Wani kallon banza ta watsa mata tace "To bari kiji irin tsanar da nayi masa, da Allah zai k'adda yazamo Aljanna a tare zamu shiga to wallahi ni wuta zan wuce direct, akan dai mushiga atare da juna gara in zamo 'yar ja....
Bayan gamayin dinner d'insu suka balle da hira, sosai suka tattauna da juna a inda Hakeem yayi ta bashi baki akan yazamo mai yarda da qaddara abisa laluran data sameshi. Yunus cike da annashuwa yayi ta godiya game da kulawansa akan laluranshi ganin yarda bai kyamace shi ba sam.