Best
33 stories
ABBAN SOJOJI by BossBature88
BossBature88
  • WpView
    Reads 49,970
  • WpVote
    Votes 972
  • WpPart
    Parts 19
💋Romantic Love story💋 Labarin matashiyar yarinya wadda ƙaddara ke kaita aikatau gidan sojoji tayi shigar maza Amatsayin ɗan aiki, gidan Abban sojoji wanda yakasance chief of Army staffs, ƴa'ƴansa goma shatakwas duk maza masu riƙe da manyan muƙamai na sojoji 💋💘💞
TAFIYAR ƘADDARA  by NASRULLAH133
NASRULLAH133
  • WpView
    Reads 1,019
  • WpVote
    Votes 54
  • WpPart
    Parts 23
"Kai bil-adama! Kai bil-adama! Kai bil-adama! Wanne tsautsasayin ne ya jefo ka cikin wannan ƙasurgumin jejin namu, Jejin Balkaltum Jejin halaka? Ya kai bil'adama kai sani cewa wannan Jejin Balkaltum birnin mune fadar muce bugu da ƙari masarautar muce, wannan ce nahiyar mu duk wani bil'adama da ya yi ƙokarin shigar mana masarautarmu za muga bayanshi" ko da mai magana yazo nan a zancen shi shiru yayi.
ANYA BAIWA CE? by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 12,999
  • WpVote
    Votes 215
  • WpPart
    Parts 11
Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, " Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Babu damar dakatar da zuwan nata? Ya za'ay na gane ita ce dan na ɗauki matakin daya dace akanta?? " Boka ya ce, " Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita ɗin FILSIFI ce, abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci, tarraya ko haɗakar shuɗaɗɗun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta, zo ki duba nan " ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata wannan jan littafin da ke gefensa. Zanen wasu matasan mata ta gani guda uku sai dai duk cikinsu babu wacce zanen fuskarta ya fito sosai daga ƙasan kowacce anrubuta wani irin gwamammen rubutu, ta farko ya fara nuna mata yace, " Wannan da kike gani ita ce Muhaibish ita ta rayu ne tsawon dubbannin shekarun da suka gabata, Ƴar Sarkin jinsin Fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa ce, tunda take bata taɓa taka doron ƙasa ba " Zaro idanu Fulani Maryama tayi tana mamakin abinda ya faɗa, ta biyu ya nuna mata ya cigaba da cewa, " Wannan kuma sunan ta Kalimsiyat Ƴar sarkin fararen Aljanu ce amma ta nan doron ƙasa itama ta rayu atsawon dubbanin shekaru, acikin wani littafin bincike na karanta cewar ta yi rayuwa ne tun bayan zuwan Annabi Yusuf (A.S) ita kuma tunda ta ke bata taɓa nutsawa ƙarƙashin ƙasa ba a matsayinta na jinsin aljanu, kuma ita Kalimsiyat mace ce mara haƙuri mai faɗan gaske, kuma abinciken da nayi dukkan su biyun kashe su akayi bisa doron zalinci, kuma abinda zai baki mamaki kusan duka ruhinsu guda ne, sai dai banbancin nahiya da zamani. Sai ta Ukun su ita ce aka ce zata xo aƙarshen zamanin nan, sunanta Rayzuta ita ta haɗa dukkan abubuwan da waɗancen suke dashi harma da wanda suka rasa, ƴar baiwa ce me ɗauke da ɓoyayyun al'amura, ita kanta batasan da wannan baiwa tata ba."
SOFIA ✔ by DielaIbrahim
DielaIbrahim
  • WpView
    Reads 545
  • WpVote
    Votes 43
  • WpPart
    Parts 24
Nakasar rashin ƙwarin ƙafar da Sofia za tayi tafiya ita ce KALUBALE da kuma JARABAWAR da ta shafe kowacce jarabawa zafi da ciwo.Binchiken likitoci sun gane cewa Kafafuwan Sofia tun a cikin cikin mahaifiyar ta suka samu rauni wanda hakan ya samu sila ne ta dalilin Depression a turance kenan, to amma likitoci sun faɗa cewa da ace mahaifiyar bata da ciki da ita zata samu rauni (na rashin ji, ko kuma rashin gani, ko ciwon hauka) sai akayi rashin sa'a uwar na ɗauke da juna biyu sai abin ya sauka akan abin da ke cikin ta,Maimakon yayi ma uwar illah sai yayi ma SOFIA illah aka haife ta nakasasshiya kuma likitoci sun tabbatar ba lallai ta iya tafiya ba saboda jijiyoyin da zasu taimake ta wajan tafiya sun mutu basu da karfin da zasu iya zama lafiyayyun jijiyoyi. Shin da gaske ita ɗin MABARACIYA ce?, Yaya zata kalli AL'UMMA ko yaya AL'UMMA zasu kalle ta?, SADAUKARWA mai cike da rugujewar Mafarkai da Burika, SARƘAƘIYA, KADDARA, RAYUWA mai cike da ZAGON ƘASA.
MASARAUTAR MAYURNO by AuntiMamee
AuntiMamee
  • WpView
    Reads 28
  • WpVote
    Votes 0
  • WpPart
    Parts 3
Masarautar Mayurno nayi shine Dan dalilai biyu. Na farko nishadi na biyu kuma domin masu karatu susan wani dadaddan masarautar misulunci mai tsohon tarihi dake yankin Sudan.
WATA MASARAUTA by hauwahhh_
hauwahhh_
  • WpView
    Reads 5,458
  • WpVote
    Votes 258
  • WpPart
    Parts 7
Mulki da Sarautar Bizar Wa'innan abubuwa guda biyun sune duniyarshi, zai iya rasa komai da kowa ta dalilinsu, ciki kuwa Harda tilon d'ansa. Musamman ma a Irin wannan lokacin da babban asirin sa ke gab da tonuwa. Asirin da ya shafe shekaru Yana Dakon su, asirin da yasa shi kashe mahaifiyar shi, k'anin shi shi da kuma matar mahaifin shi,asirin da zata iya tarwatsa shi a cikin sakanni, asirin da koh Matan shi bata san da zaman shi ba, asirin da yake ganin ya rufe ruf kenan Har abada. Sai Gashi K'aramin alhaki Kaman Ateed Zarrah Yana qoqarin tonowa. A irin wannan lokacin bashi da wani zab'i illa yayi kare jini biri jini da d'an qanin nasa kuma Sarkin na Bizar wato Ateed Zarrah. Lokaci yayi da zaibi su Naqeeba da Sameed.
SIRRIN MU by nimcyluv
nimcyluv
  • WpView
    Reads 11,987
  • WpVote
    Votes 286
  • WpPart
    Parts 12
_Duniya makaranta a lokacin da wasu suke shiganta a lokacin ne wasu ke barinta,wasu na zuwa Duniya wasu kuma na barin Duniya, Rayuwa kamar shafin littafi ce,baka sanin abinda yake bangwan baya dole saika buɗe shafin gaba,muna zuwa Duniya ne ba tare da sanin abinda ke cikinta ba,wasu na zuwa a makance, wasu a kurmance,wasu kuma babu ido,kunan jin magana,uwa uba wasu basa zuwa da ƙafar takawa_ _Nakasa bata taɓa zama kasawa,haka kuma ƙaddarar data mai dashi nakashasshen zata iya sauya, kullum cikin zullumi yake, shin tayaya ne rayuwa zata kasance masa? tayaya yana nakashasshen zai iya mulkan dubban jama'a? Cikin ana tsangwamarsa bare ace ya zama shugaba,yaya jama'ar gari zasu ɗauke sa?tayaya zai gabatar da mulkin bayan Allah ya taushe ta hanyarsa rasa wani ɓangare na jikinsa?_ _Zuciya nada abubuwan ban mamaki,abinda kake so ita bashi take so ba,kullum yana ganin abin kamar mafarki amma yadda abin ke zamar masa a gaske shike masa mamaki,me zaiyi wanda zai samu farin ciki?me zaifi wanda zuciyarsa zata daina kewa ta daina ƙunci,duhun dake cikinta haske ya mamaye shi, FARAUTA shine abinda zuciyarsa ta yanke masa,abin mamaki shine tayaya nakashasshe zai iya zama mafarauci? Tayaya farauta zata masa maganin damuwarsa?.._ '''SHIN ZAI IYA KO A'A? YANA CIN RIBA A FARAUTAR KO A'A? KUNA TUNANIN WATA RANA NAKASAR SA ZATA IYA ZAMA RIBA GARESA?
IDAN BA KE by nimcyluv
nimcyluv
  • WpView
    Reads 15,580
  • WpVote
    Votes 332
  • WpPart
    Parts 17
True life story. labarin zanan ƙaddara wanda babu wanda ya isa ya hana shi faruwa sai Ubangiji al'arshi. soyayya mai cike da tausayawa wacce ƙaddara ta haɗa a lokacin da ba'ai zato ba.
BAƘAR MASARAUTA  by UmarfaruqD
UmarfaruqD
  • WpView
    Reads 1,298
  • WpVote
    Votes 28
  • WpPart
    Parts 18
*BAK'AR MASARAUTA* *Hausawa kan ce 'Ana bikin duniya ake na k'iyama, lokacin da wani yake kuka, wani dariya yake, kamar misalin yadda Uwa ke d'aukan ciki ta raine shi da wahalhalu kala-kala, tayi burin ta haife cikin domin ba wa jariri ko jaririyar duk wata kulawa da za su samar da tagomashin tarbiyya da kyawawan d'abi'u ga abin da ta haifa, ku hasaso yadda wannan uwa bayan duk ta gama wad'annan wahalhalun za ta tsinci kanta a bak'in yanayin da za a raba ta da abin da ta haifa ta hanyar zalunci, a yayin da ko cibi ba a yanke masa ba, shin da me za ku kwatanta?* *Tana da k'arfin ikon da kwarjininta kad'ai kan girgiza jama'ar da take mulka har su kasa nutsa idanuwansu cikin nata, shi kad'ai ya yi zarrar da yake ji ya isa jera kafad'a da ita, shin me ya taka ne duk da kasancewar sa bawa?* *Mata na rububin kasancewa da shi duk da bak'ak'en d'abi'un da suka yi wa rayuwarsa k'awanya, izza da guguwar mulki ta taka muhimmiyar rawa wurin kasancewarsa haka* *Da shi take kwana da shi take tashi! Tamkar Sallar farilla haka mafarkinsa ya zame mata wajibi a duk daren duniya, ta yi namijin k'ok'ari wurin gano shi amma sai dai kash....* *SABON SALO NE MAI GIRGIZA ZUKATAN MASU KARATU, DUK A CIKIN LABARIN BAK'AR MASARAUTA. KARKU SAKE A BAKU LABARI.
SHU'UMAR MASARAUTAR 1 by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 11,333
  • WpVote
    Votes 143
  • WpPart
    Parts 13
"Na sadaukar maka da kishiyata a wannan daren, shi ne tukwicin da zan iya yi maka." Ba ta jira cewarsa ba ta ɗora rigar a jikinta. Bamaguje ya gyaɗa mata sannan ya furta. "Za ku iya tafiya." Umaima ta yi masa jinjina da hannu sannan ta sake ɗiban ruwan da ta wanke fuska da shi ta nufi wurin da Maimuna ke zaune hannunta ɗauke da kunamar da Bamaguje ya damƙa mata. Abin da suka aiwata a farkon zuwansu yanzun ma haka ne ya faru, sai da suka koma daidai wurin da suka buɗe ido suka gan su tun farkon zuwansu sannan, Fulani Umaima ta ɗaga ƙahon ta runtse ido ta busa haɗe da kiran sunan Bamaguje. Ƙamshin ɗakin Fulani ne ya ankarar da Maimuna dawowarsu gida, cike da girmamawa ta zube ƙasa ta furta. "Allah huta gajiya uwar gijiyata."