rukaiyamu's Reading List
170 stories
INDO SARƘA COMPLETE by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 79,058
  • WpVote
    Votes 5,550
  • WpPart
    Parts 57
Cikin dare lokacin ƙafa duk ta ɗauke banda kukan tsuntsaye ba abunda yake tashi, alokacin ta farka daga bacci kayan wajen Goggo tasa ta ɗauko zumbulelen farin hijabin tasa, kwandon kayan kwalliyarta da shafe sati bata buɗeshi ba, ta buɗe ta ɗauko hoda ta zazzaga ta shafe fuskarta, hannu da ƙafafuwa Ludayin miyar Baba Huwaila da tun rana ta ɓoyeshi ta ɗauka ta sa a hijabi, ƴar fitilarta ta ɗauka ta fito daga ɗaki saɗaf-saɗaf ta je wajen bakin ƙofa ahankali ta zare sakata ta fice, kamar Aljana ita kaɗai ce a waje haka ta samu ta ƙarasa bayan katangar gidan Mai Gari ( _Dake gida huɗu ne tsakanin gidana Baba Huwaila da na Mai Gari_) ta kamata ta ɗane ta dirga. A hankali ta ɗaga labulen ɗakin Mai Gari ta shiga ta same shi a kwance baccinsa yake hankali kwance, toshe bakinta tayi tana dariya ƙasa-ƙasa musamman da ta tuna irin muguntar da zata yiwa Mai Gari, sai da tayi ta gama ta koma saitin kan Mai Gari ta zaro ludayin miyar ta dai-dai ci kan sa ta bashi ƙwaaal, azabure Mai Gari ya tashi yana susar gurin baya yaja ganin mutum tsaye cikin fararen kaya. Indo canja murya tayi shigen ta Goggo sannan ta fara magana, " Ni ce Goggo Kakar Indo Sarƙa nazo tafiya kai cen makwancina tunda cin Amana zakayi " Mai Gari cikinsa ne ya juya baiyi aune ba sai ji yayi ɗumi na bin wandonsa, Indo na ganin Fitsari na bin ƙafar Mai Gari ta gimtse Dariyarta ta kuma cewa.....🥱
FATU A BIRNI (Complete) by suwaibamuhammad36
suwaibamuhammad36
  • WpView
    Reads 74,641
  • WpVote
    Votes 2,361
  • WpPart
    Parts 18
"I promise you Mami, zan nemo miki ƴar'uwarki a duk inda take a faɗin ƙasar nan. SULTAN promises you that." Sultan ya shiga ya fita, har ya aikata abunda ba'a tsammani domin ya cika wannan alƙawari da ya ɗaukawar mahaifiyarshi, aka yi dace ya gano inda take. Wani abun takaici shine a maimakon ya samu ƴar'uwar Maminshi kamar yanda ya ci buri, sai ya haɗu da ƴarta kwalli ɗaya tak da ta haifa a duniya ta bari cikin ƙauyanci da kuma rashin wayewa. Baƙin cikinshi bai tsaya a nan ba, domin dattijon da yake riƙe da ita a take ya aura masa yarinyar ba tare da ya iya kaucewa wannan mummunan ƙaddaran ba. Ya tafi ya barta ba tare da ya sake waiwayarta ba, ya kuma tafi da wani kaso na zuciyarta ba tare da ya sani ba. Fatu (Fatima) ta ji haushi, sannan tana cikin baƙin cikin tafiyar da mijinta yayi ya barta. Tun tana tsumayinshi tana fatan ya dawo ya ɗauketa, har zuciyarta ta daskare da tsantsar tsanarshi na wofintar da ita da yayi, da kuma banzatar da igiyar aurensa dake kanta. Tayi alƙawarin ɗaukan fansa, ta kuma yi alƙawarin raba tsakaninsu ko da duniya zasu taru su hanata. Sai ta nemo shi a duk inda yake. Ta shiga cikin Birni nemansa, a nan kuma ƙaddara ya gifta tsakaninsu suka haɗu a lokaci da kuma yanayin da basu yi tsammani ba. Shi kuma ganin kyakkyawar baƙuwar fuska mai ɗauke da kamala, ya sashi faɗawa cikin sonta dumu-dumu ba tare da ya shiryawa hakan ba, kuma ba tare da ya gane cewa Matarsa ce ta Sunnah ba, Halal ɗinsa. Me zai faru idan Fatu ta haɗu da mutumin da ta ƙullata tsawon shekaru a yayin da shi kuma yake jinta a zuciyarsa tamkar ruhinsa? Me kuma zai faru Idan wasu sirrikan suka bayyana a lokacin da ba'a shirya musu ba? Fatu mace ce ɗaya mai hali mabanbanta; Fatu- Matar Sultan. Fatima- Budurwar Sultan.
MAMANA CE  by HauwauSalisu
HauwauSalisu
  • WpView
    Reads 20,438
  • WpVote
    Votes 1,121
  • WpPart
    Parts 30
littafine da ke dauke da rayuwar wata yarinya bakauya da wani dan sarki , mahaifiyarta mahaukaciyar ce kuma kurma ce , babanta Makaho ne sannan kuma gurgu ne . Tun hduwarsu ta farko suka aikata ma junansu laifin da ba wanda zai iya yafema wani har suka girma da burin daukar fansa ,duk da sunyi rayuwar Abokan taka batare da sunsan sune makiyan nan ba masu burin daukar fansa ga junansu . ku dai bibiyi wannan labarin dan ganin yanda zata kasance tsakaninsu
DEEDAT by rashmarrka
rashmarrka
  • WpView
    Reads 136,368
  • WpVote
    Votes 7,211
  • WpPart
    Parts 58
Labarin wata yarinya ce wacce yan uwan baban ta suka tsane ta akan kyanta suke tunani ko aljanace hakan zaisa sudawo kano da zama matashi mai jin kai dagirman kai abokanan sa suna kiransa below eyes sojane baya daukar wasa mace bata gabansa kwatsam yaje kano meeting haduwarsu tafarko da sa imah bata ganiba tazuba masa ice cream koyaya zata kaya kubiyoni Domin jin yanda zata kaya
KISHIYA KO BAIWA???. by RealEesha
RealEesha
  • WpView
    Reads 16,700
  • WpVote
    Votes 942
  • WpPart
    Parts 30
Labarine me Cike da makirci,'kissa,biyayya,dakuma zazzafan soyayya mecike da ban tausayi
ƊAN BA ƘARA COMPLETE by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 7,430
  • WpVote
    Votes 750
  • WpPart
    Parts 15
Salati goggo ta rafka tana ja da baya cikin tsoro take Fad'in, " me nake gani ni hansatu kamar danyen kifi ke mejidda zo ki tayani gani " mejidda atunaninta rikicin Goggo ne tana daga zaune ta cewa Goggo, " tunda kifin Kika gani ay shi d'in ne, kema Goggo Banda abinki kifin k'afa garshi da zai shigo cikin gida bama nan, idan nace kinfiye rigima kice zan gaya miki magana " ganin kifin na yi Mata murmushi yasa Goggo ta K'ara rafka wani salatin tana sakin tunkunyar tana yowa gaba, mejidda dariya takewa Goggo harda rik'e ciki tace, " Goggo wai me yake faruwa ne Dan Allah ko kunyar gudu bakiji ba? gudu kikeyi amma kamar me rawar Etigee" Goggo Bata bi ta Kan mejidda ba ta rabe ajikin katanga tana leken tunkunyar data jefar ,wani Kan kifi ta hango suna had'a ido ya K'ara kashe Mata ido daya😉 sannan ya washe Mata baki😃, daskarewa Goggo tayi cikin tashin hankali ta mik'a hannu tana nunawa Mejidda kifin, da saurinta Mejidda ta K'arasa gurin ba shiri ta dakata musamman yanda taga Kan kifin Yana wangale Mata baki, k'ank'ame Goggo tayi tana ihu cikin tashin hankali Take Fad'in, " wayyo Goggo Kan kifi Yana wangalen Baki zai cinyeni, ki taimake ni Goggo na yi gamo da Aljanin kifi ". Ita kanta Goggo abun tsoro yake Bata Amma sai ta D'an dake ta K'ara lek'awa Amma ga mamakinta sai taga tukunyar wayam, ko irin alamun jinin kifin babu. Goggo ta Jima tana kallan tukunyar Amma ko d'ishin kifi Bata gani ba, zame mejidda take Shirin yi daga jikinta caraf ta Kara k'ank'ame Goggo kamar za'a k'wace Mata ita, itama goggo Bata gama sake wa ba suna cikin Haka ba zato wani almajiri ya rafka ba ra, " Waaahiiideeeeeee " Me jidda ce ta Fad'a aguje cikin d'aki tabar goggo jikinta sai rawa yake ta Mara Mata baya, kafarta D'aya d'ingisa ta takeyi Amma alokacin Nan tuni ta take ta bata sani ba, Almajirin shi dariya ma abin ya bashi yi yake yana k'yak'yatawa, goggo dake d'aki ta cika fam Dan Jin yanda Almajiri ke b'ab'b'aka dariya, lek'awa tayi Dan tayi Masa magana
'YAR HUTU (LABARIN KAUSAR DA BINTA) Editing by Ishamoha
Ishamoha
  • WpView
    Reads 296,843
  • WpVote
    Votes 23,595
  • WpPart
    Parts 74
Ta taso a gidan hutu, gidan da ko tsinsiya bata dauka tsabar hutu, soyayya takeyi mai tsafta da masoyin ta kuma sanyin idaniyarta wanda da za'a bude kirjin ta se anyi mamakin irin son da take mishi amma sedai kash HUTU ya sangartar da ita ya kuma hanata kula da sanyin idaniyarta yanda ya kamata, shin wannan soyayya zata dore? Bakar wahalan da takesha ba karami bane a hannun matar uba, tsabar tsana da rashin son ganin er baiwar Allahn da ko shekara sha hudu bata karasa ba zata turata birni kuruwanci bayan tanada masaniyar cewar mafiyarta ta tsine mata duk ranar da ta bawa wanda ba maharraminta ba jikinta, shin tazayi abinda aka tura yi kokuwa ?
 (GYARAKANKI) by ummuelham
ummuelham
  • WpView
    Reads 23,707
  • WpVote
    Votes 1,157
  • WpPart
    Parts 35
wanna litafi me suna GYARAKANKI litafine da zai kawomiki magunguna da Suka kasance masu kyau da inganci Wanda Suka kunshi abubuwa kamar haka. Gyaran jiki wande yashifi bangaren kamshi da gyaran fuska d gyaran gashi da dai sauran su. Bangare nabiyu Kuma yashifi bangaren ni'ima na mata matsi magunguna masu inagan ci Wanda Zaki had da kanki batare da kinsha wahalaba Kuma basuda matsala ga lafiyarki Bangare na uku kuma bangarene da Zaki samu addu'oi dasuka shifi sihiri,janyo hankalin megida ,mallaka, addu'a domin rinjaye akan abokin gaba ,janyo hankalin saurayi,fahintar karatu,neman kasuwanci da daukaka ,d samun sa'ar jarabawa,Ina masu samun matsala da kishiya kizo ganaki,da wace uwar miji Bata santa ,Ina wace miji ke juya mata baya saboda abokiyar zamanta,ina iyayen da yaransu basa fahintar karatu ,Ina iyayyen da yarasu keyawan sasu magana Suma ganasu,kubiyoni domin samun dabaru da salon janye hankalin megida.
RUWAIDAH by Mumseeyama
Mumseeyama
  • WpView
    Reads 16,881
  • WpVote
    Votes 758
  • WpPart
    Parts 36
Labari ne mai cike da soyayya ma rikitarwa da kuma makirci wanda duk yanda kaso ka hana abinda Allah ya tsara to fa babu tsumi babu dabara sai ya faru.
TUBALIN TOKA by SalmaMasudNadabo
SalmaMasudNadabo
  • WpView
    Reads 12,666
  • WpVote
    Votes 779
  • WpPart
    Parts 21
bana tunanin zan iya rayuwar aure da bagidajiya d'iyar qanwar mahaifina wadda mahaifina ya za6a min a matsayin matar aure bayan ina da nawa za6in, ya rayuwata zata kasance zaman aure da mashayi manemin mata wanda sam baya so na bayan ina da nawa za6in nabi za6in iyaye na, wace irin rayuwar aure zanyi da mutunan ba sa son tallaka da wanne zan ji uwar miji na ko mijina?