zaisal2's Reading List
3 stories
KOWA YA GA ZABUWA... by Gureenjo6763
Gureenjo6763
  • WpView
    Reads 47,661
  • WpVote
    Votes 2,044
  • WpPart
    Parts 47
Rayuwa wani abu ne da kan zo mana da kalubale iri iri, wani muna iya fin karfinshi da taimakon Allah wani ko sede mu zubawa sarautar Allah idanu zuwa sadda ze kawo mana karshen shi walau Mutuwa walau sakamako na farin ciki. HIDAYAT yarinya me ƙarancin shekaru marainiya gaba da baya, bata da kowa bata san kowa ba, ta taso cikin kangin rayuwar marikiya an aura mata mafi zaluncin miji cikin maza a rashin sani, wadda ya kasance ɗa ga marikiyarta Kaddarar ƴaƴa ta Haɗa ba tare da wannan azzalumin miji yayi maraba da su ba, ya rayuwa zata zame mata? Ta ina zata iya Kula da kanta da kuma yaranta? Cin su shan su, suruturarsu? Anya zata iya tsallake wannan jarabawar kuwa? Anya ba zata gaza a hanya ta fawallawa Allah lamuranta ta zubawa sarautar shi idanu ba? Shin da dangin miji zata ji ko da Shi karan kanshi mijin ko kuwa da baƙar rayuwa da take ciki? Shin zata iya tsira daga wannan taskar na Tsaka mai Wuya? Duk ku biyo ni cikin wannan littafi na KOWA YA GA ZABUWA... Na muku Alkawari ba Zaku taɓa yin nadama ba, Alqalamina a feke yake don Nishad'antar daku, fad'akantar daku da kuma ilmantar daku duk a cikin wannan littafi.. karku bari a baku labari.
TSANTSAR BUTULCI COMPLETE by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 23,384
  • WpVote
    Votes 1,734
  • WpPart
    Parts 47
Ko daga jin sunan littafin basai na baku labarin irin BUTULCIN da za'a tafka acikinsa ba, labari ne me tab'a zuciyar me karatu ya kunshi darasi acikinsa, Kuma izna ne ga azzaluman mutane, kubiyo zasu fahimci abinda nake nufi.
FURUCI NA NE by HauwaAUsmanjiddarh
HauwaAUsmanjiddarh
  • WpView
    Reads 55,135
  • WpVote
    Votes 3,770
  • WpPart
    Parts 37
"Baba meyasa kazama boka bokanci fa haramun ne kuma k'arya ne shirka ne Allah baya yafewa mushirki..... "ke Izza ki kiyayeni idan kika nemi d'agamin hankali abin bazai miki kyau ba dan ni zan iyayin komai akan cikar burina na kashe Faida ma balle ke zaki kawo min maganar banza yanzu kinga wani abin da ya Dan ganci bokan ci ne atare dani na dena aikin ki kad'ai zan cigaba dayi shima idan burin mu yacika kika auri daya daga ahalin gidan nan zan bari na tuba meye Allah baya yafewa nide nasan zai yafemin". shiru tayi can ta nisa tace'' to shikenan Baba ance idan zaka sha giya shata dubu ni megaba dayan nake so Nasuru din". dariya yayi yace"shegiya Naira ba babba ba yaro ni kai na naso haka naso ace Nasara kika mallaka amma sam taurari sun nuna ba al'kairi taurarin ku basu hadu ba ba aure a tsakanin ku da Nasara shine na hakura amma ina lefin Aiban ko Agrif din'." tace'' amma Baba nafison Agrif din dan shine akusa da Nasara kaga yafi sauran sanin sirrin komai na dukiyar ". murmushi yayi yace"yanda kike so haka za ayi wa gareni inba keba".