nimcyluv
"Laa! Baka da lafiya ga hantarka nan naga ya zama ƙarama" ya dube ta da mamaki. Cikin sauri ta ce. "Ai ni mayya ce, ga taliyar da ka ci nan ma bata narke ba, Babata sai data ci mutane 85 a ƙauyenmu"
Da wani irin yanayi yake kallon ta, da wannan blue ƙwayar idanun tasa mai tasiri. "Ina jin kamar na kame kurwarka ko yaya na suɗa, daga gani za ka yi maiko" ta sake hanzarin faɗin hakan.
Shirun nan me kashe mutane ya sake yi mata. Caraf ta ce "Amma ban taɓa cin ko rai guda ba, ina shan wahala idan abin ya motsa mini"
"To kar ki ci"
Ta ji kasalalliyar muryarsa a kunnenta a karo na farko. "To ya zan yi"
"Ki kama ni, ki kama kurwata" ya bata amsa. "Ba zan iya cinye ka ba, ai kyakkywa ne kai"
A hankali ya ce "Daman ba za ki iya cin nawa ba, ki rage zafi zan sadaukar da lafiyata a wajanki muddin ba za ki maita ba" ta ja idanunta ta lumshe ta sake buɗewa jinin jikinsa ne yake ta gudana yana tsinkar mata da kwaɗayinta.
"Ya sunanka?"
"Mara tabbas"
Ta ce "shine sunan?"
Ya jinjina mata kai.
Miƙewa ta yi tsaye ta zubawa kurwarsa idanu cikin sa'a ta kame ta damƙe a hannunta nan take kan shi ya sara zazzaɓi ya rufe shi.
TAƁA KA LASHE
HIYAAM
zai fara 1 ga watan June.
08164069385