aminuaisha19's Reading List
3 stories
RAYUWAR BADIYYA ✅  by Aishatuh_M
Aishatuh_M
  • WpView
    Reads 277,894
  • WpVote
    Votes 21,590
  • WpPart
    Parts 61
"Tun ina yarinya kike zagin mahaifiyata, tun bansan menene maanar kalmomin wulakanci da muzgunawa ba nakejin kina fadarsu ga mahaifiyata, ina cikin wannan halin wani azzalumi yaje ya kashe min mahaifiya, a gaban idona kika hana a tafi dani inda zanji dadin rayuwata, babu yadda na iya haka na biyoki inda kika doro mani karan tsana, kullum sai kin zage kin dukeni, sunan mahaifiyata kuwa ya zama abun zagi a gareki a koda yaushe, kin hanani abinci, kin sakani wanka da ruwan sanyi lokacinda ake matukar sanyi, kin cuceni iya cutuwa, a haka Allah ya rayani. Sai ke yau dan rana daya kince zakici uwata nace nima zanci taki shine zakiyi kukan munafurci? Ni kin taba laakari da irin kukan danake cikin dare kullun? Dukda mahaifiyata ta rasu hakan bai hanaki zaginta ba. To na fada da babbar murya, wallahi duk kika kara cewa zakici uwata to sai naci taki uwar nima, and that's final!" Zuwa yanzu duk bakin cikin dake zuciyar Badiyya saida ya fito, kuka take kamar ranta zai fita, mahaifiyarta kawai takeda bukata, bakin ciki ya mata yawa, batada wanda zai saka ranta yayi sanyi bayan Momynta, amma tayi mata nisan da yakeda wuyar isa. Ta buda baki zatayi magana kenan Ahmad ya wanke ta da marika kyawawa guda biyu, ta dama da haggu, rike wajen tayi tana kallonshi. Magana ya fara cikin tsananin bacin rai, "Yanzu Badiyya a gabana kike cewa zakici uwarta? Uwata kenan fa Badiyya! To ko Yaya kika zaga bazan kyaleki ba balle wadda ban taba gani ba, dan haka wallahi zakiyi mugun dana sani," ya fada cikeda tsananin fushi, yana kara kai mata mazga saman kai. Kukane ya kara kwace mata "Kai kenan da baka taba ganin taka ba, nifa? Nifa Dady?! Na taba ganinta, nasanta, nasan dadin uwa, amma haka wani azzalumin ya raba ni da ita, sannan kai da nake tunanin zaka share min hawaye kaine kake kara sakani kuka, me na maka? Me Momyna ta maka?" Ta tambaya tana kureshi da idanu. _______ Me zai faru a rayuwar yarinya yar shekara goma data rasa mahaifiyarta? Wace irin rayuwa zatayi a gidan yayar mahaifinta?
TARKON AURE,,,!!! by jiddanberry
jiddanberry
  • WpView
    Reads 3,669
  • WpVote
    Votes 129
  • WpPart
    Parts 1
TARKON AURE...-1 Cikin sanda Jamila ta ke tafiya a soron gidan, rike da takalminta. Sannu a hankali kuma tana wuwwurga idanunta a zagayen gurin. Za ta shige kenan cikin gidan ba zato ba tsammani ta ji an riko mayafinta. Gabanta ya yi wani irin yankewa ya fadi. Ta kasa juyowa bare ta yi wani kwakkwaran motsi illa sauke numfashi da ta ke yi a jigace. Birkito da ita ya yi suka fuskanci juna sosai. "A tunaninki za ki iya yaudara ta Jamila? A tunaninki zan sha wahalar kaunarki a banza?" Ya girgiza kai, "Ba zan iya ba! Ba zan iya wasa da wannan damar ba, domin ni ma Dan Adam ne da yake da jini tare da tsoka. Ban da haka tanadin da muka jima muna yi wa yaranmu ba zai tashi a wofi ba!" Jamila ta kasa rike kukan da ya taho mata, duk da ba ta ba shi damar fitar da sauti sosai ba, amma tuni hawaye ya wanke kundukukin fuskarta. "Ka yafe min Jamilu, ka yafe min... Ka yi hakuri mu karbi wannan nannauyar kaddarar. Jamilu ya dinga irgiza kai har ta rufe baki, sannan ya ce, "Na ji... Na ji... Yanzu ya ki ke so a yi?" Ta yi shiru tana sunkuyar da kanta kasa. "Kina nufin na rabu da ke, na daina sonki? Na cire ki a matsayin da na ba ki na zamowa uwar 'ya'yana? Uhum Jamila kenan, kin san Allah daya kenan ko? To wallahi ba zan iya hakura da ke ba, don haka ya kamata ki sani idan ma kin manta ni Jamilu SadeeQ M ba irin wadannan ragwayen mazan nan ba ne da ake kwace soyayya a hannunsu ta ruwan sanyi ba". Ya juya ya koma cikin dakinsa, ya barta tana share hawaye. Ta jima a gurin, yana daga dakin yana jin sautin shesshekar kukanta, wani irin tausayinta yake ji har zuciyarsa, amma ba shi da yadda zai yi, dole ya zage damtse don mallakar makullin farin cikin rayuwarsa. Motsin da ta jiyo daga cikin gidan ya sa ta saurin shanye sautin kukan nata sannan ta fara kokarin saisaita nutsuwarta. "Ah Jamila? Ai gidanku zan je". Amina kanwar Jamilun ta fada bayan ta shigo soron ta ga Jamilar.
ZAN SOKA A HAKA by queenbk2020
queenbk2020
  • WpView
    Reads 451,460
  • WpVote
    Votes 25,161
  • WpPart
    Parts 95
#5 tausayi June 2020. #3 tausayi 20 June 2020. #1 munafurci #8 hausa novel. #2 tear drop june 2021.