HauwaAUsmanjiddarh
- Reads 1,301
- Votes 24
- Parts 1
Shi da aka aika ya farauto SO
sai ya faɗa a tarkon SO
Mutane biyu masu muhimmanci, mutane biyu da ƘADDARA take son bashi zaɓi a cikin su
Shine duniyarshi
Itace rayuwarshi
Anya idan ya zaɓi ɗaya zai iya rayuwa babu ɗaya?
Tafiya cikin salo na daban, tafiya cikin rayuwar mutane uku...💔
Labarin ya ta'allaƙa ne akan SO!
ƘADDARA...! A koyaushe mu kaji wannan kalmar hankulanmu sukan jirkita, zuciyoyinmu su karye, zukatanmu su raunana, jinin jikinmu ya tsinke, dar-dar da faduwar gaba sukan yawaita a gare mu har muji muna neman fita daga hayyacinmu,
a kowanne yare, a kowacce k'abila wannan kalmar tana da girman gaske da takan iya ya mutsa zuƙata, muna iya kiranta kalma me munin gaske ko akasin haka.. K'ADDARAR kowanne mai rai kenan....!