beautyjiddah's Reading List
46 stories
GOBE NA (My Future) by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 165,845
  • WpVote
    Votes 17,199
  • WpPart
    Parts 65
Babu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta kasance. Daga ni sai ire-irena mu ke iya labarta yadda mace ta ke ji idan aka keta haddin yarta ko kuma ita kanta! Ina ma ace yau haddina ni Halimatu aka keta ba na yata ba? GOBE NA... Zawarcin Halimatu... *** *** *** Babu wanda zuciyarsa ta raya masa sai matar nan, sosai ya maida hankali yana kallon gurin da take zaune tare da yaranta, the way ta take sharar hawaye ya kara karafafa zatonsa a kanta, labarin yarsa ya shigo ciki duk kuwa da bata fadi sunansa ba ko sunan yarsa sai dai ta fadi cewar mahaifin yar ya zargeta da kisan yarsa saboda kaddarar mutuwarta ya fada mata, kamar yadda kadarar gushewar hankalin abokin aikinta ya fada a kanta, an keta mata haddi an ketawa yarta, mijinta ya ci zarafinta, a kokarin kwatar hakkin yarta mijinta ya saketa, ga labarin samun aikin kamfanin da tai ya shigo ciki sai dai shi ma bata fadi sunan kamfanin ba..... Wani irin kallonta yake, har ya ji kamar gilashin dake idon sa ya tare ganinsa sai ta ya cireshi yana cigaba da kallonta, ita kuma ta soke kai kasa yana ta latsa waya tana sharar kwalla, wa akai wa fyade? Wacen karamar ko babbar? No wait mutunen da take bawa abincin a kusa da kamfaninsu abokin aikinta ne? Is that why take kokarin kula da shi? Waye mijin na ta? Waya ke bibiyarta? A lokaci daya ya jerowa kansa wadannan tambayoyin, da bashi da amsar su, and he can't take his eyes on her kamar his life defend on her.
IMTIHAL (COMPLETED) . by Nafeesat_Anka1
Nafeesat_Anka1
  • WpView
    Reads 150,330
  • WpVote
    Votes 8,253
  • WpPart
    Parts 40
Labarin wata yarinya ne data had'u da jarabawan rayuwa, soyayya me had'e da sarkakiya, da tarin rikici, kada Ku bari a baku labari 💖😍
MUNAFUKIN MIJI by nimcyluv
nimcyluv
  • WpView
    Reads 79,122
  • WpVote
    Votes 3,800
  • WpPart
    Parts 53
Na kasa fahimta da gasgata abinda zuciyata ke ayyana mini a kansa, SO ne ko BIRGEWA?. Komai nasa birgeni yake, ban taɓa ji ko ganin wanda ya haɗa abu ɗari bisa ɗari ba sai shi ɗin, ba zan kira hakan da jarabta, domin ko mahaifina bai sha ba akan yadda nake jin Mijina, bana ganin laifinsa sai nawa ina jin ban kyauta ba, na masa ƙwauron soyayya, rashin wadataccen abinci bai taɓa damuna ba, hatta ruɓewar da yarinyata tayi a ciki. ranar dana fahimci mara gurbi nake aure, matacciyya na zama, ina rayuwa cikin duhun kabarin da babu mai fiddani tambayar da zuciya ke mini me ya sanya ya zama MUNAFUKIN MIJI...
MARAICIN 'YA MACE by _bambiee
_bambiee
  • WpView
    Reads 70,651
  • WpVote
    Votes 6,580
  • WpPart
    Parts 36
Labari ne na wata yarinya da ta taso cikin tsana tsangwama wajen iyayenta. Tun da ta taso ta fara fuskantar matsaloli daban daban wajen iyayenta Inda ta fara tunanin anya ta hada wata alaka dasu kuwa? Ta fitar da rai daga samun wata soyayya ta iyaye kwatsam Allah ya had'a ta da Wani saurayi inda ya zamo gatan ta ya mantar da ita wahalar da tasha a baya...
A JINI NA TAKE by Aishatuh_M
Aishatuh_M
  • WpView
    Reads 69,992
  • WpVote
    Votes 3,092
  • WpPart
    Parts 12
Labari ne daya kunshi masarautu biyu; Masarautar Katsina, wacce take cikin Nigeria da kuma Masarautar Damagaran, wacce take cikin Kasar Niger. Labarin yayi duba ne da rayuwar Yarima Bilal, wanda rashin magana da miskilanci ya kanja ya shiga tarun matsaloli, wanda hakan yake haifar mashi da auren Zeenah Kabir Muhammad. Diyar Bafade da kuma baiwa. Me zai faru a rayuwar auren da aka hada miskili da kuma masifaffiya? Wanda dama tun farkon haduwarsu da masifa aka fara har yakai ga ya kure hakurinta ta sharara mashi maruka biyu? Shin ko zasu samu zaman lafiya kuwa? Bilal wanda ya kasance zuciyarshi a kulle take tun bayan rasuwar mahaifiyarshi zai bude ma Zeenah ita? Ya rayuwa zata basu bayan Zeenah ta fada soyayyarshi sai kwatsam Juwairiyya ta kunno kai? Wane hali Bilal zai shiga a lokacin da Fulani ta bankado wani tsohon sirri dake tsakaninsu? Fulani fah? Wacce take uwar gida kuma mai kula da hidimomin Masarautar Katsina gaba daya? Zata rufe sirrin data gano tsakanin Zeenah da Bilal dan gujewa tarwatsewar farin cikinsu? Abu daya ne zai kai ga na biyu, wanda har Bilal zai tsinci kanshi an mashi shamaki da Masarautar Katsina, hakan zai dangantashi da Masarautar Damagaran! Ku biyo Yar Malumfashi domin jin yadda labarin zai kasance.
BA GIRIN-GIRIN BA  by Ummu-abdoul
Ummu-abdoul
  • WpView
    Reads 62,002
  • WpVote
    Votes 8,387
  • WpPart
    Parts 36
BAN YARDA A YI COPYING DAGA NAN ZUWA KO INA BA, YIN HAKAN SHIGA HAKKIN MALLAKA NE ANA IYA MANA HISABI AKAN HAKAN Burin dukkan iyaye shi ne su aurar da ya'yansu da sun taka munzalin aure musamman ya'ya mata. Hakan ya kasance daga cikin Addini da Al'adunmu. Rashin aure kan haifar da damuwa a zukatan iyaye da su kan su ya'yan amma kamar yanda addini ya koyar da mu cewa "Komai da lokacin sa" shi ma auren ya shiga sahun "komai" ɗin. Gaggawa da kwallafa ran akan sai anyi aure ya sa da yawa daga cikin jinsinmu yin KUSKUREN da har su mutu suna nadamar sa. Jinkiri kan sa mutane su rasa tauhidinsu na duk abin da zai faru a doron kasa ya kan faru ne a bisa ga ikon Allah, in bai so ba hakan ba zai faru ba, kuma komai rubutacce ne, kuma alkaluma sun bushe. Sai su zama su na takurawa wanda aurensu ya zo da jinkiri da kalaman "Yaushe za ki yi aure?" ko kuma "Kin ki aure ko" abin tambaya ga duk wanda ya ke ɗaukan aure a wani hanyar nuna Darajan mutum shi ne "mai ya hana musu mutuwa" don kuwa aure, haihuwa da mutuwa lokutansu rantsattse ne. Babu abin takaici kamar a ce mace don ba ta yi aure ba, sai ma su kiran ta ki aure su zagayo suna neman ta da lalata don a ganinsu tun da ta ki aure toh mazinaciya ce. Wacce gaggawa ya dibe ta sai ta ba da kai bori ya hau don a tunanin ta hakan zai sa su aureta. Wasu daga cikin kawayensu kuma kan ɗauki rashin aure dalilin yanke zumunci da su, saboda a ganinsu babu kaskanci kamar rashin aure ko da kuwa auren da za'a rike zai kai su ga wuta ne ba Aljannar da kowa ke yin aure don nemansa ba. Tsabagen son aure ya sa tun yarinya na kwailar ta ake dasa mata ra'ayin duk abin da za ta yi don farin cikin wani ɗa namiji ne ba wai don kanta ko farin cikin mahallicinta ba. Sai ka ga don yarinya ta ci kwalliya ba za'a nuna mata tayi kyau don ta ji daɗi ba sai dai a nuna mata tayi kyau za ta burge wani ɗa namiji. A haka za ta taso in ba'a taki sa'a ba sai ta kai ga siyar da mutuncin ta duk don ta birge namiji.
TAZARAR DA KE TSAKANINMU by Ummu-abdoul
Ummu-abdoul
  • WpView
    Reads 147,671
  • WpVote
    Votes 15,094
  • WpPart
    Parts 41
Biyo mu sannu a hankali don jin TAZARAR da ke tsakanin Dee Yusuf da Amatullah. Updates zai dinga zuwa duk ranakun Laraba da laha3. Ku biyo Ni Safiyyah Ummu-Abdoul tare da Khadija Sidi don jin wannan TAZARAR
KYALKYALIN KAUNA by MSHAKURworld
MSHAKURworld
  • WpView
    Reads 70,425
  • WpVote
    Votes 1,555
  • WpPart
    Parts 48
A story about a drug lord with an innocent girl suffering from dyslexia
DR SAHEEB by Z11AMN
Z11AMN
  • WpView
    Reads 28,784
  • WpVote
    Votes 957
  • WpPart
    Parts 15
the story of arrogant doctor
🤍Dr.TAHEER🤍 by aysharano22
aysharano22
  • WpView
    Reads 133,857
  • WpVote
    Votes 5,618
  • WpPart
    Parts 58
Dr.TAHEER labari ne mai cikeda soyayya mai tsuma zuciya...labarin wani matashin likita daya kamu da matsananciyar soyayyar yarinyar da ya raineta a hanunshi..yarinyan dake kiranshi da suna daddy kasancewarshi cousin brother din mahaifiyarta daya girme mata da shekaru biyu...it's an interesting love story indeed 😊