe da ita. Cikin tsananin tsoro da bugun zuciya ta daga baki zata saki ihu, taji an sanya hannu an rufe mata baki, a lokaci guda kuma aka juyata tana kallon wanda yayi mata wannan aika-aika. Ta saki wani numfashi da bata san lokacin data rike shi ba, ta jefa mishi harara cikin wasa. Duk da cewa manyan fararen idanunta babu abinda suke fitarwa sai tsananin kauna mai tsafta. Ya kasheta da murmushin nan nashi da har kullum yake kashe mata jiki, ya kanne mata idanu, "Hello, love!". * Wai bahaushe yace 'hali zanen dutse!', 'mai hali baya canza halinsa!'. Bahijjatu tayi tunanin wadannan duk fada ce kawai, sai da ta kwashe watanni shida bata cikin gidansu ta koma, ta ga babu abinda ya canza zani daga tsarin rayuwar gidan. Wata irin rayuwa ce ake yi a cikin gidansu mai matukar daure kai. Rayuwar da babu girmama na gaba, babu bautar Allah, babu kuma tsoron Allah a cikinta. Bata san cewa rayuwarta na shirin yin juyi wanda bata taba zata ko tsammani a wannan dawowar ba. Ku biyo matashiya Bahijjatu domin jin ta yadda zata karbi wannan canji da yazo mata babu zato balle tsammani, ba kuma tare da ta shirya ba. Wannan littafi kyauta ne, wanda zai dinga zo muku a duk lokacin da damar yin typing ta samu... :)
MEKE FARUWA by AyshaIsah
AyshaIsah
  • WpView
    Reads 90,004
  • WpVote
    Votes 3,695
  • WpPart
    Parts 30
Labarin wata budurwa ne wacce aure yayi mata wahala. Amira kenan 'yar kimanin shekara 24 da hud'u, tayi samari fiye da biyar amma dukkan su sai magana tayi nisa kwatsam sai a nime su a rasa. Amira na da kishir uwa wacce sam basu shi da ita. Ko meke faruwa dake sanadin rabuwan ta da masoya ta? Ku biyo ni don jin inda labarin zata kaya.
👑MUTUNCIN'KI YAN'CINKI👑 by fareedathusainmsheli
fareedathusainmsheli
  • WpView
    Reads 504
  • WpVote
    Votes 24
  • WpPart
    Parts 8
📚📚📚📚📚📚📚📚 📚📚📚📚📚📚📚 📚📚📚📚📚📚 📚📚📚📚📚 📚📚📚📚 📚📚📚 📚📚 📚Mutuncinki yancinki,labari ne yazo da sabon salo ta hanyar fadakar da iyaye mata akan illar shaye-shaye hade da nunar ma iyaye mata illar kwadayi da kuma abinda yake haifarwa. , Fadakarwa,ilmantarwa,wa'azantarwsuna daga cikin abinda zai nusar da Yayan mu su gane shifa mutunci madara ne matukar ya zube baya kwasuwa duka ayayin da baka zuba mutuncinka ba kuwa zai kasance maka yanci a rayuwar ka.
KASHE FITILA by BatulMamman17
BatulMamman17
  • WpView
    Reads 250,838
  • WpVote
    Votes 18,431
  • WpPart
    Parts 53
Iyaye musamman mata sukan sadaukar da dukkan farincikinsu domin kyautata rayuwar 'ya'yansu. Haka ce ta faru ga Maamu har zuwa lokacin da Allah Ya azurta mata tilon danta Awaisu. A daidai lokacin da take tunanin kyautatawa wadanda suka wahalta musu a baya sai Gimbiya matar dan nata ta murda kambun da ko iyayenta basu santa dashi ba.... Ga uwa, ga da sannan ga suruka.