MSKutama87
- Reads 4,019
- Votes 127
- Parts 2
labari ne akan wani madubin sihiri Wanda wannan madubi mallakar Sarkin Bakaken aljanu ne na farko lokacin da aka sana'anta madubin
amma sai aka samu wani hatsabibin boka Wanda ya kware a harkar tsafi da tsatsuba ya tura aljanunsa suka kwato daga hannun sarkin bakaken aljanun
sannan ya soma mulkar gabadaya halittun duniya
har sarkin bakaken aljanun sai da yayi masa mubaya'a sanoda babu yanda ya iya dashi
madubin nan yayi yawo a hannun masarautu daban daban
daga karshe aka samu wani shugaban sarakunan musulmai
ya raba shi izuwa gida bakwai
sannan yasa kowane a cikin akwatin bakin karfe
yasa aka kulle da makullin muftahul zarmal
Wanda wannan makulli kafin kasame shi sai aka keta dajika guda goma sha biyu mafiya hadari a duniya
suka kai akwatu ta farko izuwa Bahur akhlas teku mafi girma a duniya suka kulle inda sarkin aljanun ruwa ke gadinta
akwatu ta biyu suka kaita izuwa bangon duniya na gabas
akwatu ta uku suka kaita izuwa bangon duniya na yamma
ta hudu suka kaita izuwa bangon duniya na kudu
ta biyar ka kaita izuwa bangon duniya na arewa
ta shida suka rufeta adaji na sha daya India kubar take
ta bakwai suka rufeta a daji na sha biyu