omarzainabb's Reading List
48 stories
JINI YA TSAGA by Oum_Nass
Oum_Nass
  • WpView
    Reads 21,323
  • WpVote
    Votes 1,334
  • WpPart
    Parts 20
Ba son ko wano uba bane samun balagurbi acikin ahalinsa, sai dai sau da dama ALLAH kan jarrabi bayinsa ta hanyoyi da dama. Duk da kasancewarsa babban Malami agarin hakan bai hana ya samu ta waya wajan gaza daqusar da mutum ɗaya tilo acikin ahalin sa ba. "Tabbas HAFSA zakka ce, daban take acikin yara na. Ni kuma itace tawa JARRABAWAR." "DUK da ana cewa JINI YA TSAGA FATA TA CIZA, awanan karon haƙuri na ya gaza. Bazan iya zama da HAFSA ba! zuciya ta ba zata ci gaba da jurar muyagun habaicin ta ba!" "NA san zaman ku da HAFSA ba mai ɗorewa bane HALIMA! Bazaki juri zama da ita ba. Ni na HAIFI HAFSA aciki na, na fiki sanin dafi da mugunyar halayyar ta." sai kun shiga cikin labarin zakuga ruɗaɗɗan al'amarin da ke cikin sa, labari ne mai ban haushi da takaici. labarin rikitacciyar yarinya mai halayyar ban haushi.
BOROROJI....The Journey of Destiny!!! by Mai_Dambu
Mai_Dambu
  • WpView
    Reads 91,795
  • WpVote
    Votes 16,558
  • WpPart
    Parts 73
love and Destiny.... She never thought of falling in love with him, but he never fell in love with her. She never knew who you trusted would betray you until she sought true love ....
KALMA DAYA TAK by AyusherMuhd
AyusherMuhd
  • WpView
    Reads 152,384
  • WpVote
    Votes 24,196
  • WpPart
    Parts 67
A rayuwata ban taba neman abu nawa na karan kaina ba, duk abinda aka tsaramin shi nake bi, ko inaso ko banaso abinda suka shimfidamin shi nake bi. Haduwata dake yasa zuciyata ta fara canzawa inaji kamar samunki shine cikar buri na rayuwata..... Sai dai me? Kalma guda daya tak daya kamata ta fito daga bakina ta wargaza miki rayuwa, na jefaki cikin kuncin rayuwar da nake ciki........
ZAMAN YA'YA by Mmnmuhibbat
Mmnmuhibbat
  • WpView
    Reads 13,604
  • WpVote
    Votes 1,219
  • WpPart
    Parts 35
Labari ne akan illar da zama da miji mazinaci take haifarwa da illar da ake samu daga mijin da ke ciyar da iyalinsa da haramun wane irin zaman ya'ya ya kamata mace tayi wane ne bai kamata ba.Wane bakin ciki mata ke fuskanta akan zaman Ya'ya.Labari ne akan yadda Maza suke amfani da ya'ya wurin kuntata ma mace mutane suke amfani da kalmar zawarci suke kuntata ma mata yan'uwansu.Labarin Salma da sule maketacin namiji mai kwace kudin matarshi.Bala da balki da gaje masu munafukin miji mazinaci.Ma'u da Mudi Miji mai shaye shaye ga zama haramci.Sai baiwar Allah zainab wacce maraicin ta bai zama rauni gareta ba wurin kwatar kanta daga Miji mai cin amanar aure wato talle.
JALILAH by AyusherMuhd
AyusherMuhd
  • WpView
    Reads 1,175,017
  • WpVote
    Votes 103,711
  • WpPart
    Parts 84
A painful love story.......... Duk yanda taso bacci ya dauketa ta kasa, juyi kawai take akan yar katifarta, ina zata sa kanta? Ya zatai da rayuwarta? Ina zata sa kanta? Me ya cancanta tai? Me zata zaba tsakanin burin zuciyarta da lafiyar Mahaifiyarta? Wasu zafaffan hawayene suka zubo mata......... Ku biyoni dan jin rayuwar Jalila a tsakiyar so da ceton Mahaifiyarta,
K'WARK'WARAH....(ITAMA MATAR SARKI CE) by Mai_Dambu
Mai_Dambu
  • WpView
    Reads 302,908
  • WpVote
    Votes 50,735
  • WpPart
    Parts 113
A zanen da Alkalanin kaddarar su ya zana musu! Akwai Soyayya! Akwai Sadaukarwa! Dan haka zanen kaddarar su a hade take su Uku! Babu wanda ya isa tsallake na wani ba tare da ya faɗa na wani ba! Jaamal! Jannart! Sarah! Sun rayu akan abu daya! Kuma sun haɗakar soyayyan Abu daya! Domin farin cikin mutum daya domin samun farin cikin mutum daya! Dole sai an sadaukar da farin cikin mutum daya
RAYUWAR AURENA  by Preety-hammud
Preety-hammud
  • WpView
    Reads 125,814
  • WpVote
    Votes 5,280
  • WpPart
    Parts 63
Labari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,
KHADIJATUU by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 286,396
  • WpVote
    Votes 24,841
  • WpPart
    Parts 66
NOT EDITED ⚠️ Yayi kyau matuƙa, yadin ya fito da farinsa da kuma kyaun fuskarsa, Idan ka kalleshi, sai ka ganshi kamar mai cikakkiyar natsuwa da kwanciyar hankali, al-halin sune abubuwan da suka masa tawaye. A hankali ya sauke ajiyar zuciya yana lasa lip ɗinsa. Juyowa yayi yana wani taku da idan baka karance shi ba, zaka iya cewa na wulaƙanci ne da nuna isa, al-halin babu hakan a tare da shi ko kaɗan, ƙarasowa yayi gun da Khadijatu take kwance ya duƙo daidai ita, ya hura mata iska a fuska kamin ya kai hannu ya taɓa jikinta. Hannun yasa ya tallafota ta dawo saman cinyoyinsa, fuskarta na fuskantar tasa, ido ya sakar mata kamar yau ya fara ganinta, a hankali ya kai hannun ya shafa gefen fuskarta, tausayinta ne yake ƙara shiga zuciyarsa. Shi kansa yana ji a jikinsa akwai wani sirri dake tsakaninsa da haɗuwarsa da Khadijatu, sirrin da har yanzu bai san na minene ba, yana jin shi ɗin wani bangone a shafin rayuwarta, lallai idan har babu shi a ƙaddarar Khadijatu toh babu wanzuwar labarinsa a doron ƙasa, yana ji a jiki da kuma ruhinsa domin ita akayi shi, kamar yadda yake jin da a'ace ya rabu da ita tsakanin jiya zuwa yau da bai san yadda rayuwarsa zata kasance ba, bai san wane irin hali zai samu kansa ba, dan baya taɓa rasa natsuwarsa idan yana kusa da ita, idan tayi nisa dashi ji yake kamar ya rasa wani ɓangare na jikinsa. Ba sonta yake ba, dan baya tunanin zai iya buɗewa wata ƴa mace zuciyarsa, tun bayan abunda Malak tayi masa, sai dai kuma yana jin fiye da yadda yake ji idan yana tare da Malak, yana jinsa cikin wani yanayi wanda bai taɓa ji ba idan yana tare da Malak. ® 2018
Zanen Dutse Complete✓ by Aysha-Shafiee
Aysha-Shafiee
  • WpView
    Reads 185,107
  • WpVote
    Votes 25,414
  • WpPart
    Parts 35
#1 in Aure 19/09/2020 #1 in Sarauta 19/09/2020 #2 in Halal Romance 19/09/2020 Ta riga ta san duk wata tarin ma'ana ta k'addara, walau mai kyau ko akasinta. Kamar kowa abinda bata sani ba shine... Me cece tata k'addarar? Yaushe zata fuskance ta? A wane yanayi zata zo? Mai kyau? Ko akasin haka? Wad'annan tambayoyin suke yawo kullum cikin kanta, da su take kwana take tashi, cikin tsumayin lokacin da alk'alami ya bushe akansa. Don wata k'addarar tamkar ZANEN DUTSE ce... Babu wani abu da ya isa ya canja ta!
SAMU YAFI IYAWA by SURAYYAHMS
SURAYYAHMS
  • WpView
    Reads 216,307
  • WpVote
    Votes 13,058
  • WpPart
    Parts 20
Its all about Abusive marriages ,sex and loyalty.