ushe021's Reading List
88 stories
KAI NE JARUMI by HAERMEEBRAERH9900
HAERMEEBRAERH9900
  • WpView
    Reads 1,579
  • WpVote
    Votes 106
  • WpPart
    Parts 33
Talauci da arziqi dika na Allah ne..Amma Mai hankali me kad'ai yake Gane hakan...Tsakanin Rasheedah da Sakeenah akwai Wani al'amari Babba da yake buqatar hankulan ku makaranta...ku biyo HAERMEEBRAERH Dan Jin mene ne wannan al'amarin.....
SILAR AJALI  by Ummu-abdoul
Ummu-abdoul
  • WpView
    Reads 67,168
  • WpVote
    Votes 7,695
  • WpPart
    Parts 35
Duk manoman dake wucewa zuwa gona a KAUYEN MARKE idan lokacin damina ne sun shaida fuskar RAHANATU . sun tabbatar da itace wadda tafi duk wani dan adama bi ta hanyar.... Saboda nanne hanyarta ta zuwa makaranta. Dabi'arta ce zuwa makaranta, duk wani matashi dake kauyen da makwabtan kauyukan sun shaidata ne a matsayin daliba mai zuwa makarantar boko. Iyayenta basu da kudi, basu mallaki komai ba sai ita da kanwarta AMINA, daga su sai gatarin faskaren da mahafinta malam TANKO ya gada a wurin kawunsa, daga nan sai tukunyar da Rahanatu ta sani da ake dora musu abinci ba kullum ba. Kullum bata manta maganar babanta "karatun ki shine hanyar ceton mu, ke kamar gona ce da muke shuka muke fatan girban albarkacin noman mu anan gaba, karatun ki ne zai sa mu san dadin cire kudi mu biyawa kanmu bukata, karatun kine zai sa wata rana mu daina lissafa abincin da muke ci, karatun ki ne zaisa wata rana mu iya siyan sutura har mu manta adadin wadda muka mallaka, karatun kine zaisa a rika tunawa damu a matsayin masu rufin asiri. Dan haka kada kiyi wasa da karatun ki rahanatu" ba zata yi ba, saboda tana so taga iyayenta sun fita daga talauci. Ta sha alwashin haka. Sai dai a hanyar ta ta zuwa makarantar taci karo da shaidanin yaro HADI ALJAN. Yaron sarkin garin, yaci alwashin lalata rayuwarta koda ta hanyar fyade ne, bata bashi goyon baya ba, amma kuma ba zata iya hana shi ba Ba zata fadawa iyayenta ba saboda kada hankalinsu ya tashi Kota fada musu ba zasu iya komai ba babansa ne sarki. Ba zata kuma daina zuwa makaranta ba saboda canne fatansu yake. Ba zata iya salwantar da rayuwarta ta yarda dashi ba dan zai lalata rayuwarta. A haka ba yadda zata iya, yayi mata fyade. Ba zata iya fadawa iyayenta ba, duk da saida ta wuni a cikin gona cikin jinni, aka samu mai taimaka mata ta ceceta. Cikin da ya bayyana a jikin rahana shine ya zama silar tarwatsewar iyayenta da ita. Har ta tsinci kanta a birni.... A cikin tarragon rayuwa mai tsananin daci da burin daukar fansa...
'KAZAFI  by Ummu-abdoul
Ummu-abdoul
  • WpView
    Reads 16,773
  • WpVote
    Votes 1,966
  • WpPart
    Parts 12
Sau da yawa hotunan mu kan shiga kafofin sadarwa, tare da lbr mabambanta haɗe da hotunan wanda hakan kan iya zama Qaharu.
TSANINMU by Ummu-abdoul
Ummu-abdoul
  • WpView
    Reads 3,658
  • WpVote
    Votes 318
  • WpPart
    Parts 3
Duk abin da mutum zai zama a duniya sai ya bi ta wasu matakala wanda ke manne a jikin tsani, tsanin kan iya zama na katako wanda ruwa da rana ke saurin lalatasu wani tsanin kuma na karfe ne da sai dai yayi Tsa-tsa. Ana samun tsani na azurfa ko lu'ulu'u ko ma zinari wanda hakan bai isa a ki kiran sa da tsani ba, hakan bai ki a bar shi yashe cikin ruwa da rana ba, hakan bai isa a daraja sama fiye da shi ba duk da kuwa in babu shi ba za a isa ga saman ba. Maluma su ne TSANINMU. Duk abin da gobe zai haifar mana dole sai ta sanadinsu. Ku biyo ni mu shiga rayuwar TSANI malam Muhyideen Jibril.
GIDAN AURENA  by Ummu-abdoul
Ummu-abdoul
  • WpView
    Reads 33,714
  • WpVote
    Votes 571
  • WpPart
    Parts 4
Completed on 27th October 2017 #1 in General Fiction more than 10x since 2/10/17, #2 in General fiction 12/09/17 Afaf ta kasance abar so ga kowa tun daga kakanta har zuwa iyaye da yan uwa har dangi da na nesa, nagartanta da kyawawan dabiu ya haifar mata da wannan soyayya wanda ya zarce har zuwa gidan aurenta in da ta zama mafi soyuwa a wajen uwar mijinta. Takan raba dare wajen rokon Allah ya azurta ta da miji nagari, cikin rahamar sa ya sada ta da affan a lokacin da batayi zato ba, ya gwada mata soyayyar da ba kasafai ake samu ba, soyayyar da ta ninku zuwa kiyayya yan kwanaki bayan aurensu..
RUMANATU by Ummu-abdoul
Ummu-abdoul
  • WpView
    Reads 4,144
  • WpVote
    Votes 647
  • WpPart
    Parts 10
Lafiya jari ne kuma dama ce ga duk wani dan Adam
MAKARANTAR MALAM LAMI by Ummu-abdoul
Ummu-abdoul
  • WpView
    Reads 5,052
  • WpVote
    Votes 567
  • WpPart
    Parts 8
Shaye-shaye ya zama ruwan dare a al'umman wannan zamani, sau da yawa sakacin iyaye kan kai yara ga wannan dabia, wasu kuma yanda qaddarar rayuwa ce ta kai su ga hakan. Makarantar Malam Lami makaranta ce tsantsa don ba da kariya ga masu shaye-shaye da kara dulmiyar da su ga wannan dabia
YANKAR KAUNA  by Ummu-abdoul
Ummu-abdoul
  • WpView
    Reads 31,483
  • WpVote
    Votes 3,693
  • WpPart
    Parts 20
"Wanena halan?" Daya daga cikin 'yan union ya tambaya. "Alhaji Usman na hwa. Baka gani ZUNNURAIN ga jikin lambar mota nai. Ko da yake duk kuna yaka hwadi ma magana ko yak'i da jahilci baku tai ba." Daya daga cikinsu wanda dagani direba ne yake fadi. "Allah wadaran naka ya lalace, ashe haka mutuminga yake, ko de cikin hushi yake ne, da azumin rabon abinci yakai kuma duk buda baki ga gidanai 'yan shiyarsu ka buda baki, kwano guda fa, kai 'kila ba shina ba'. "Shina wulai, Alhaji Usman Gwandu, duk fadin garinga anya da mai arziki nai, gashi zaune cikin talakawa, shekaran jiya ya bude gidan mai nai gazauro wolla inaga sati biyu kenan, duk wanda yibba aiki ba dangi nai na ba, haka yake kwansan matasa zuwa Abuja, Kaduna, Zanhwara, Sokwato yana basu aikinyi. Da yake ma yaransa duk mata ne shi yasa" "Inji wa? Wolla yana da Da guda, Umair ba kasanga yake ba, ance ko spain ko ina, nima jiya da natai hwadi ma Alhaji mai dakina ta haihu naji suna zantawa ze dawo jibi, wallahi Rago guda da buhun shinkahwa ya aiko min. Allah saka masa da Alkhairi." "Ameen shi yassa banga laihinsa ba, da ma ya nakada ma shegiya duka muga qaryanta, ita ba arziki ba daga dai ta dan tai boko shike nan tafi qarfin mazan gari. This story was first published on Facebook and whatsApp 2013, and am publishing it here unedited, so don't mind the errors pls
IZZA.. by Ummu-abdoul
Ummu-abdoul
  • WpView
    Reads 6,597
  • WpVote
    Votes 412
  • WpPart
    Parts 7
.
MAFARKIN ABDOUL  by Ummu-abdoul
Ummu-abdoul
  • WpView
    Reads 18,698
  • WpVote
    Votes 1,187
  • WpPart
    Parts 11
Abdoul matashin magidanci ne da ya haɗa da wacce ya sadaukar ma soyayyar sa a kurarren lokaci. Shin soyayyar na kaiwa ga kyakkyawar riba ?