toyima's Reading List
36 stories
DARE DUBU by PrincessAmrah
PrincessAmrah
  • WpView
    Reads 38,787
  • WpVote
    Votes 2,424
  • WpPart
    Parts 61
Kaddara! Mece ce ita? Yaya rayuwar yarinya mai karancin shekaru za ta kasance a lokacin da ta tsinci kanta cikin mummunar kaddara, irin kaddarar da ba ta da magani? Shin dukkanin mutane ne ke jingine mafarkai da burikansu, su sadaukar da duk wani farincikinsu domin aminnansu? Ba matsalarta ce kadai ta dauka matsala ba, har matsalar aminiyarta ta mayar da ita tata, yayin da ta ci alwashin daukar fansa , ta ajiye burinta a gefe. Ku shigo cikin labarin DARE DUBU, na muku alkawarin ba za ku yi nadamar bibiyarsa ba.
HAKKIN UWA by PrincessAmrah
PrincessAmrah
  • WpView
    Reads 5,142
  • WpVote
    Votes 294
  • WpPart
    Parts 13
Wannan labari ne mai tsananin ban tausayi da taba zuciya wanda kuma ya faru da gaske sai dai 'yan gyare-gyare wadanda ba za a rasa ba. Shin kun san girman hakki kuwa? Kun san girma da darajar da uwa take da shi? Kun san babbar tabewa ce ga mai murje darajar uwa? Kun san cewa hakkinta ba zai bar mutum ba? Ku biyo ni don ganin salon wannan labarin.
ZUCIYARMU 'DAYA✅ by Mamuhgee
Mamuhgee
  • WpView
    Reads 60,096
  • WpVote
    Votes 3,009
  • WpPart
    Parts 12
love and hatred
IDON NAIRA by Mamuhgee
Mamuhgee
  • WpView
    Reads 5,049
  • WpVote
    Votes 219
  • WpPart
    Parts 8
Life/sisters/fmly
ZAFIN KAI by Mamuhgee
Mamuhgee
  • WpView
    Reads 6,812
  • WpVote
    Votes 137
  • WpPart
    Parts 6
Zafin kai????
HAIHUWA DA HANJI  by Gureenjo6763
Gureenjo6763
  • WpView
    Reads 20,088
  • WpVote
    Votes 975
  • WpPart
    Parts 60
TIME... LOKACI. Lokaci kamar Unit ne da ke barin shaidar wanzuwar abu walau kyakyawa ko mummuna sai dai shin yaushe zai wuce? Ta yaya zai shuɗe? Me ya ke tafe da shi? Allah ne kaɗai masani.. Kaman yadda ƊIGON RUWA kan bushe cikin lokaci ƙanƙani haka na ɗauki jarrabawa ta da ke maƙale bisa zaren ƙaddarar rayuwata... Sai dai kash tawa ɗigon ruwan duk yadda zan fifitata ta gagara bushewa. Na zaɓi zama tamkar tuwon hatsi don juriya sai kuma ya kasance ba komai ne tuwon hatsin ka iya jura ba. Matsi, takura da tsananin rayuwa sun sa na yanke yin mai ɗungurungun wai haihuwa da hanji wurin ɗaukar raina da hannuna saboda ban ɗanɗani wani garɗi ko zaƙi na wannan duniya ba!
WANI GARI by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 14,121
  • WpVote
    Votes 605
  • WpPart
    Parts 16
A wani gari, da al'ummarsa basa hada jini da mutanen wajen garin, akwai wata yarinya da alkalamin kaddara yayi mata zane a garin da bata da kowa ciki kuwa har da masu jin yarenta! Garin da babu masu cin irin abincinta babu ma su kalar addininta balle kuma al'adar da ta ginu a kai! Ta fallasa wani sirri da aka dade da binnewa shekaru ashirin da bakwai a baya, ta yi nasarar sauya rayuwar Maleek. Hakika wani mafarkin baya nufin cikar burin mai shi, wani burin kuma yana tabbatuwa ne tun kamin zuwa mafarki. Ya Ameer zai ji idan ya farka daga dogon bachin da ya dauke shi mafarkin shekarun da babu wanzuwarsu a rayuwarsa ta baya da kuma wanda za ta zo a gaba? Mi ya haifar da gaba a tsakanin yan'uwa jini? Anya wuta da ruwa za su hadu? Find out in WANI GARI. Rikicin cikin gida. Labarin soyayyar da bata jin yare...
H U R I Y Y A by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 18,645
  • WpVote
    Votes 657
  • WpPart
    Parts 16
Wata rayuwa ce zan taɓa ta Hausawa, wani ɓangare na ƙabulan da yara suke fuskanta a gidan iyayensu, tun farko tashi har girma, wani abu ne da nake ta hangowa kuma na daɗe da ƙishin son rubutawa. ••• ••• H U R I Y Y A -Labari ne mai ban tausayi da taɓa zuciya. Story of the Year 2023... Be kind to every human being, because you don't know the whole story and matter what you are facing never give up. You don't know what the future holds...
Z A K I by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 42,821
  • WpVote
    Votes 2,612
  • WpPart
    Parts 15
Meet Ataa - a 16 years old muslim girl. Growing up wasn't easy for her, she's struggling to make her life comfortable for her mother and her little brother. Doctor Asim helps her, and secretly sold her mother's kidney to Mr billionaire wife. Mr billionaire Aliyu was arrogant, strong as an lion CEO of Sky Global Resources, he doesn't tolerate negligence or stupidity, when he roars no one will roar back.
BAKAR WASIKA by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 25,154
  • WpVote
    Votes 1,093
  • WpPart
    Parts 11
BAƘAR WASIƘA... Mai farin rubutu Ban ce tafiyar mai sauki ba ce. Ban muku alkawarin zallar soyayya ba. Ban ce babu farincikin ba. Kunci, bakinciki da damuwa, sune abubuwan da suka taru suka tare farincikin AMINATU, kalubalen rayuwa bayan wata rayuwar, tabbas akwai kuka akwai damuwa da bakinciki. Labarin Talba, Rafi'a, Laila, Madina, Ramlee, Faruk, Amal da kuma Aminatu. Labarin BAKAR WASIKA, labari ne da zai tabo wani bangare na rayuwar mace, kuma wani bangare na rayuwar al'ummarta da iyayenta... Ina fatar zaku karbe shi kamar sauran, duk na san ba lallai ne yai muku dadi ba domin ba soyayya ce zalla ba, kalubalen rayuwa ne da fadi tashin yar gudun hijira! A ina zata kwana? Wa zai bata masauki? Taya za a fahimce ta har a nade mata damuwarta? Wa zata kaiwa kukanta iyeyenta ko al'ummarta? Ta ina mafarkinta ke tabbatuwa? Ashe bayan wuya akwai wata wuyar, bayan dadi ma akwai wata wuyar, bayan wuya kuma akwai dadi. Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke? Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa? BAKAR WASIKA... JUANURY 2022