Sojoji sun zame mana wannan babban jigo a rayuwa. Sune suke sadaukar da duk wani farincikinsu ciki kuwa harda iyali da jindadin rayuwa domin tsaron lafiyarmu....shin wace gudunmawa al'umma take bawa wadannan jarumai da iyalansu???
Bahaushen mutum yana da kyawawan dabi'u wadanda addinin Musulunci da al'adunmu su ka koyar damu. Sai dai zamani yazo da wani salo, mun wayi gari bamu da abin koyi da tinkaho sai AL'ADUN WASU. Shin hakan hanya ce mai bullewa???
ZAINABU ABU ta taso a babban gida cikin gata duk da maraicin mahaifiyarta da tayi tun tana yar qanqanuwa. Duk yadda ta so haka take yi a Al'amuran rayuwarta ba tare da shakka ko tsoron komai ba. Salmanu wanda ya zama zabin yayarta da yayanshi ya zama mijinta ba tare da ta amince da hakan ba.