Abdul10k
Dukan kofar ake da karfin tsiya,yayin da kowannensu ke kokarin tokare kofar da karfin jikinsa, kowace bugawa tana ratsa jikinsu kamar tsawa, har sai da kura ta rika fadowa daga silin din dakin.
kafafunsu na karkarwa a kasa, Amma abin mamaki, duk da wannan yanayi na firgici da suke a ciki, ihu kawai suke yi na neman tsira babu daya daga cikinsu da ya tuna ya ambaci sunan Mahalicci.
Duhu ya mamaye dakin, sai kawai karan numfashinsu da sautin katakon kofar da ke shirin tsagewa,Ba zato ba tsammani sai aka daina dukan kofar.
Shuru ya gauraye dakin shurun da ya fi dukan kofar ban tsoro, Sun tsaya cak suna kallon kofar yayin da gumi ya jika sassan jikinsu,Can kuma sai suka ji wani nishi mai nauyi daga bayan kofar wanda yasa hanjin cikinsu kaɗawa.
Kwatsam! Sai suka jiyo wani irin kara kamar ana yakusan kofar da farce,Katakon kofar ya fara tsastsagewa tsamkar bulon da ruwa taiwa karanci, A daidai wannan lokacin ne wutar dakin ya fara daukewa yana dawowa (flickering), yana nuna musu inuwar wani katon abu da ke kokarin bankado kofar, tsoro da fargaba ne ya hana su ko da kalma daya ta ambaton Allah, sai ihu mara sauti da ke fita daga makogwaronsu.
Daidai lokacin da katakon kofar ya fara rarrabewa, sai daya daga cikinsu mai suna [Fahad] ya farga, Duk da karkarwar da jikinsa yake yi, haka ya nufi wasu kayan tsafi da ke jere a tsakiyar dakin, wanda yake kyautata zaton sune suka haddasa faruwan wannan abu, Ya kwashe su da kafa sannan ya kifar da wata kwarya a kasa mai dauke da bakin garin magani, sannan ya tattake kasusuwan dake wannan guri da kuma kyandir da aka shirya a gun.
Nan take, sai dukan kofar ya tsaya cak! Gurin yayi shiru mai ban tsoro,Wutar da take ta daukewa ta tsaya cif, ta haske dakin radau, Sun rage su kadai a dakin, kowannensu na kallon kofar da ta rabe, kirajinsu na sama da kasa. Duk da cewa hatsarin ya kau, amma kowannensu ya sani cewa shuru ya dawo ne kawai saboda an bata tsarin bakin Tsafin, amma abin da ke wajen har yanzu yana nan a kusa.