Giwa2020's Reading List
4 stories
MURADIN ZUCIYA by UmmAsghar
UmmAsghar
  • WpView
    Reads 39,757
  • WpVote
    Votes 2,597
  • WpPart
    Parts 20
'yan biyu ne masu tsananin kama ďaya masu mabambanta halaye. Maryam ta kasance miskila marar ďaukar raini, yayinda Mariya ta kasance mai son mutane da saurin sabo, tana da saurin fushi amma kuma tana da saurin sauka. Imran yaya ne a wurin Maryam da Mariya haka nan kuma daďaďďan saurayi a wurin Maryam wanda suka yiwa juna alkawarin aure. Me zai faru idan Maryam ta gano shakikiyar 'yaruwar da bata da kamarta a faďin duniyarta ta faďa tsundum a cikin son Imran. Zata hakura ta sadaukar mata da soyayyarta ne ko kuwa zata jajirce wajen ganin cewa bata rasa abin kaunarta ba. Ku biyoni cikin labarin sarkakkiyar soyayyar dake tsakanin Imran, Maryam da kuma Mariya.
A JINI NA TAKE by Aishatuh_M
Aishatuh_M
  • WpView
    Reads 69,559
  • WpVote
    Votes 3,091
  • WpPart
    Parts 12
Labari ne daya kunshi masarautu biyu; Masarautar Katsina, wacce take cikin Nigeria da kuma Masarautar Damagaran, wacce take cikin Kasar Niger. Labarin yayi duba ne da rayuwar Yarima Bilal, wanda rashin magana da miskilanci ya kanja ya shiga tarun matsaloli, wanda hakan yake haifar mashi da auren Zeenah Kabir Muhammad. Diyar Bafade da kuma baiwa. Me zai faru a rayuwar auren da aka hada miskili da kuma masifaffiya? Wanda dama tun farkon haduwarsu da masifa aka fara har yakai ga ya kure hakurinta ta sharara mashi maruka biyu? Shin ko zasu samu zaman lafiya kuwa? Bilal wanda ya kasance zuciyarshi a kulle take tun bayan rasuwar mahaifiyarshi zai bude ma Zeenah ita? Ya rayuwa zata basu bayan Zeenah ta fada soyayyarshi sai kwatsam Juwairiyya ta kunno kai? Wane hali Bilal zai shiga a lokacin da Fulani ta bankado wani tsohon sirri dake tsakaninsu? Fulani fah? Wacce take uwar gida kuma mai kula da hidimomin Masarautar Katsina gaba daya? Zata rufe sirrin data gano tsakanin Zeenah da Bilal dan gujewa tarwatsewar farin cikinsu? Abu daya ne zai kai ga na biyu, wanda har Bilal zai tsinci kanshi an mashi shamaki da Masarautar Katsina, hakan zai dangantashi da Masarautar Damagaran! Ku biyo Yar Malumfashi domin jin yadda labarin zai kasance.
WATA FUSKA by 68Billygaladanchi
68Billygaladanchi
  • WpView
    Reads 206,465
  • WpVote
    Votes 17,323
  • WpPart
    Parts 50
Sosai take a tsorace, ganin komai take tamkar a mafarki ji takeyi tamkar ma ace bata rayuwa a doron qasar, se zare ido takeyi tana kallon qungurmin dajin datake ciki, gata a d'aure ba hanyar guduwa, tayi iya kacin qoqarin taga ta qwace kanta amma sam abun ya faskara ya kuma tunzura, tunaninta d'aya yanzu idan wani naman daji yazo ya cinyeta ya zatayi kokuma wani mugun aljani gashi ko dankwali babu a kanta, babban tashin hankalinta shine sallar dabatayi ba, tun shekaranjiya da aka gudo da ita rabon datae sallah!!!! zata iya d'aukar kowane hukunci amma banda na hanata sallah!!! yaya zatayi da tulin sallolin dake kanta? batada halin yin koda taimamane sabida a d'aure tamau take to meye mafita?!!!!!!!
TARAYYA by Mamuhgee
Mamuhgee
  • WpView
    Reads 703,698
  • WpVote
    Votes 58,739
  • WpPart
    Parts 49
Royalty versus love.