maryamaliyu12's Reading List
13 stories
So koh kiyayya❤️ by Hafsateeeh
Hafsateeeh
  • WpView
    Reads 62
  • WpVote
    Votes 1
  • WpPart
    Parts 1
Soyayya, tausayi, takaici
SIYAAM (JIKAR ME KOSAI) by divaadoveysdiaries03
divaadoveysdiaries03
  • WpView
    Reads 1,417
  • WpVote
    Votes 35
  • WpPart
    Parts 8
Labari akan wata sangartacciya Kuma shagwabbabiyar yarinya me suna SIYAAM wato jikar kakar ta,ita dai wannan yarinya zata kamu da soyayyar wani bawan Allah,Wanda ze kasance yayan ta me suna imaan (Man),Amman Kuma ta ta kaddarar ita ce baya son ta Yana son budurwar da ya hadu da ita me suna huu-dah,sedai ko zuwa gaba ta yuyu ze iya son ta,bari muga yadda abun nasu ze kaaya. shin ko yaya zata kasance,se an biyo mu sannan za'a gani ..
GIMBIYA ZAIR👑👸 by Humaayyrahh
Humaayyrahh
  • WpView
    Reads 395
  • WpVote
    Votes 16
  • WpPart
    Parts 5
Er sarki Zair mai tausayin talaka da bayin ta,nan suka aka musu hadi ita da yarima zafir. Ku biyo ni domin muji ya abin zai kasan ce😍😍
MA'U by Auntyshabash
Auntyshabash
  • WpView
    Reads 280
  • WpVote
    Votes 13
  • WpPart
    Parts 4
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM MA'U 1 Ina zaune can kur'yan daki na na hada kai da gwiwa cike da damu , ni dai ba kuka nake yi ba , sannan ban san mai zan kura kai na a lokacin ba , mutum mutumi ko mutum mai rai , a can gefe kuma ma'u ce take shishshikan kuka , a hankali ta matso kusa dani ta kama hannu na , cike da damuwa tace umma muna don Allah ki yafe min wlh ni fa bana son mal , kuma wlh idan aka matsamin kashe kaina zanyi ko na gudu , duk da cewa dakin babu ishashshen haske amma acikin idon ta na hango zata iya aikata abinda ta fada . MA'U 2 Da sauri na maida hankali gare ta , cikin jin dacin ta nace a kul din ki ma'u kar na sake jin kin furta irin wannan maganar , bana son ki zama mara biyayya wa mal , koba komai yayi miki komai a rayuwa , ma'u ta kara fashewa da kuka , hawaye wani na bin wani a jajayen idanun ta da suka kada suka yi ja kamar garwashin wuta , magana take yi cikin kuka tun tana fada a hankali har na fara gane mai take cewa , na shiga uku ni ma'u mai yasa duniya za tayi min haka , mai yasa na zama daya daga cikin mutane mara sa sa'a a rayuwa . MA'U 3 Haka kawai an raba ni da abin sona , an hadani da wanda yayi jika dani , an sani cin amanar uwata wadda ta soni tamkar yar da ta haifa ,wlh bazan taba yafewa duk wanda yake da hannu acikin wannan zalincin da akayi min ba , sai Allah ya saka min , umma muna ta kwashe ta mari jikake tas tas , baki da hankali ne ma'u iyayen naki kike jawa Allah ya isa , Allah sarki ma'u mai makon taji haushin dukan da nayi mata sai ma ta kara makalkale ni tana umma ta don Allah ki cece ni , ki dauke ni daga gidan nan dama bani da wani gata sai ke .
MANSA MUSA by IsaChairmor
IsaChairmor
  • WpView
    Reads 23
  • WpVote
    Votes 0
  • WpPart
    Parts 1
Labarin tsohon sarki daular Mali wato sarki Mansa Musa wanda a lokaci sa daular ta zama mafi arziki a nahiyar afrika da kuma irin gudumawan da ya bayar har zuwa rasuwansa.
ASEELA COMPLETE by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 22,508
  • WpVote
    Votes 1,704
  • WpPart
    Parts 52
Ƙwarangwal ɗin suna tafe wani irin ruwa mai yauƙi na fita daga gaɓɓan jikinsu tamkar waɗanda aka kunna fanfo ajikinsu, daga kowanne ɓangaren hallita akwai shugabansu wanda shi ne yake kan gaba su kuma suna biye dashi abaya, hannu kowanne shugaba ɗauke yake da wani farin ƙyale da jikinsa yake da ɗishi-dishin jini, ahankali ta fara ɗaga ƙafarta tana ƙoƙarin ja da baya da niyyar guduwa sai dai nauyin jikinta shi ya hana ta gudu har suka ƙaraso inda take, mararta ce ta ɗan karta mata bayanta ya riƙe sannu ahankali ta tsugunna ta duƙa agurin wani irin azababben ciwo na cinta, jeruwa suka yi sahu-sahu sannan suka fara zagaye ta suna faɗin wasu kalmomi da sam bata fahimtar mai suke faɗa, " YAMDUMISA! YAMDUMISA!! YAMDUMISA BISRATIK KUZAR!!!, KIMBASA MIN! KIMBASA MIN!! KIMBASA MIN MAR FAZKINBAT!!! " ( BARKA! BARKA!! BARKA DAI SHUGABA!!!, DAWOWARKU NASARA CE! DAWOWARKU NASARA CE!! DAWOWARKU NASARA CE TARE DA FANSA!!! ) haka suka dinga zagayeta suna maimaita kalmomin bakinsu shugaban ɓangarori biyun masu ɗauke da farin ƙyallen nan suna zazzaga mata wannan kyalen akanta, ciwon da take ji ƙara tsananta yake banda ihu ba abinda takeyi sai kiran sunan KABEER take tana maimaitawa, idan abun ya kuma tsananta ta kuma kiran Kabeer ko Habeebee amma ko gezau basu fasa wannan surutan nasu ba kuma basu fasa zagayeta ba suna yarfa mata wannan farin ƙyallen ba, wani lokacin ma wannan ruwan mai yauƙi na ɗiga ajikinta, ita bata ma san suna yi ba saboda azabar ciwo fatanta kabeer ya kawo mata ɗauki. Ta ɗan ɗauki lokaci ahaka kamar minti talatin ahaka sai ji sukayi kukan jariri alokacin ta galabaita sosai amma ahaka take yunƙurin ɗaukar abinda ta haifa dan neman tsira daga garesu, sai dai kafin tayi wani yunƙuri tuni shugaban ƙwarangwal ɗin nan ya kai hannu yayin da shima shugaban mai mummunar hallitar shima ya kai hannunsa, atare suka suka ɗago jaririyar kowanne ya riƙe hannunta ɗaya yana faɗin, " KAGARSIN BIDA, KAGARSIN BIDA LANBISMA GIRUS " ( KA
DUNIYA MAKARANTA CE. by queenbk2020
queenbk2020
  • WpView
    Reads 27,341
  • WpVote
    Votes 2,417
  • WpPart
    Parts 52
#10 Hausanovel, 15 June 2020. #47 Nigeria june 2021. Duniya Labari, Duniya Makaranta, Duniya Kasuwa, Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa kafa su rusa. Ta rasa me ɗaya zata yi taji sassauci a halin da take ciki, a ɓangare guda kuma ta rasa da wane ɗaya zata ji cikin abubuwa barkatai da sukai mata katutu a cikin wannan duhun dare, shin za taji da halin baro innarta da tayi cikin mawuyacin halin da bata da gata sai Allah? Ko da mutuwar Baba zata ji? Ko za taji da dabi'ar ƴan gidan su ne? Ko ko za taji da hanyar gidan su Naty data ɗinke mata ne? ta jefa ta tsundum cikin wata duniya sabuwa da bata san kowa da komai game da ita ba? Shin ita Bintu wai dama haka rayuwar take da tarin ɗaci da maƙaƙi a wuya? Haka duniyar take da kwazazzabe da tarin ramuka a cikinta? Nan ta ƙara sautin kukanta tana darzar majina. *** Garin yayi tsit baka jin komai sai kukayen tsuntsyen da suke ma Bintu rakiyar da bama tasan da shawagin su ba. Iskar dake ta kaɗa yaloluwar doguwar rigar dake jikinta yana wasa da jelar shukun kanta ma bata san da zaman shi ba, domin duk wasa sensory receptors da neurotransmitters dama duk wasu jijiyoyi dake aikin kai ma ƙwaƙwalwarta rahotanni. Sun tsaya cak sun tafi hutun taƙaitaccen lokaci. *** Tayi tafiya mai tsawo! ita kanta bata san adadin tsowon data ɗauka tana tafiya cikin babin ƙaddarar rayuwarta ba, take kuma aka maido nepa a cikin ƙwaƙwalwarta, tsayawa tayi cak ta dubi gabas da yanma, kudu da arewa amman ba hanyar da tai mata tayin sani.
ZAN SOKA A HAKA by queenbk2020
queenbk2020
  • WpView
    Reads 452,592
  • WpVote
    Votes 25,163
  • WpPart
    Parts 95
#5 tausayi June 2020. #3 tausayi 20 June 2020. #1 munafurci #8 hausa novel. #2 tear drop june 2021.
MULKI KO SARAUTA👑 by Pherty-xarah
Pherty-xarah
  • WpView
    Reads 78,412
  • WpVote
    Votes 2,975
  • WpPart
    Parts 11
👑
❣️QALBINA ❣️ (KECE ZAKI FIDDA NI)  by Aysha_sona
Aysha_sona
  • WpView
    Reads 224,183
  • WpVote
    Votes 9,573
  • WpPart
    Parts 112
Hassan Sooraj Marafa yana da'ya daga cikin hamshakan masu kud'in Lagos. One of the seven billionaire elites dake ruling garin Lagos. Sune ake kira da Asiwaju's of Lagos. Babu wanda ya isa yaja dasu. "Kinfi karfin million d'ari Hibba, ki zauna kiyi nazari akai. Million d'ari, shekara biyar, and your brother is free. It's a contract." Waenan sune kalaman da kyakyawan billionaire Hassan Sooraj ya ra'da mun a kunne. Mutumin dake sa zuciyata hargitsi a duk sanda na daura idanuna akansa. Ina so na kalli cikin kwayar idanunsa nace masa a'a amma taya zan fara? kanina yaci masa bashin naira million da'ya da'ya har d'ari. Bashin dana san har duniya ta na'de bazamu ta'ba iya biya ba saboda mu talakawa ne gaba da baya, ina zamu samu waenan makudan kudi mu biyashi? Abunda yafi daure mun kai yafi bani takaici shine yanda zuciyata kulum take dalmiya cikin kogin sonsa, mutumin da bai daukeni a bakin komai ba sai abar wasarsa. Sunana Hibba Abdullahi, shekarata ashirin da biyu a duniya, ni yar Biu ce, Babur gaba da bayanta, banida kowa banida komai sai kanina, gatanmun shine Allah. Shi kadaine zai iya fiddani daga tarkon wanan kyakyawan attajirin, mai dara daran idanu masu mugun firgitar mun da zuciya. Wanan shine labarin mu.