Uwziri's Reading List
71 stories
SALON IZZAH by saadahalkali
saadahalkali
  • WpView
    Reads 1,886
  • WpVote
    Votes 78
  • WpPart
    Parts 3
*Salon Izzah* Labari ne dake qunshe da wasu 'ya'yan shararun masu kudi, SAFWAN DA SAFNA, dukkansu suntaso cikin kulawa da jin dadi wanda hakan yasa ko wannesu yakeji da kansa, haduwarsu kokadan batazo da dadi ba wanda hakan ya haddasa mumunar tsana a tsakinsu.
Jarabtarmu Kenan by MaryamerhAbdul
MaryamerhAbdul
  • WpView
    Reads 1,525
  • WpVote
    Votes 77
  • WpPart
    Parts 25
"I missed you sister, wallahi duk kewarku nakeyi, mutumin nan kad'ai zai hanani zuwa, amma naji zai tafi umrah, dan Allah yana tafiya ki sanar dani ko ki sanar da Usama" hawayen da take k'ok'arin hanashi fitowa ne ya sauk'o, ta share da gefen mayafinta sannan tace "Jabir Baban kake cewa mutumin nan? Bazaka zo ka nemi afuwar mahaifinka ku rabu lafiya ba Jabir?". Dogon tsaki yaja sannan yace "wallahi wallahi kinga irin maganar nan naki kadai yake hanani d'auka wayanki, Usama da yake biye miki ma wallahi dan na rasa yanda zanyi dashi ne, but nikam hak'ok'ina nawa ya tauye bai nemi afuwata ba? Shine ni dan na tafi na barsa zan nemi afuwarsa? Tsaya ma in tambayeki, wani hak'k'i ne na mutumin nan a rayuwana na tauye ban bashi ba da har zan nemi afuwarsa?". Kai tsaye Maryam tace "kak'i bin umarninsa a lokacin da yace lallai ku dawo gida." dariya yayi yace "wannan kawai? Ni kuma fad'a min, hak'k'ok'i nawa Baba ya tauye min a matsayinsa na mahaifina? Bayan bak'in halin da yake nuna mana? A rayuwana ban taba ganin mai bak'in hali irin nashi ba wallahi, kuma bana fatan in sake had'uwa dashi har abada". Kuka mai k'arfi ne ya kubce wa Maryam na tsananin bak'in ciki da takaici, wannan wani irin rayuwa ne d'a ya siffanta mahaifinsa da kalma mafi muni?.
DUHUN DAMINA... Maganin mai kwadayi by MaryamerhAbdul
MaryamerhAbdul
  • WpView
    Reads 55,112
  • WpVote
    Votes 1,721
  • WpPart
    Parts 7
Rayuwar matasa Sharhi:- Wannan littafi nawa ƙiƙirarre ne, kashi ashirin cikin ɗari, ko ma ince bai kai ba shine gaskiya, kuma akansa na ƙirƙiri labarina. Mas'alar da na ɗauko a yau mas'ala ce mai girma, hakan yasa na ƙirƙiri duk wani SUNAN da na gina labarin a kai, kamar sunan makaranta, sunan kamfani da ma sunayen jaruman littafin. (Note, SUNA kawai, dan duk wani abunda ya samu jaruman littafin, zai iya samuna, ya sameka/ki idan har halin mu yazo iri ɗaya da na su) Mas'ala ce wanda dole wurin isarwa sai ka yi takatsantsan wurin zaɓen kalmomi, hakan ya sa na ke ɗaukan kowacce kalma da na ajje da muhimmanci, gudun samun akasi, wurin neman gyara a samu ɓaraka. Ina fata ku fahimceni, kuma ku bi ni cikin haƙuri har zuwa inda zan ajiye alƙalamina, ban ce kada a dawo dani in na kauce ba, hukunci nake son ku ajje gefe guda, har in samu damar isar da nufina. Idan labarina ya yi shige da rayuwarki/ka, akasi aka samu, ban gina labarina ba sai da na samu cikakken haɗin kai daga wurin wacce ta bani wannan 20% ɗin da na ambata a baya. Nagode, a sha karatu lafiya!
SOYAYYA CE by MaryamerhAbdul
MaryamerhAbdul
  • WpView
    Reads 30,012
  • WpVote
    Votes 1,315
  • WpPart
    Parts 12
"Zan dawo miki pretty, Elmansoor is yours, yours alone, banson kukan nan kina karya min zuciya in kinayi, let's be strong, ba'a tab'a samun abu meh kyau sai ansha wahala. Zan tafi in baki sararin yin duk yanda kikeso dan bazan iya ganinki haka ba Aisha, bazan iya jurewa ba". B'angaren zuciyarsa ya d'aura hannunsa akai ya furta can ciki, muryarsa cike da rauni. "A nan nake jin duk kukan nan da kikeyi, bana son in mutu ban samu Aisha ba, bana son in tafi ban samu damar kasancewa da farin cikina cikin inuwa guda ba, you mean everything to me, ina sonki fiye da yanda kike zato".
•••BADAK'ALA••• by MaryamerhAbdul
MaryamerhAbdul
  • WpView
    Reads 6,915
  • WpVote
    Votes 211
  • WpPart
    Parts 70
Labarin 'yan mata bakwai mabanbanta kowacce da nata BADAK'ALAR, yaya zasu samu bakin zaren kowanne matsala su warware har su samu rayuwa mai inganci?
AKWAI ILLA by MaryamerhAbdul
MaryamerhAbdul
  • WpView
    Reads 19,533
  • WpVote
    Votes 2,246
  • WpPart
    Parts 1
Tafe take tana sanye da riga da siket na atamfa, idanunta na rufuwa a hankali tana kokuwar bud'ewa. Layi take kamar wacce ta sha kayan maye, hannunta rik'e da cikinta tana yamutsa fuska. Kayan jikinta yayi bak'i, ya canja launi daga kalar kore zuwa wata kalar daban tsabar daud'a, farat d'aya in aka ce a k'idaya tsawon lokacin da ake sanye da wannan kayan zaka iya d'iba masa shekara da d'ori, sai dai la'akari da yanayin wacce ke sanye da kayan zai sa kayi tunani akasin hakan. Gashin kanta bud'e yake, k'ura da k'asa turbune ya mamaye ya koma kalar hoda, kitson kanta ya cunkushe ba'a iya ganin tsagunsa. Siket na jikinta a yage, ana iya ganin farin siketin da ke ciki {under wear} wanda ya koma ruwan k'asa dan datti, ga jirwaye da shatin fitsari da ya mamaye. "Argghhh!" Ta furta lokaci d'aya ta d'aga k'afarta na dama.
HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA by MaryamerhAbdul
MaryamerhAbdul
  • WpView
    Reads 6,121
  • WpVote
    Votes 419
  • WpPart
    Parts 19
True life story
KE NAKE SO by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 182,645
  • WpVote
    Votes 12,533
  • WpPart
    Parts 19
#1 sacrifice 21/08/2020 #5 in romance 27/09/2016 "Malam, ka yi kuskure, idan ka na tunanin zaka canza min ra'ayina a minti biyar". "Ko za ki gwada ki gani?" Ya tambaya, yana murmushi, ita ta rasa ma yadda aka yi ya iya murmushi, da dai ba ta ganin hakan a tare da shi. Ta kan dauka shi haka Allah ya halitto shi, duk lokacin da ta samu ganinsa a rayuwarta, sau daya ta taba ganin murmushinsa, ko ba da ita ba, idan tana wurin, baya yin murmushi da kowa. Ta danne zuciyarta, sannan ta zauna, don ita ko ganinsa ma ba ta son yi, bayan abin da ya yi jiya. "Tambaya na ke son na miki. Shin Alhaji Yusuf da ki ke son ki aura, kin tabbata ya damu da farin cikin ki, ko kuwa bacin ranki?" "Wace irin tambaya ce wannan?" Kallonta yake yi kamar zai hadiyeta "Ki amsa min, me ya sani game dake?" Kafin ta ba shi amsa ya ci-gaba. "Shin ya san cewa ba ki son turare mai karfi, saboda ki na da Allergy, ko kuwa ya san idan kin sha ruwan sanyi ciwon Agalawarki na tashi? Ko kuwa kin fi son kasancewa cikin mutane ki yi walwala. Ya san da cewa ba ki amfani da Salary dinki, sai dai ki yi hidima wa wadanda ki ke so?" Ya numfasa cikin murya kasa-kasa ya-ce. "Ya san cewa ba kya son shi?" This is the limit. Ya kai ta makura. "Yaya aka yi ka san duk wannnn a tare da ni?" "Saboda Jidda, na sanki. Na san komai game dake every. Little. Detail. na sani". Ya fada cikin wani yanayi mai tsinka jiyoyin jikin mai saurare. "Well, abinda ba ka sani ba, shi ne ka bata kan batun Alhaji Yusuf, domin kuwa SHI NA KE SO!
DIY COOKERY by zahrah_z_s
zahrah_z_s
  • WpView
    Reads 20,773
  • WpVote
    Votes 572
  • WpPart
    Parts 28
For those who love cooking, check out this book for mouth watering recipes that I'm sure you'll love. The recipes are not totally mine. This book is a compilation of what I watch on Food Channel and my own researches. Don't be afraid to venture and try out new ingredients as substitutions for the already listed ingredients. Cooking is amazing. It is a hobby; a necessity. So why not make it more fun by trying out my recipes? Always at your service. DIY!!