Hausa novel
3 stories
TABARYA....mai baki biyu by Mrsjabo
Mrsjabo
  • WpView
    Reads 38,322
  • WpVote
    Votes 2,432
  • WpPart
    Parts 22
" kin yaudareni BAHIJJA, ni zaki rainawa wayo, ki mai dani SAKARAI, ki rik'a saka wasu abubuwa a jikinki, wad'anda kinsan Allah bai Halicceki dasu ba?" Jikinta rawa ya fara yi kamar mazari, "Ahamd dan Allah kayi hak'uri." Ta furta tana share hawaye. Katseta yayi, ta hanyar d'aga mata hannu....
GIMBIYA SA'ADIYYA (Aljana Ko Fatalwa?) by PrincessAmrah
PrincessAmrah
  • WpView
    Reads 160,533
  • WpVote
    Votes 19,531
  • WpPart
    Parts 55
Haka rayuwarta ta kasance tsawon lokaci a cikin kwalbar sihiri. sai dai kuma a lokaci guda BOKA FARTSI ya yi watsi da alkawarinsa da KURSIYYA, ya fiddo ta tare da umurtar ta kan cewa ta ci gaba da bibiyar rayuwar KURSIYYA domin ta kwato wa kanta da kuma shi kanshi fansa. Ko wace ce wannan Kursiyyar? Wace ce wannan daga cikin kwalba? Wace irin fansa ce za ta kwatar wa kanta da boka FARTSI? Ku biyo ni a cikin labarin GIMBIYA SA'ADIYYA don jin bayanai game da abubuwa da dama.
GADAR ZARE by HauwaAUsmanjiddarh
HauwaAUsmanjiddarh
  • WpView
    Reads 401,595
  • WpVote
    Votes 19,019
  • WpPart
    Parts 85
A firgice ya mik'e daga inda yake zaune, yana kallon sauran abokanan nasa fuska cike da hawaye idonsa yayi ja sosai Buga kansa ya fara yi ajikin bango yana ihu yana cewa " sun kashe min kowa bani da kowa yanzu, zaman dirshan yayi a k'asa, yana ihu yana yarfa hannunsa, zumbur ya mik'e ya nufi fridge ya d'auko robar ruwa ya bulbulawa kansa "Akan ido na suka k'one gidan mu, mahaifiya ta, mahaifi na, k'anne na duk suka mutu akan kunne na ina jiyo ihun su *************** "Cikin waye wannan a jikin ki? uban waye yayi miki ciki? bazaki fad'a ba saina kashe ki, wayyo na shiga uku duk irin tarbiyyar dana baki abinda zaki saka man dashi kenan, cikin kuka tace " wallahi Aunty ban sani ba, idan za'a kashe ni ban san wanda yayi min cikin nan ba, nima ganin shi kawai nayi ajiki na, tafiya tayi ta bud'e durowa ta d'auko Qur'an ta d'ora akan ta tace " na rantse da wanda raina ke hannunsa bansan wanda yayi min ciki nan ba. Kanta tayo gadan-gadan tana nizaki rainawa hankali, ta shak'e ta idonta suka kakkafe ************** A cikin gidan yarin yake ihu yana kuka yace " sunci Amana ta, sunyi min butulci, na yarda dasu amma sun ci min amana sun had'a min GADAR ZARE Amintattu nane suka yi silar zuwa na gidan yarin, sun raba ni da kowa nawa sun raba ni farin cikina,cikin matsanancin kuka yace " wallahi koda zan rasa komai na rayuwata bazan kyale su ba. Sun mun sharri, sun had'a man makirci da GADAR ZARE ************* "Koken a cikin kayana kuma, kafin ya k'ara sa maganar dubbun police sun kewaye shi da bindugogi, Ana cikin haka wayarsa ta fara ringing, dakyar ya samu ikon d'agawa, ji yayi muryarsa ta tintsere da dariya yace " nine, d'an uwanka, kaga yadda nayi wasa da hankalinka ko, na nuna maka halin 'yan Adam Cikin rawar murya yace " mai yasa kaci amanata? " saboda ina santa, ita rayuwa tace kuma mallakina , Wani irin mahaucin ihu ya saki tare da buga wayar da k'asa .