maryamabdullahiahmad's Reading List
11 stories
AUREN DOLE by Usman_Babura
Usman_Babura
  • WpView
    Reads 573
  • WpVote
    Votes 22
  • WpPart
    Parts 1
AUREN DOLE Zaune nake a katafaren falon gidansu wanda yake dauke da manyan kujeru na Alfarma . Tun karfe 4:30 Pm na yamma nake zaune a falon gidan na shafe kusan mintuna 30 bata fito ba , Ina zaune ina danna wayata saiga kanwarta maryam, ta shigo falon dauke da plate ruwa ne da kofuna akan plate din tace dani ina wuni gashi inji Aunty Aisha , cikin murmushi nace nagode kanwata,ta tashi zata fita nace ina antin taki haryanzu bata gama shirin ba , cikin yanayin murmushi maryam tace haryanzu kwalliya take, nace da ita shikenan nagode. Naci gaba da zama can saina farajin wani irin kamshi mai gusar da tunani , Ashe Gimbiyar tawa ce Aisha take tafe daga kaina da zanyi sai hada ido mukayi, Aisha farace doguwa, kyakykyawa ta sakko da gashi kanta har gadon bayanta , gata mai sanyin murya, ga dumple ta hada komai na kyau da ake bukata ga " ya mace, Cikin rangwada da salo na tafiya, Aisha ta karaso inda nake zaune cikin sanyayyiyar muryata tace yayana kayi hakuri na dade ko? , Cikin Annushuwa da farin ciki nace haba ni banga dadewa ba, tadan sadda kai kasa tayi murmushi, tace yayana amma baka sha ruwan nan ba , cikin shawagaba ta fadamin haka, a yanayi na shauki nace wanna ruwa zansha banga sarauniyar mata ba, muna cikin haka kwatsam saiga daddy dinsu ya shiga falon ganinsa danayi yayi matukar girgiza ni matuka saboda nasan halinsa baya kaunar talaka, hada ido mukayi dashi sai naga ya harare ni , na gaishe shi bai amsa ba, ita ko aisha binmu kawai take da kallo, tayi mamakin abunda mahaifinta yayi min , a lokacin tabi daddy din nata daki domin ta bashi hakuri ta kuma fada masa wanene ni a wajenta, ko saurarenta bai ba ya daka mata tsawa ! Ina falo amma tsawar ta gigita ni, saiji nayi yace wancan dan gidan uban waye kika kawomin cikin gida banace karki kara kawomin diyan talakawa gidan nan ba, kuma ki saurareni da kyau gobe dan Aminina , Zaizo gidan nan ku sasanta kanku,
BAMBANCIN ƘASA(Battle to reach) by Siyamaibraheem
Siyamaibraheem
  • WpView
    Reads 1,844
  • WpVote
    Votes 251
  • WpPart
    Parts 35
"Make sure you take good care of your sister duk runtsi da tsanani kar ki bari ki karaya ko ki sami rauni dangane da abin da kika saka a gaban ki,ki sani,horon da kika samu sama da shekaru ashirin da uku tun kina jaririyar ki,farat ɗaya ba'a isa a ƙwace maki shi ba sai in ke kika bada damar yin hakan dan haka nake ƙara jadadda maki kamar yadda kika yaƙi sojoji ɗari biyu da talatin da bakwai da aka sako su daga masarautar OTTOMAN haka zaki jajirce ki cigaba da yaƙar duk wasu maƙiyan ki da zasu biyo ki,make sure you find your sister and take her far away from Ottoman promise me"!!haka jikin ta na ɓari gaban ta na faɗi zuciyar ta na daɗa bushewa sakamakon ƙudiri mai nauyin gasken da ta alkawarta ma kan ta.. Wuf ta miƙe ta tashi tsaye ran ta na tafasa zuciyar ta na rura mata wani irin hucin ɓacin rai.. Kamar ƙiftawa da bisimillah ta zari doguwar takobin da ke gefen ta lulluɓe cikin marufin fatar sa da ke sagale a jikin rigar ta ta soƙe shi da shi ta daɗa tursasa takabin ciki ta juya shi ta yadda zai illata kayan cikin sa,ta cire takobin ta kuma yunƙurawa da iya ƙarfin ta ta kuma caka mai a daidai inda ta cire na farkon..ƙasa yayi yana nishi daga bisani numfashin sa ya ɗauke ɗif.. Kallon matar tayi idanun ta a ƙuntace ta mata kallon ƙarshen sannan ta juya ta yanki daji tayi wucewar ta.....!!!
ARNAN DAJI by feedynbash
feedynbash
  • WpView
    Reads 44,686
  • WpVote
    Votes 1,638
  • WpPart
    Parts 26
Action fantasy romantic
AMSOSHIN TAMBAYOYINKU 2 by sameehasusman
sameehasusman
  • WpView
    Reads 59,955
  • WpVote
    Votes 1,381
  • WpPart
    Parts 200
JANABA TA SAME NI, BAN YI WANKA BA SAI HAILA TA ZO MINI, YA ZAN YI WAJEN YIN WANKA
+7 more
YA JI TA MATA by miss_untichlobanty
miss_untichlobanty
  • WpView
    Reads 88,444
  • WpVote
    Votes 8,201
  • WpPart
    Parts 63
Wannan labari me suna YA JI TA MATA shine littafina na uku.... Labarin wani saurayi ne Wanda bashida aiki sai zina, a cewar sa ba laifinsa bane Allah ne yayi sa hariji. Toh hakan ne yasa iyayen sa suka rufe ido sai yayi aure amma fa an gudu ba'a tsira ba domin kuwa babu wacce take iya zaman sati biyu dashi tsanani kwana 10 sai su gudu. Toh fa an Sami matsala domin reshe ta juye da mujiya inda Allah ya hadosa da Wanda ta fisa jaraba toh yanzu kuma shi ke gudu. Wai ya za'a kwashe ne a lokacin da iyayen sa sukace bai isa ya saketa ba kamar yadda ya dafa kur'ani cewa bazai saketa ba? KU BIYONI CIKIN WANNAN LABARI NAWA DAN JIN YADDA ZA'A KAYA. SAURAN LABARAI NA: 1.KURUCIYAR MINAL 2. YARINYAR CE TAYI MIN FYADE AND NOW 3. YAJI TA MATA.
DUNIYA MAKARANTA CE. by queenbk2020
queenbk2020
  • WpView
    Reads 27,315
  • WpVote
    Votes 2,417
  • WpPart
    Parts 52
#10 Hausanovel, 15 June 2020. #47 Nigeria june 2021. Duniya Labari, Duniya Makaranta, Duniya Kasuwa, Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa kafa su rusa. Ta rasa me ɗaya zata yi taji sassauci a halin da take ciki, a ɓangare guda kuma ta rasa da wane ɗaya zata ji cikin abubuwa barkatai da sukai mata katutu a cikin wannan duhun dare, shin za taji da halin baro innarta da tayi cikin mawuyacin halin da bata da gata sai Allah? Ko da mutuwar Baba zata ji? Ko za taji da dabi'ar ƴan gidan su ne? Ko ko za taji da hanyar gidan su Naty data ɗinke mata ne? ta jefa ta tsundum cikin wata duniya sabuwa da bata san kowa da komai game da ita ba? Shin ita Bintu wai dama haka rayuwar take da tarin ɗaci da maƙaƙi a wuya? Haka duniyar take da kwazazzabe da tarin ramuka a cikinta? Nan ta ƙara sautin kukanta tana darzar majina. *** Garin yayi tsit baka jin komai sai kukayen tsuntsyen da suke ma Bintu rakiyar da bama tasan da shawagin su ba. Iskar dake ta kaɗa yaloluwar doguwar rigar dake jikinta yana wasa da jelar shukun kanta ma bata san da zaman shi ba, domin duk wasa sensory receptors da neurotransmitters dama duk wasu jijiyoyi dake aikin kai ma ƙwaƙwalwarta rahotanni. Sun tsaya cak sun tafi hutun taƙaitaccen lokaci. *** Tayi tafiya mai tsawo! ita kanta bata san adadin tsowon data ɗauka tana tafiya cikin babin ƙaddarar rayuwarta ba, take kuma aka maido nepa a cikin ƙwaƙwalwarta, tsayawa tayi cak ta dubi gabas da yanma, kudu da arewa amman ba hanyar da tai mata tayin sani.
DIYAR DR ABDALLAH  by Aynarh_dimples
Aynarh_dimples
  • WpView
    Reads 46,910
  • WpVote
    Votes 6,343
  • WpPart
    Parts 32
Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wannan yanayin ba. Yanayin da zai zama useless baida amfani. Sai yanzu ya lura da dalilin dayasa ya kasa barci. Ba komai bane illa wannan sabon shafin dake baƙunta sa. A hankali yake mamayansa, ya shammace shi cikin dare. Yanzu gashi yazo yayi kane kane yana kokarin gina muhalli cikin rayuwarsa. Tabbas zuciya batada ƙashi, kuma ba'a kwaɓanta. Amma idan tace zatayi mashi abinda yake tsammani bata kyauta mashi ba. Tayi mugun cutan sa. Ya kamata tayi tunani saboda abinda take so yafi karfin ta. Runtse ido yayi ransa yana mashi ɗaci. Shi dama dukansa akayi da itace zai fi jin daɗi akan raɗaɗin dayake ji cikin ransa. Akwai abubuwa da ke faruwa da bawa wanda baida ikon hanawa. Kamar yadda zuciyar sa take raya masa ga abinda takeso yanzu, idan kuma bata samu ba tabbas zatayi masa tijara. Toh tijara na yaushe kuma, fafur ta hanashi barci. Murmushi yayi na takaici, "akwai ƙura," yace a fili. Dimplicious Empire, ku biyoni sannu a hankali domin jin wannan labari. Love you Fisabillahi ❤️
EL-BASHEER by Nuceeyluv
Nuceeyluv
  • WpView
    Reads 24,211
  • WpVote
    Votes 1,713
  • WpPart
    Parts 36
EL-BASHEER, Yana kaunar ta dukda baida halin ya nuna mata Hakan a dalilin halin data same shi a ciki saidai kullum Addu'ar sa Allah ya kawo Masa karshen Wannan aikin da yake domin ya bayyana mata dunbin soyayyar da yake Yi mata, Wutar soyayyar ta na Kara ruruwa a ransa a Duk lkcn daya kalli kyawawan kwayar idonta Yana hango kulawa da tausayin sa da take hakama kaunarsa da take dukda ta same shi a halin HAUKA, lalle ba kowa bane zai aminta dakai ya zauna dakai a lkcn da aka Tabbatar baka da hankali ko kadan, LABARI ne me cike da Abubuwan ban mamaki, MAHAUKACI ne shi a zahiri Amma a badini Shidin cikakken jami'in sirrine na farin kaya wato SS, bincike ya biyo ta gidansu sbd irin mutanen da yake rayuwa dasu Hakan yasashi maida kansa MAHAUKACIN dole domin gano gskyr Abinda ke wakana a gidansu, hakan ya bawa sauran mutanen gidan Daman cin Karensu Babu babbaka a ganinsu Dan masu gida baida hankali, oh🤔 Rashin sani yafi dare duhu Basu sani ba Ashe su yakewa kallon mahaukata, ikon God! Wai ya abin yake? Wai Menene asalin Abinda ake zargi a gidan nasu? Ku shigo cikin labarin dan ganewa kanku amsoshin dake ciki.
DARAJAR MACE by swriter09082
swriter09082
  • WpView
    Reads 1,671
  • WpVote
    Votes 130
  • WpPart
    Parts 8
Guru so nake ku fafe minshi kamar yadda ake fafe gwangwani karku raga masa ko da wasa ku tabbatar kun koya masa hankali. Da sunan Allah mai rahma maijin qai Wannan labarin qirqirane banyishi domin cin zarafin wata ko wani ba. 💞 Page1 💞 Mama ki taimakeni dan Allah karki bari baffa ya auramin wancan tsintaccen bana sonshi kamal nake so dashi zanyi rayuwa dan Allah ki taimaki rayuwata idan na rasa Kamal mutuwa zanyi ta qarasa cikin matsanancin kuka mai cike da tsantsar tashin hankali. Haba zeenatu nace ki kwantar da hankalinki idan kinga anyi auranki da wancan tsintaccen to ki tabbatar cewa ni harira bana numfashi,auranki da kamal kamar anyi angama domin awannan karon bazan lamunta ba domin nima inada haqqi akanku daza ake min hawan qawara,banda san kai ya aurawa khairiyya mana ko dan ita uwarta shafaffiya damaice"yar gaban goshi to nima na daina dauka ta qara cike da bacin rai. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 Khairiyya tunanin mai kake haka kwana biyu Ina hankalce dake kin rage walwala mai yake damunki cewar Ammi tana kallonta, shiru tayi to ita mai zatace shin cewa zatayi soyayyar Ahmad ce tasata damuwa ko kuwa cewa zatayi"yar uwarta dazai aurane yasata cikin damuwa,kin yi shiru idan baki fadamin ba wazaki fadawa ko kina da wata uwar bayanni ta tsinkayi muryar Ammi,bakomai Ammi kawai Ina tausayawa ya Ahmad ne tunda Baffa ya masa maganar auren nan yak cikin damuwa,shi Ahmad dinne ya fada miki haka cewar Ammi tana kallonta,a'a Ammi ni ce dai nake ganin haka,to yazamuyi khairiyya Baffanku ne sha'aninsa sai shi babu mai lanqwasa shi sai kawu Bala,saidai mu taya yaron nan da addu'ah domin Ina tausaya masa kasancewarsa mai haquri. 💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞 Ahmad ga wannan dubu talatinne sai ka fara rage gyaran gidan,gobe idan Allah ya kaimu zan je daqaiyyawa nasanarda kawu bala shawarar dana yanke domin zancen bana waya bane,to Baffa nagode Allah ya qara girma na gode cewar Ahmad da kansa yake
ƘWAI cikin ƘAYA!! by BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    Reads 1,501,455
  • WpVote
    Votes 121,601
  • WpPart
    Parts 106
Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wasu a cikin matsalolin zuminci, gidajen aurenmu, Tsaro, rikita-rikita, harma da ruguntsumi. Kai lamarinfa ba'a cewa komai, mai karatune kawai zai banbance tsakanin aya da tsakkuwar zancena bayan mun tsunduma cikin labarin tsundum