Ya zakiyi idan aka ce mutumin da kike nema ruwa a jallo shine subordinate naki da kuke tare a kodayaushe ba tare da kin sani ba?
Ya zaki yi idan aka ce mutumin da kike nema ruwa a jallo miji ne a gareki?
..
#ZAHRAN GADANGA
Labari ne da ya kunshi ilmantarwa, fadakarwa, tare da nishadan tarwa. sannan yazo da sabon salon da yasha banban da sauran labaran da kika/ka taba karantawa.
Sultan ya shigo cikin gidan yana duba versace wristwatch din shi.
A hankali yayi sallama ya shiga main entrance wanda ke leading dinshi to parlour din da hajiya zaynab ke zaune.
Ta amsa tana kallon shi da murmushi
Sai yanzu ka iso?
Kamar wanda ya taho daga sokoto.