Halimaanche's Reading List
9 stories
BUDURWAR MIJINA by Sadnaf
Sadnaf
  • WpView
    Reads 13,688
  • WpVote
    Votes 473
  • WpPart
    Parts 11
love betrayal a short story of lady that struggle with a side chick
DIREBAN GIDANMU COMPLETE✅ by SaNaz_deeyah
SaNaz_deeyah
  • WpView
    Reads 13,409
  • WpVote
    Votes 526
  • WpPart
    Parts 43
Labarin wata yarinya data bijirewa iyayenta saboda direban gidansu. Labari ne da yake nuna illar taurin kai da kuma bijirewa umarnin iyaye.
SIRRIN MU by nimcyluv
nimcyluv
  • WpView
    Reads 11,779
  • WpVote
    Votes 286
  • WpPart
    Parts 12
_Duniya makaranta a lokacin da wasu suke shiganta a lokacin ne wasu ke barinta,wasu na zuwa Duniya wasu kuma na barin Duniya, Rayuwa kamar shafin littafi ce,baka sanin abinda yake bangwan baya dole saika buɗe shafin gaba,muna zuwa Duniya ne ba tare da sanin abinda ke cikinta ba,wasu na zuwa a makance, wasu a kurmance,wasu kuma babu ido,kunan jin magana,uwa uba wasu basa zuwa da ƙafar takawa_ _Nakasa bata taɓa zama kasawa,haka kuma ƙaddarar data mai dashi nakashasshen zata iya sauya, kullum cikin zullumi yake, shin tayaya ne rayuwa zata kasance masa? tayaya yana nakashasshen zai iya mulkan dubban jama'a? Cikin ana tsangwamarsa bare ace ya zama shugaba,yaya jama'ar gari zasu ɗauke sa?tayaya zai gabatar da mulkin bayan Allah ya taushe ta hanyarsa rasa wani ɓangare na jikinsa?_ _Zuciya nada abubuwan ban mamaki,abinda kake so ita bashi take so ba,kullum yana ganin abin kamar mafarki amma yadda abin ke zamar masa a gaske shike masa mamaki,me zaiyi wanda zai samu farin ciki?me zaifi wanda zuciyarsa zata daina kewa ta daina ƙunci,duhun dake cikinta haske ya mamaye shi, FARAUTA shine abinda zuciyarsa ta yanke masa,abin mamaki shine tayaya nakashasshe zai iya zama mafarauci? Tayaya farauta zata masa maganin damuwarsa?.._ '''SHIN ZAI IYA KO A'A? YANA CIN RIBA A FARAUTAR KO A'A? KUNA TUNANIN WATA RANA NAKASAR SA ZATA IYA ZAMA RIBA GARESA?
DUKKAN TSANANI  by Jeeddahtou
Jeeddahtou
  • WpView
    Reads 120,920
  • WpVote
    Votes 9,598
  • WpPart
    Parts 71
Yunwa da ƙishirwar da suka addabe ni ne suka sanya ni kasa bacci ina yi ina farkawa sbd yunwa ta riga da tayi min illah, haka ma innata baccin kawai take yi amma na fahimci ita ma tana jin irin radadin da nake ji, don na lura sosai tunda ta kwanta take juyi. Agogon da ke manne a dakin mu na duba ƙarfe goma dai-dai na dare, har na share na hakura saboda na san matukar na fito diban abinci xan iya samun matsala da innah salamatu, har na hakura naji abin ba mai yiwuwa bane matuƙar muka wayi gari a haka zamu iya samun matsala. daurewa nayi na tashi na don samo mana abinda zamu kai bakin salati, ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar korar mu daga gidan gaba daya. A hankali na lallabo na fito daga dakin innata saboda bana so ita kanta tasan zan fita, indai ta sani sai ta dakatar da ni saboda bata son abinda zai bata mata rai. Kasancewar innata mace ce mai saukin kai bata fiye son abinda zai kawo tashin hankali ba, wannan dalilin ya sanya aka mayar da ita bora saboda hakuri da kawar da kai irin nata. Inna salamatu da yayanta su suke juya gidan duk a abinda suke so shi ake yi. Bakin murhu na nufa a hankali na bude tukunya, tuwo miyar kuka na gani, ba karamin dad'i naji ba saboda rabon da na sanya wani abu a bakina tun abincin safe. tsugunnawa nayi tare da yin bismillah na fara cin tuwon, kafin kace me tuni naci rabinsa, daga nesa na hango ana haskani da fitila a raxane na mike tare da boye hannuna a bayana, sai da ta karaso daf da ni sannan na ga ashe innah salamatu ce, wani kallo ta sakar min wanda ya sanya jikina rawar ɗari, kafin tace min wani abu tuni hawaye sun cika idona, don na san na taro kwai tara tsinana, na janyo wa kaina da innata masifar da Allah ne ya san ƙarshen ta, tsungunawa nayi tare da rokonta ta yafe min
WACECE NI??? Part 2 by cutyfantasia
cutyfantasia
  • WpView
    Reads 5,734
  • WpVote
    Votes 461
  • WpPart
    Parts 34
Wacece ni labari ne akan matashiyar da ta taso cikin wata irin rayuwa mai ďaure kai da jan hankali. Ba abun mamaki bane idan kishiyar mahaifiyar mutum ta tsane shi amma mahaifiyar kanta ta nunawa ďanta tsantsar tsana da tsangwama da kyara abun ban mamakin gaske ne! Ko wani dalili yana sa uwa ta tsani ýarta? Wanne dalili ne wannan da zai iya juya matsananciyar soyayyar da uwa ta ke yi wa ýarta ta koma kiyayya zalla? Ita kuma ýar wacce irin rayuwa zata yi? Wanne irin kalubale zata fuskanta? Wanne irin hali zata shiga kuma ya za'ai ta warware wannan kullin? Wa zai bata amsar wannan tambayar mai nauyi? Shin yaya aka dauki matsalar fyade a kasar Hausa? Wanne irin hukunci ake yankewa wanda yayi da wanda akai wa? Ya rayuwar macen da wannan kaddarar ta faruwa da ita take kasancewa kuma wanne irin trauma take shiga? Wanne irin effect abun yake haifarwa a gare ta mentally and physically? Wacce hanyar ya kamata abi domin a warwaware wannan matsala mai cin tuwo a kwarya?
KASHE FITILA by BatulMamman17
BatulMamman17
  • WpView
    Reads 249,491
  • WpVote
    Votes 18,429
  • WpPart
    Parts 53
Iyaye musamman mata sukan sadaukar da dukkan farincikinsu domin kyautata rayuwar 'ya'yansu. Haka ce ta faru ga Maamu har zuwa lokacin da Allah Ya azurta mata tilon danta Awaisu. A daidai lokacin da take tunanin kyautatawa wadanda suka wahalta musu a baya sai Gimbiya matar dan nata ta murda kambun da ko iyayenta basu santa dashi ba.... Ga uwa, ga da sannan ga suruka.
🌺KuSKuReN 🥀BaYa🌺 by HafsatMohdArabi
HafsatMohdArabi
  • WpView
    Reads 10,581
  • WpVote
    Votes 338
  • WpPart
    Parts 13
Zara-zaran yatsun hannunta wanda suke sanye da zobina masu matukar kyan gaske da d'aukar hankali ,idona ya soma hangowa sanadiyyar motsa hannun da take tana juya stearing tana ɗan kad'asu lokaci-lokaci saboda wak'ar dake tashi a cikin Motar, tare da fitar sautin siriryar muryarta me dadin saurara. 'I don't care who you are, where you from what you did as long as you love me'. sautin dake tashi kenan a cikin motar na Back Street Boys wanda take marming kamar ita tayi shi. yayinda a hankali take motsa lips dinta kamar batason motsasu, gefe guda kuma zuciyarta ke bugawa da matsanancin karfi gaske wanda ta rasa dalili faruwar haka tun safe ta tsinci kanta cikin tsanani faduwar gaba ..
KUSKUREN BAYA by hauesh
hauesh
  • WpView
    Reads 21,259
  • WpVote
    Votes 702
  • WpPart
    Parts 22
Zara-zaran yatsun hannunta wanda suke sanye da zobina masu matukar kyan gaske da d'aukar hankali ,idona ya soma hangowa sanadiyyar motsa hannun da take tana juya stearing tana ɗan kad'asu lokaci-lokaci saboda wak'ar dake tashi a cikin Motar, tare da fitar sautin siriryar muryarta me dadin saurara. 'I don't care who you are, where you from what you did as long as you love me'. sautin dake tashi kenan a cikin motar na Back Street Boys wanda take marming kamar ita tayi shi. yayinda a hankali take motsa lips dinta kamar batason motsasu, gefe guda kuma zuciyarta ke bugawa da matsanancin karfin gaske wanda ta rasa dalili faruwar haka tun safe ta tsinci kanta cikin tsanani faduwar gaba ..