AKWAI ILLA
Tafe take tana sanye da riga da siket na atamfa, idanunta na rufuwa a hankali tana kokuwar bud'ewa. Layi take kamar wacce ta sha kayan maye, hannunta rik'e da cikinta tana yamutsa fuska. Kayan jikinta yayi bak'i, ya canja launi daga kalar kore zuwa wata kalar daban tsabar daud'a, farat d'aya in aka ce a k'idaya tsawon...