Love novel
9 stories
Mata Tagari  by 13deeja
13deeja
  • WpView
    Reads 12,447
  • WpVote
    Votes 701
  • WpPart
    Parts 29
A love story
MASARAUTAR FULANI  by MSKutama87
MSKutama87
  • WpView
    Reads 3,650
  • WpVote
    Votes 134
  • WpPart
    Parts 1
labarine akan zuriyar fulani masu gaba tsakaninsu da Tsananta yaki. kowane bangare daga cikin bangarorin biyu so yake ya mallaki wannan lardi ya zamo shine Babban sarki cikin zuriyar tasu. sa'ili ya zamo Jan ragamar masarautun guda biyu. wannnan ne yasa gaba da hassada ta shiga tsakaninsu gasu dai duk zuriya daya ne amma mara hadin kai. wannnan gaba ta samo asaline tun zamanin da a shekarar alif dubu daya da dari takwas inda yan uwa guda biyu y'ay'a ga sarkin futa toro suka samu sabani sakamakon rikicin sarauta inda har sai da takai an raba masarautar biyu wato futa da toro 😥
MADUBIN SIHIRI by MSKutama87
MSKutama87
  • WpView
    Reads 4,019
  • WpVote
    Votes 127
  • WpPart
    Parts 2
labari ne akan wani madubin sihiri Wanda wannan madubi mallakar Sarkin Bakaken aljanu ne na farko lokacin da aka sana'anta madubin amma sai aka samu wani hatsabibin boka Wanda ya kware a harkar tsafi da tsatsuba ya tura aljanunsa suka kwato daga hannun sarkin bakaken aljanun sannan ya soma mulkar gabadaya halittun duniya har sarkin bakaken aljanun sai da yayi masa mubaya'a sanoda babu yanda ya iya dashi madubin nan yayi yawo a hannun masarautu daban daban daga karshe aka samu wani shugaban sarakunan musulmai ya raba shi izuwa gida bakwai sannan yasa kowane a cikin akwatin bakin karfe yasa aka kulle da makullin muftahul zarmal Wanda wannan makulli kafin kasame shi sai aka keta dajika guda goma sha biyu mafiya hadari a duniya suka kai akwatu ta farko izuwa Bahur akhlas teku mafi girma a duniya suka kulle inda sarkin aljanun ruwa ke gadinta akwatu ta biyu suka kaita izuwa bangon duniya na gabas akwatu ta uku suka kaita izuwa bangon duniya na yamma ta hudu suka kaita izuwa bangon duniya na kudu ta biyar ka kaita izuwa bangon duniya na arewa ta shida suka rufeta adaji na sha daya India kubar take ta bakwai suka rufeta a daji na sha biyu
BAHAUSHIYA.....!? by Mai_Dambu
Mai_Dambu
  • WpView
    Reads 40,144
  • WpVote
    Votes 3,362
  • WpPart
    Parts 22
'YA CE kamar kowa wadda ta taso cikin ɗabi'a da al'ada irin ta BAHAUSHE! "Me ta ke so? Me nene burinta?" Babu wanda ya taɓa tambayarta. Kalma ɗaya ce ko yaushe take hawa kanta "KE BAHAUSHIYA CE! Ko me da ke gareki zai zama irin na Hausawa ne." Tabbas Bahaushiya itace macen da ke shimfiɗar da rayuwarta dan kula da mijinta da yaranta. Itace mace guda da ke killacewa ƙarƙashin igiyar riƙon Ɗa Namiji, da ke kiran shine mafi rinjaye akanta. Sanan Kalma guda da yake nanatawa, Rayuwar 'YA MACE kamar gilashin da ke riƙe a dungulumin hannu ne, ko wani lokaci zai iya faɗuwa dan ya tarwatse ne. Idan aka ci gaba da ganinsa to zai zama shuɗaɗɗen labarin rayuwarsa. Tabbas bayan karatun allo babu buƙatar biyantar da kururuwar zamani wajan tsoma hannayenta dumu-dumu dan janta da tafiya a ƙarƙashin hasken Nasaran da ke da jajayen kunnuwa.
CUTAR KAI  by hauesh
hauesh
  • WpView
    Reads 24,795
  • WpVote
    Votes 488
  • WpPart
    Parts 17
"Ka sake ni ko dole sai nayi rayuwa da kai?" Me zanyi da kai a rayuwata ? " wallahi Dady ya gama cutata tunda ya rasa Wanda zai hadani aure dashi sai kai , bari na Tina Maka idan ka Manta matsayinka... Kai din fa bakowa bane face yaron babana me aikin gidanmu ,dan tsintuwa wanda aka tsinta akan titi Wanda babu da rashi na talauci yasa kanin mahaifina ya taimakawa rayuwarsa ya yantoka daga bauta zuwa yan'ci kai yanzu bakaji kunyar kasancewarka miji gareni ba?" Kalleni sama da kasa Ka gani Aliyu nafi karfinka na karfin aurenka ni ba kalar matar matsiyaci irinka bace . "wallahi yau ko duniya zasu taru ko sama da kasa zasu hade ko zaayi ruwan jini sai ka sakeni domin babu ta yadda zanyi rayuwar aure da kai .. " babu abinda ke damunki sai tsabar jahilci da rashin cikakken ilmin addani, karancin ilimin addini shi yasa kikewa mijin aurenki hk ,wallahi da kina da cikakken ilimin addini da bazaki taba yiwa mijinki na sunnah haka ba ... "kai ne jahili dan talakawa kawai , danging matsiyata waye Kai ? Waye ubanka a duniya ? kazo cikin arziki da bana ubanka ba kana neman kafi ya'yan masu gida karfi .....
MAKAUNIYAR ƘADDARA!! by BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    Reads 12,804
  • WpVote
    Votes 298
  • WpPart
    Parts 9
MAKAUNIYAR ƘADDARA Labari mai cike da cakwakiyar rayuwa. Ta wayi gari da ƙaddarar da batasan mafarinta ba, batasan tushenta ba. Gata da ƙarancin shekaru, gata da ƙarancin gata. Labarin zai taɓo muku zamantakewa, Soyayya, harma da nishaɗi. Bama shiba, a wannan karon duka zafafa biyar sunzo mukune da sabon salo na musamman. Karku bari ayi babuku masoyan ƙwarai abokan tagiya😍😍😍😘🤗.
MADUBIN GOBE by phartyBB
phartyBB
  • WpView
    Reads 86,245
  • WpVote
    Votes 8,547
  • WpPart
    Parts 63
Duniyar Nuratu cike take da duhun da ta mamaye. Rayuwarta tafe take cikin damuwa da ƙaddarar da ta tsinci kanta. Ko yaushe za ta samu haske cikin duniyarta da rayuwarta? Waye gwanin da zai haskaka mata? Yaya Al-ameen? Col.Ahmad? Dr Awwab ko Mufid? 19/11/2020 #8 in love, most impressive ranking🥇 #1 in thriller story #3 in hausa Novels 03/05/2023 #1 in Africa most impressive ranking🥇 #3 in Muslim #11 destiny My new Book GOBE DA NISA Ya fara sauƙa a ArewaBook da Wattpad, da WhatsApp. 07037487278 chat me.
ILLAR RIK'O ('yar rik'o) by AyshaIsah
AyshaIsah
  • WpView
    Reads 26,607
  • WpVote
    Votes 1,619
  • WpPart
    Parts 56
Labarine wanda yake nuni da illolin da rik'o ya k'unsa. A b'angare guda akwai Luba wacce duk halacin da uwar rik'onta tayi mata amma taci amanar ta. D'ayan b'angaren kuma Bintu tare da Uwar rik'onta wacce ke gana mata azaba wanda ya kaiga har ta fara shaye-shaye. Ku biyoni don jin inda wannan labarin zata kaya.
ƘWAI cikin ƘAYA!! by BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    Reads 1,502,282
  • WpVote
    Votes 121,601
  • WpPart
    Parts 106
Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wasu a cikin matsalolin zuminci, gidajen aurenmu, Tsaro, rikita-rikita, harma da ruguntsumi. Kai lamarinfa ba'a cewa komai, mai karatune kawai zai banbance tsakanin aya da tsakkuwar zancena bayan mun tsunduma cikin labarin tsundum