khadee50's Reading List
26 stories
BA UWATA BACE by meeshalurv
meeshalurv
  • WpView
    Reads 68,266
  • WpVote
    Votes 5,250
  • WpPart
    Parts 48
BA UWA TA BACE Zaune take gefe guda cikin gidan nasu, tana kallon abinda Yan gidan nasu sukeyi k'awar tace Hadiza zaune gaban mamar tasu tana mata lissafin kud'i da tasamu, daga daren jiya zuwa yau da safe. Mamar sai washe hak'ora take tana murna sannan tace "Ai na fad'a Miki idan Kika bi Alhaji Hamza kwanan gida sai ya Baki mamaki." Hadiza tace gashi kuwa ya bani mamaki mama domin tunda Nike arayuwata bantab'a kama irin kud'in Dana kama yau gugu na gugur naira har dubu hamsin mama tawani wutsilo daga kugerar da take Yar tsugunne, ta fad'o k'asa sannan ta d'aga Kai ta dubi Hadiza ko zafin fad'uwar bataji ba tace da gaske kike ko da Wasa Yar nan. Hadiza tace "wallahi mama kingansu ma" ta fito dasu ta nuna mata kud'in hannu na rawa mama ta k'arbesu ta tashi tana juyi da rawa agaban d'iyar Tata. Bilkisu ji tayi k'amar ta kurma ihu Dan bak'in ciki wannan wata irin uwa ce Allah ya Basu, wasu hawaye masu zafi ya zubo mata ganin yadda ita Tata rayuwar zata Kaya kenan ga wata uwar yunwa datakeji, Amma saboda tak'i bin abinda uwar Tata takeso ta hanata, gashi ita tashin hankalinta shine idan dare yayi wani irin tuggu zasu had'a mata Dan taji mamarta da yayanta na zancen, zuwan Alhaji kamilu zuwa gareta ko tanaso ko bataso yau sai ya kwana da ita, Anya kuwa wannan ita d'in uwa ce agaresu tana cikin wannan tunanin taji k'ara bud'e kyauren gidansu na langa langa daga Kan da zatayi Dan taga Mai shigowa sai taga k'awarta ce ta biyu zainab. Shigowa tayi cikin wata irin shiga domin kayan jikinta amatse suke sosai duka sun fitar da surar jikinta rabin breast d'inta duk awaje cikin takun yauk'i da yanga tashigo, tana yatsina ko sallama babu mamarta ta k'alla sannan tace "wallahi mama yau nagaji Dan wannan d'an iskan Alhajin bak'aramin sasuk'a ta yayi ba tun dare yake abu d'aya har safe gashi bak'arami ba ga abun tashi kamar tabarya, gaskiya ya cika d'an iska
DUKKAN TSANANI  by Jeeddahtou
Jeeddahtou
  • WpView
    Reads 121,061
  • WpVote
    Votes 9,598
  • WpPart
    Parts 71
Yunwa da ƙishirwar da suka addabe ni ne suka sanya ni kasa bacci ina yi ina farkawa sbd yunwa ta riga da tayi min illah, haka ma innata baccin kawai take yi amma na fahimci ita ma tana jin irin radadin da nake ji, don na lura sosai tunda ta kwanta take juyi. Agogon da ke manne a dakin mu na duba ƙarfe goma dai-dai na dare, har na share na hakura saboda na san matukar na fito diban abinci xan iya samun matsala da innah salamatu, har na hakura naji abin ba mai yiwuwa bane matuƙar muka wayi gari a haka zamu iya samun matsala. daurewa nayi na tashi na don samo mana abinda zamu kai bakin salati, ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar korar mu daga gidan gaba daya. A hankali na lallabo na fito daga dakin innata saboda bana so ita kanta tasan zan fita, indai ta sani sai ta dakatar da ni saboda bata son abinda zai bata mata rai. Kasancewar innata mace ce mai saukin kai bata fiye son abinda zai kawo tashin hankali ba, wannan dalilin ya sanya aka mayar da ita bora saboda hakuri da kawar da kai irin nata. Inna salamatu da yayanta su suke juya gidan duk a abinda suke so shi ake yi. Bakin murhu na nufa a hankali na bude tukunya, tuwo miyar kuka na gani, ba karamin dad'i naji ba saboda rabon da na sanya wani abu a bakina tun abincin safe. tsugunnawa nayi tare da yin bismillah na fara cin tuwon, kafin kace me tuni naci rabinsa, daga nesa na hango ana haskani da fitila a raxane na mike tare da boye hannuna a bayana, sai da ta karaso daf da ni sannan na ga ashe innah salamatu ce, wani kallo ta sakar min wanda ya sanya jikina rawar ɗari, kafin tace min wani abu tuni hawaye sun cika idona, don na san na taro kwai tara tsinana, na janyo wa kaina da innata masifar da Allah ne ya san ƙarshen ta, tsungunawa nayi tare da rokonta ta yafe min
UMARNIN SAURAYI by mnaige
mnaige
  • WpView
    Reads 187
  • WpVote
    Votes 1
  • WpPart
    Parts 10
labari ne wanda ya kunshi wata yarinya mai bin umarnin saurinta saɓanin na iyayen ta,abin dai sai wanda ya karanta.
WATA FUSKA by 68Billygaladanchi
68Billygaladanchi
  • WpView
    Reads 206,449
  • WpVote
    Votes 17,323
  • WpPart
    Parts 50
Sosai take a tsorace, ganin komai take tamkar a mafarki ji takeyi tamkar ma ace bata rayuwa a doron qasar, se zare ido takeyi tana kallon qungurmin dajin datake ciki, gata a d'aure ba hanyar guduwa, tayi iya kacin qoqarin taga ta qwace kanta amma sam abun ya faskara ya kuma tunzura, tunaninta d'aya yanzu idan wani naman daji yazo ya cinyeta ya zatayi kokuma wani mugun aljani gashi ko dankwali babu a kanta, babban tashin hankalinta shine sallar dabatayi ba, tun shekaranjiya da aka gudo da ita rabon datae sallah!!!! zata iya d'aukar kowane hukunci amma banda na hanata sallah!!! yaya zatayi da tulin sallolin dake kanta? batada halin yin koda taimamane sabida a d'aure tamau take to meye mafita?!!!!!!!
KATANGA by Rashuna
Rashuna
  • WpView
    Reads 917
  • WpVote
    Votes 21
  • WpPart
    Parts 4
Tabbas ta fishi gaskiya a ko ina, ya za'ai su dinga abubuwa irin na ma'aurata bayan ba auranta zai ba, shak'uwarsu k'ara k'arfi take ta na gudun da basu san bigiren da za ta ajiyesu ba, ya na jinta a can k'asan zuciyarsa, itace farin cikinsa itace rayuwarsa, ita ta fara gina Katangar farin cikin da ya dad'e da rusheta a babin rayuwarsa, bai tab'a nuna rauninsa ga kowa ba sai akanta, itace zai shiga jikinta ya yi kuka kuma ta rarrasheshi ta sanya masa nutsuwa a zuciyarsa, to ta yaya zaiyi sakacin da zai rasata gaba d'aya? Inama zai iya auranta da sai ya fi kowa farin ciki domin auranta shine burin zuciyarsa, ruhinsa da ma gangar jikinsa, amman hakan ba za ta tab'a samuwa ba bazai tab'a yafewa kansa ba idan har ya zamo silar mutuwarta, ya na hango tu'kuk'in bak'in cikin da zai d'and'ana na rashinta gaba d'aya Cikin Duniyarsa, abu d'ayane mafita a garesa dole ne ya nisanceta ya k'auracewa ganinta gaba d'aya amman kuma ta yaya hakan za ta kasance? Bai tab'a jin bakin cikin abinda yai masa Katanga da aure ba sai yau, ya na jin inama zai iya rushe wannan Katangar ta yadda zasu gino sabuwar Katangar rayuwar auransu amman hakan ba za ta yuyu ba, hakan ya na da nasaba da rasata gaba d'aya cikin duniyarsa, kuma ya rasa da wani yare zai fahimtar da ita hakan. Waye shi d'in wannan, kuma wace yake magana a kanta, kuma meye ya yi musu Katanga da auran da suke buk'ata? Samun wannan amsoshin sai kun ninkaya cikin wannan littafi akan 300 kacal. Rashuna Bebe'art ke muku fatan alkhairi.
NAGA TA KAINA by Sadnaf
Sadnaf
  • WpView
    Reads 96,510
  • WpVote
    Votes 7,863
  • WpPart
    Parts 64
A TRUE LIFE STORY A HRT TOUCHING STORY
ƘWAI cikin ƘAYA!! by BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    Reads 1,500,424
  • WpVote
    Votes 121,594
  • WpPart
    Parts 106
Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wasu a cikin matsalolin zuminci, gidajen aurenmu, Tsaro, rikita-rikita, harma da ruguntsumi. Kai lamarinfa ba'a cewa komai, mai karatune kawai zai banbance tsakanin aya da tsakkuwar zancena bayan mun tsunduma cikin labarin tsundum
WITHOUT MY DREAMS (HAUSA NOVEL)✔️ by mssmeemah
mssmeemah
  • WpView
    Reads 13,828
  • WpVote
    Votes 991
  • WpPart
    Parts 59
'Doki da zumud'in rayuwar da Muneera ke Jin labari yasa ta toshe kunnuwanta da duk wanda zai kawo mata shawarar da zata kushe za'binta, ta d'aukeshi rayuwarta ta bashi yarda da aminci, saidai shin a wurinsa haka take? shin dalilinsa na aurenta tsakani da Allah ne ko kuwa yabi sin zuciyarsa ne? ta wacce hanya muneera zatayi maganin matsalar da ta jefa kanta ciki bayan duk masu sonta da alkhairi ta yanke ala'ka dasu?
GOBE NA (My Future) by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 165,100
  • WpVote
    Votes 17,188
  • WpPart
    Parts 65
Babu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta kasance. Daga ni sai ire-irena mu ke iya labarta yadda mace ta ke ji idan aka keta haddin yarta ko kuma ita kanta! Ina ma ace yau haddina ni Halimatu aka keta ba na yata ba? GOBE NA... Zawarcin Halimatu... *** *** *** Babu wanda zuciyarsa ta raya masa sai matar nan, sosai ya maida hankali yana kallon gurin da take zaune tare da yaranta, the way ta take sharar hawaye ya kara karafafa zatonsa a kanta, labarin yarsa ya shigo ciki duk kuwa da bata fadi sunansa ba ko sunan yarsa sai dai ta fadi cewar mahaifin yar ya zargeta da kisan yarsa saboda kaddarar mutuwarta ya fada mata, kamar yadda kadarar gushewar hankalin abokin aikinta ya fada a kanta, an keta mata haddi an ketawa yarta, mijinta ya ci zarafinta, a kokarin kwatar hakkin yarta mijinta ya saketa, ga labarin samun aikin kamfanin da tai ya shigo ciki sai dai shi ma bata fadi sunan kamfanin ba..... Wani irin kallonta yake, har ya ji kamar gilashin dake idon sa ya tare ganinsa sai ta ya cireshi yana cigaba da kallonta, ita kuma ta soke kai kasa yana ta latsa waya tana sharar kwalla, wa akai wa fyade? Wacen karamar ko babbar? No wait mutunen da take bawa abincin a kusa da kamfaninsu abokin aikinta ne? Is that why take kokarin kula da shi? Waye mijin na ta? Waya ke bibiyarta? A lokaci daya ya jerowa kansa wadannan tambayoyin, da bashi da amsar su, and he can't take his eyes on her kamar his life defend on her.
MARAICIN 'YA MACE by _bambiee
_bambiee
  • WpView
    Reads 70,601
  • WpVote
    Votes 6,580
  • WpPart
    Parts 36
Labari ne na wata yarinya da ta taso cikin tsana tsangwama wajen iyayenta. Tun da ta taso ta fara fuskantar matsaloli daban daban wajen iyayenta Inda ta fara tunanin anya ta hada wata alaka dasu kuwa? Ta fitar da rai daga samun wata soyayya ta iyaye kwatsam Allah ya had'a ta da Wani saurayi inda ya zamo gatan ta ya mantar da ita wahalar da tasha a baya...