AliyuShamsiyya9's Reading List
172 stories
KUƊIN ZOBE by Autan-Eloquence
Autan-Eloquence
  • WpView
    Reads 529
  • WpVote
    Votes 50
  • WpPart
    Parts 4
Tarin Ƴan Jaridu ne ke gewaye da Ƴan Sandan da suke a tsaitsaye a bakin katafaren gate na Luxury Hotel ɗin da ke birnin Maiduguri, gaba ɗaya Ƴan Jaridun sun gama hargitsa ilahirin wajen da hayaniyar su ta watsa labaran ji-da-gani kai-tsaye a ƙafafan yaɗa labarai. Daga cikin harabar Hotel ɗin kuwa, Sufeta Hassan ne da Sajen Gambo tare da wasu ma'aikatan Asibiti ke tsaye a jikin motar ɗaukan marasa lafiya ta General Hospital Maiduguri. A gaban su kuma gawarwaki ne guda Uku jere a ƙasa lulluɓe da fararen ƙyallaye, wanda tuni jinin da ke ɓul-ɓula daga jikin gawarwakin ya gama sauya musu launi daga asalin kalar su ta farare.
ZAHRA TAWA CE  by FatimaZois
FatimaZois
  • WpView
    Reads 97,932
  • WpVote
    Votes 6,288
  • WpPart
    Parts 163
Ya zakiyi idan aka ce mutumin da kike nema ruwa a jallo shine subordinate naki da kuke tare a kodayaushe ba tare da kin sani ba? Ya zaki yi idan aka ce mutumin da kike nema ruwa a jallo miji ne a gareki? .. #ZAHRAN GADANGA
KARAN BANA by ZahraSurbajo1
ZahraSurbajo1
  • WpView
    Reads 19,928
  • WpVote
    Votes 528
  • WpPart
    Parts 1
hmmm karan bana maganin zomon bana,shigo ka karanta kaji yadda yaya ke soyayya da kanwarsa uwa daya uba daya,shin da saninsa yakeson kanwarsa uwa daya uba dayan?,se kun shigo daga ciki zaku gane haka.
DAGA ALLAH NE by FatimaZois
FatimaZois
  • WpView
    Reads 43,135
  • WpVote
    Votes 2,267
  • WpPart
    Parts 45
soyayyar iyayensu ne tayi transferring xuwa kan diyansu da basu samu damar yin aure va "haidar zahra" Soyayyar da haidar ke mah zahra ita Sanya yake ganinta tun a mafarki kafin mah a haifeta alhalin kasar su mah ba daya bace
Hasken Lantarki (Completed)  by Aynarh_dimples
Aynarh_dimples
  • WpView
    Reads 154,679
  • WpVote
    Votes 5,103
  • WpPart
    Parts 16
Dan mutum yana maka wasa da dariya kuma ya nuna akwai aminci tsakanin ku ba lallai bane yana kaunar ka. Makashinka yana tare da kai, da dan gari ake cin gari... Ku biyo ni
Kudiri by Gimbiya229
Gimbiya229
  • WpView
    Reads 170,343
  • WpVote
    Votes 12,629
  • WpPart
    Parts 39
Hausa story of love, commitment and sacrifice. Yusuf and Asiya belong to different classes with nothing in common. Well, except for humanity. An incident had occurred which brought them together. Will their shared sacrifice bring them happiness and perhaps, everlasting love?
AMAREN BANA by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 143,611
  • WpVote
    Votes 9,319
  • WpPart
    Parts 17
#9 in romance on 05/09/2016 "Wai ina son ki fada min, me yake damun ki ne, da za ki haddasa irin wannan fitina, sannan ki zauna lafiya, kamar ba abinda ya faru?" Dubansa ta yi a sanyaye, sannan ta-ce. "Ina da dalilina." "Wane irin dalili ne, zai sa ki na ji, ki na gani auren iyayenki ya mutu? Idan banda irin gurguwar tunani irin naki? Ashe ki na da halin yin gyara a wannan al'amari, ba za ki yi ba?" Mikewa ya yi daga kan kujerar zai tafi, da sauri ta kamo bakin rigarsa, ya tsaya, ganin zai saurareta, ya sa ta sakar masa riga. "An fada maka ni ma ina jin dadin ganinsu da na ke yi a haka ne? Sam, ba son raina bane, amma na daure na kauda kaina, saboda mu kawar da gagarumar matsalar da ta fi wannan. Na san halin Momi, tana da fada, tana da rashin son gaskiya, amma kuma haka tana da saurin nadama, na san za ta nemi afuwa, kuma Abba zai saurareta. Sai dai wannan tafiyar, dole ka taimaka ka ba ni goyon baya, don mu shawo kan al'amarin nan tare." Kallonta ya yi, ita ma duk ta jikkata, ta jejjeme ta zama wata iri, tabbas yadda take ji haka yake ji, koma fiye, don bayan baya sonta, ya tsani uwarta, sannan yana mutuwar son Meena. "Ki yi hakuri, amma ba zan iya aurenki ba." Ranta ya baci kwarai, har ya juya zai fita ta-ce. "Saboda me ya sa ba za ka iya aure na ba? Saboda me ya sa ban kai matsayin na zamo matarka ba?" "Ki fada min, ta yaya zan iya zama dake, alhali ki na matsayin 'yar matar da na tashi da tsanarta a zuciyata?" "Wane irin dalili zai sa maka tsanar mahaifiyata, har da zai sa ni ba za ka iya aurena ba?" Shiru ta yi don ta ji dalilin wannan tsanar.
MAIMAITA TARIHI (DANDANO) by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 130,692
  • WpVote
    Votes 6,326
  • WpPart
    Parts 14
***Wannan labarin somin tabi ne. Za a iya samun cikakken labarin akan manhajar Okada cikin watan Janairu, 2021. In sha Allah*** *** #1 aure 9th 01 2021 Tarihi yana kunshe da fuskoki da dama. Banda na wucewar abunda ya shude harda kasantuwar abunda ya shude a rayuwarmu ta yanzu. Sannan a duk lokacin da aka Maimaita tarihi, farashin yana karuwa ne fiye da kima. Hakan ne ya faru da Maryama-Siddiqa a lokacin da ta dauki alwashin bazata bari ta maimaita tarihi ba duk da kasancewa dukkan alamu sun nuna hakan ne yake shirin faruwa. Bayan zaman aure na tsawon shekaru ashirin tare da mijinta Sufyaan Barkindo Sajoh, sun gamu da kalubale wanda ya sa Sufyaan tono abunda ya dade da burnewa yayinda Siddiqah ta jajirce wurin neman 'yancinta daga rayuwar da ta samu kanta a ciki. Sai dai komai ya kwabe musu a lokacin da suka samu masu kalubalantar matakin da suka dauka. Siddiqa ta gamu da abokan hamayyar da suke neman rayuwarta wadanda bazasu tsaya ba har sai sun ga karshenta. Shin zata zakulo kanta daga wannan kangin, ta samu rayuwar da ta yi karfin halin mafarki wa kanta, ko kuwa za a maimaita tarihi ne? Shin wani bangare Sufyan zai zaba idan tura ta kai bango? ***