Yet to read❤
166 stories
SAFEENATU by UmmAsghar
UmmAsghar
  • WpView
    Reads 2,850
  • WpVote
    Votes 32
  • WpPart
    Parts 11
A duk lokacin da ƙararrawar ƙaddara ta kaɗa akan wani rubutaccen al'amari to tabbas rayuwa zata yi ta gudu wannan ƙaddarar na binta har sai ta zama wanzajjiya a gareta, rai biyu ne haka ma gangar jikin guda biyu ce, zazzafar soyayya ita tayi sanadin zamowar su abu ɗaya, tayi musu ƙullin goron da sai data tabbatar da samun gundarin farin ciki a tsakanin su duk da tarin ƙalubalen daya cigaba da yi musu kutse a cikin rayuwa, kwatsam wannan rubutacciyar ƙaddara dake bibiyar su ta wanzu a garesu karo na biyu ba tare data basu damar cigaba da kasancewa abu ɗaya ba, zai yi tafiya mai nisa ɗauke da ita a cikin zuciyar shi, yayin da ita kuma zata ci gaba da yin tafiya tare da wata sabuwar ƙaddara a cikin rayuwarta. Shin wannan tafiyar zata zo mata da sabon farin cikin data samu a baya, ko kuma zata zo mata da akasin hakan da zai sa har ta cimma shi a tafiyarta yana maƙale a cikin zuciyarta shima? Domin samun wuɗannan amsoshin sai ku biyo mu sannu a cikin ƙayataccen labarin namu mai suna SAFEENATU!
RAYUWA TA....(ƙaddara ta) by leemaMuhammad826
leemaMuhammad826
  • WpView
    Reads 9,296
  • WpVote
    Votes 243
  • WpPart
    Parts 65
RAYUWA DA ƘADDARA wasu kalmomi ne guda biyu masu sauƙin ambata a baki amma kuma,masu wuyar fahimta. Ko wane ɗan Adam da yanda ubangiji ya hallice shi,ya ƘADDARO yanda RAYUWAR shi zata kasance tun daga haihuwa har ya koma ga mahallicin shi. Mutane da dama na shan matuƙar wahala a RAYUWAR su saboda rashin amsan ƘADDARAR RAYUWA a yanda tazo masu wanda shi kan shi gaba ɗaya RAYUWAR ɗan adam ba'a bakin komi take ba amma ga wanda ya fahimta kenan. Yarda da ƘADDARA mai kyau ko akasin hakan na daga cikin rukunan imani. Saboda haka,a duk halin da bawa ya tsinci kan shi a duniyan nan ya rungumi ƘADDARAR RAYUWAR shi da hannu biyu cike da imani.
RAYUWAR AURENA  by Preety-hammud
Preety-hammud
  • WpView
    Reads 129,125
  • WpVote
    Votes 5,385
  • WpPart
    Parts 63
Labari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni har zuwa gaba dan jin yanda labarin zata kasance, Ana tare,
Auren Katin Kasa(unexpectedly falling❤️🇦🇪) by QueenMarh✍️ by Rukieyfarook
Rukieyfarook
  • WpView
    Reads 6,819
  • WpVote
    Votes 152
  • WpPart
    Parts 29
AUREN KATIN KASA (Akk unexpectedly falling)❤️✨✨ Labarin auren Katin kasa yarjejeniyar aure ne tsakanin wani saurayi wanda rayuwarshi da tasowarshi da career dinshi duk a dubai yayi, General Muhammad taura, (Amar) da kyakyawar yarinya marainiya (Amra) wadda tasha wahalar rayuwa ita da kannenta wajen marikin su kuma babban wa a gurin mahaifinsu, inda ta samu scholarship din karatu zuwa dubai. Amar hamshakin mai kudi ne wanda mahaifinshi Alhaji taura ya bar mashi gado dukda bai damu da dukiyar Tashi ba saboda burinshi na zama babban general army officer a United arab, Amar is a definition of charming, wealthy, handsome and filthy rich guy, babu abunda bashi dashi a duniya saidai ance mutun Tara yake bai cika goma ba, yana fama da cutar oligospermia (rashin kwayayen haihuwa da yawa) inda likita ya shaida mashi chance daya yake dashi na haihuwa idan ya rasa bazai taba haihuwa ba, wannan yasa dole aure ya shigo cikin plans dinshi na rayuwa wanda kwata kwata ada bashi da burin haka. Amra ta shugo rayuwar shi lokaci guda babu zato babu tsammani inda sanadiyar auren yarjejeniyar da sukayi akan ta samu katin kasa a karkashin sa zai bayyanar da wani babban sirrin dake boye shekaru da suka wuce.... Littafine wanda zai ilimantar kuma ya nishadantar sannan zai tabo al'adu daban daban da rayuwar data banbanta da kasarmu ta hausa...❤️😻 Pure loveeeeeee!!!🙈🔞 Hausa-English novel📝
A SOYAYYAR MU by hijjartAbdoul
hijjartAbdoul
  • WpView
    Reads 21,653
  • WpVote
    Votes 309
  • WpPart
    Parts 51
Be tashi ya ga mace a gidan su ba, rayuwar su gaba ɗayan babu mata idan kaga mace a gidan to auro ga akayi har shiyasa mutanen unguwa suke musu laƙabi da gidan GIDAN MAZA, yayin da gidan ya kasance babu wani ɓacin rai acikin sa ya kasance kullum cikin farin ciki suke muddin ba mutuwa akayi ba bazaka taɓa ganin su cikin alhini ba. kwatsam ƙaddara ta sauya musu gidan su da suke alfahari da shi gidan da suke ganin sa tamkar haske a gare su ya dawo babu komai a cikin sa sai duhu. Shin wacce ƙaddara ce wannan ? acan, labarin yana ƙunshe da abubuwa masa tarin yawa ciki kuwa yarda tausayi, sadaukarwa, fasaha wani abun sai an shiga ciki za'a gani.
TSINTACCIYA by nimcyluv
nimcyluv
  • WpView
    Reads 26,362
  • WpVote
    Votes 340
  • WpPart
    Parts 16
Rayuwa mai ɗauke da ƙunci da kuma tarin baƙin ciki, Yayinda hasken wata ke fitowa yana haskaka samaniya, a lokacin ne kuma zuciya keyin zafi da wani irin tafarfasa, Idaniya sun makance dalilin zubar Hawayen da ban san yaushe ne zai tsaya ba, Ina jin inama zan iya kashe kai na! Ko hakan zai sanya zuciyata ta samu nutsuwa da kuma salama, a lokacin da kowa ya kamata yayi farin ciki a lokacin na kejin duniya nayi min zafi, Idaniyan zuciyata na tafarfasa, ban sani ko zan zama dai-dai kamar kowa? Ban san yaushe rayuwa zata juya min daga juyin wainar fulawan da take dani ba, rayuwata ita ake kira da GABA GAƊI rayuwa mara ƴan ci, ko wacce mace na amsa sunanta dana mahaifinta yayinda ya kasance ni kuma ina amsa sunana kana na bashi makari da TSINTACCIYA!
MAFARI..... (HARGITSIN RAYUWA) by Ummuazamm
Ummuazamm
  • WpView
    Reads 531,849
  • WpVote
    Votes 42,248
  • WpPart
    Parts 59
MAFARI...komai yana da farko, komai yana da tushe, komai yana da asali, HARGITSIN RAYUWA kan faru cikin ƙanƙanin lokaci. Duniyar daka saba da ita zata iya birkicewa zuwa baƙuwa a gareka cikin ƙanƙanin lokaci. Tafiya mabanbanciya da sauri a cikin kaddara da dai-daito
A Gidan Mami by Miss_Leeymart
Miss_Leeymart
  • WpView
    Reads 11,118
  • WpVote
    Votes 199
  • WpPart
    Parts 25
Labari ne mai cikeda kalubalen da mahaifiya(mami)ta ke fuskanta bayan rasuwar uban yayanta!yadda zata shiga wani sabon rayuwa wanda bata taba tsammanin ganinta a ciki ba,maimakon ya'yanta su kwantar mata da hankali sai sukeyin tsabanin haka,har suke daura mata laifin talauchin su,bakaken maganganu,da hantarar ta,da wulakanci!Shin yayan da suka wulakanta mahaifiyarsu zasu ga daidai a rayuwarsu kuwa? Ya ya rayuwar jamal,Afaaf,muneera da Faruk zai kasance? Ku biyoni domin jin sauran labarin!
Auren Haďi (COMPLETE) by imaan_am
imaan_am
  • WpView
    Reads 65,270
  • WpVote
    Votes 2,436
  • WpPart
    Parts 22
Tayaya ummi da salman zasuyi rayuwar aure wanda da abaya basu son junan su an hada su AUREN HAĎI ku biyoni muji yadda zata kaya
BAKAR WASIKA by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 29,961
  • WpVote
    Votes 1,136
  • WpPart
    Parts 11
BAƘAR WASIƘA... Mai farin rubutu Ban ce tafiyar mai sauki ba ce. Ban muku alkawarin zallar soyayya ba. Ban ce babu farincikin ba. Kunci, bakinciki da damuwa, sune abubuwan da suka taru suka tare farincikin AMINATU, kalubalen rayuwa bayan wata rayuwar, tabbas akwai kuka akwai damuwa da bakinciki. Labarin Talba, Rafi'a, Laila, Madina, Ramlee, Faruk, Amal da kuma Aminatu. Labarin BAKAR WASIKA, labari ne da zai tabo wani bangare na rayuwar mace, kuma wani bangare na rayuwar al'ummarta da iyayenta... Ina fatar zaku karbe shi kamar sauran, duk na san ba lallai ne yai muku dadi ba domin ba soyayya ce zalla ba, kalubalen rayuwa ne da fadi tashin yar gudun hijira! A ina zata kwana? Wa zai bata masauki? Taya za a fahimce ta har a nade mata damuwarta? Wa zata kaiwa kukanta iyeyenta ko al'ummarta? Ta ina mafarkinta ke tabbatuwa? Ashe bayan wuya akwai wata wuyar, bayan dadi ma akwai wata wuyar, bayan wuya kuma akwai dadi. Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai tsoro a mafarkin da ka gagara farkawa! Ta ina lamarin ya fara? Ina tsakiyarsa da karshe? Yaushe damuwar zata wuce? yaushe bakincikin zai gushe? Sai yaushe hawayen zasu tsaya? Zuwa yaushe ne kuncin zai yanke? Ashe a cikin rayuwa akwai wata rayuwa? A cikin rayuwar ma akwai mutuwa? BAKAR WASIKA... JUANURY 2022