Nana_haleema
- Reads 12,629
- Votes 373
- Parts 27
Izza, mulki, ƙasaita sun tattara a gare ta ita kaɗai. ƴar sarki ce, jikar sarki ce, matar sarki ce. Bata ƙaunar talaka, bata son haɗa hanya da talauci. Burinta ɗaya tak ya rage a duniya; shi ne ɗanta ya zama sarki, ita kuma ta zama babar sarki kuma kakar sarki na gobe. Sai dai kash! ƴaƴan nata maza har guda uku, masu matuƙar kama da juna, sun kasance babu wanda yake da qualities ɗin riƙe ragamar al'umma. A Lokacin da burinta ke gab da cika kwatsam aka ti mata dirar mikiya, ƴar talakawa, baƙa, gurguwa, mai tallan abinci ta shigo rayuwar samarin ƴaƴan nata guda uku, gurgurwar da ta zama silar girgizar duniyarta da burinta, gurgurwar da ta haddasa mata raunin da bata da shi, gurguwar da ta zamar mata inuwar dodo, gurguwar da ta zama mata ƙadangaren bakin tulu. Shin me zai faru? Ta wacce hanya gurguwa zata kutso cikin rayuwar waɗannan jinin sarautar...? Waye zai zama sarki cikinsu ukun duk da kasnacewar su masu kama ɗaya? ina alwashin da ta ɗauka na ganin cewar sai taga bayan duk wanda ya nemi ya ruguza lissafinta?, ina alwashinta na cewar sai ta kassara rayuwar wanda ya kawo kutsen hana ɗanta zama sarkin gari....?