maina_hafsat's Reading List
79 stories
TARKON AURE,,,!!! by jiddanberry
jiddanberry
  • WpView
    Reads 3,670
  • WpVote
    Votes 129
  • WpPart
    Parts 1
TARKON AURE...-1 Cikin sanda Jamila ta ke tafiya a soron gidan, rike da takalminta. Sannu a hankali kuma tana wuwwurga idanunta a zagayen gurin. Za ta shige kenan cikin gidan ba zato ba tsammani ta ji an riko mayafinta. Gabanta ya yi wani irin yankewa ya fadi. Ta kasa juyowa bare ta yi wani kwakkwaran motsi illa sauke numfashi da ta ke yi a jigace. Birkito da ita ya yi suka fuskanci juna sosai. "A tunaninki za ki iya yaudara ta Jamila? A tunaninki zan sha wahalar kaunarki a banza?" Ya girgiza kai, "Ba zan iya ba! Ba zan iya wasa da wannan damar ba, domin ni ma Dan Adam ne da yake da jini tare da tsoka. Ban da haka tanadin da muka jima muna yi wa yaranmu ba zai tashi a wofi ba!" Jamila ta kasa rike kukan da ya taho mata, duk da ba ta ba shi damar fitar da sauti sosai ba, amma tuni hawaye ya wanke kundukukin fuskarta. "Ka yafe min Jamilu, ka yafe min... Ka yi hakuri mu karbi wannan nannauyar kaddarar. Jamilu ya dinga irgiza kai har ta rufe baki, sannan ya ce, "Na ji... Na ji... Yanzu ya ki ke so a yi?" Ta yi shiru tana sunkuyar da kanta kasa. "Kina nufin na rabu da ke, na daina sonki? Na cire ki a matsayin da na ba ki na zamowa uwar 'ya'yana? Uhum Jamila kenan, kin san Allah daya kenan ko? To wallahi ba zan iya hakura da ke ba, don haka ya kamata ki sani idan ma kin manta ni Jamilu SadeeQ M ba irin wadannan ragwayen mazan nan ba ne da ake kwace soyayya a hannunsu ta ruwan sanyi ba". Ya juya ya koma cikin dakinsa, ya barta tana share hawaye. Ta jima a gurin, yana daga dakin yana jin sautin shesshekar kukanta, wani irin tausayinta yake ji har zuciyarsa, amma ba shi da yadda zai yi, dole ya zage damtse don mallakar makullin farin cikin rayuwarsa. Motsin da ta jiyo daga cikin gidan ya sa ta saurin shanye sautin kukan nata sannan ta fara kokarin saisaita nutsuwarta. "Ah Jamila? Ai gidanku zan je". Amina kanwar Jamilun ta fada bayan ta shigo soron ta ga Jamilar.
AUREN DOLE by Usman_Babura
Usman_Babura
  • WpView
    Reads 573
  • WpVote
    Votes 22
  • WpPart
    Parts 1
AUREN DOLE Zaune nake a katafaren falon gidansu wanda yake dauke da manyan kujeru na Alfarma . Tun karfe 4:30 Pm na yamma nake zaune a falon gidan na shafe kusan mintuna 30 bata fito ba , Ina zaune ina danna wayata saiga kanwarta maryam, ta shigo falon dauke da plate ruwa ne da kofuna akan plate din tace dani ina wuni gashi inji Aunty Aisha , cikin murmushi nace nagode kanwata,ta tashi zata fita nace ina antin taki haryanzu bata gama shirin ba , cikin yanayin murmushi maryam tace haryanzu kwalliya take, nace da ita shikenan nagode. Naci gaba da zama can saina farajin wani irin kamshi mai gusar da tunani , Ashe Gimbiyar tawa ce Aisha take tafe daga kaina da zanyi sai hada ido mukayi, Aisha farace doguwa, kyakykyawa ta sakko da gashi kanta har gadon bayanta , gata mai sanyin murya, ga dumple ta hada komai na kyau da ake bukata ga " ya mace, Cikin rangwada da salo na tafiya, Aisha ta karaso inda nake zaune cikin sanyayyiyar muryata tace yayana kayi hakuri na dade ko? , Cikin Annushuwa da farin ciki nace haba ni banga dadewa ba, tadan sadda kai kasa tayi murmushi, tace yayana amma baka sha ruwan nan ba , cikin shawagaba ta fadamin haka, a yanayi na shauki nace wanna ruwa zansha banga sarauniyar mata ba, muna cikin haka kwatsam saiga daddy dinsu ya shiga falon ganinsa danayi yayi matukar girgiza ni matuka saboda nasan halinsa baya kaunar talaka, hada ido mukayi dashi sai naga ya harare ni , na gaishe shi bai amsa ba, ita ko aisha binmu kawai take da kallo, tayi mamakin abunda mahaifinta yayi min , a lokacin tabi daddy din nata daki domin ta bashi hakuri ta kuma fada masa wanene ni a wajenta, ko saurarenta bai ba ya daka mata tsawa ! Ina falo amma tsawar ta gigita ni, saiji nayi yace wancan dan gidan uban waye kika kawomin cikin gida banace karki kara kawomin diyan talakawa gidan nan ba, kuma ki saurareni da kyau gobe dan Aminina , Zaizo gidan nan ku sasanta kanku,
DUKKAN TSANANI  by Jeeddahtou
Jeeddahtou
  • WpView
    Reads 121,095
  • WpVote
    Votes 9,598
  • WpPart
    Parts 71
Yunwa da ƙishirwar da suka addabe ni ne suka sanya ni kasa bacci ina yi ina farkawa sbd yunwa ta riga da tayi min illah, haka ma innata baccin kawai take yi amma na fahimci ita ma tana jin irin radadin da nake ji, don na lura sosai tunda ta kwanta take juyi. Agogon da ke manne a dakin mu na duba ƙarfe goma dai-dai na dare, har na share na hakura saboda na san matukar na fito diban abinci xan iya samun matsala da innah salamatu, har na hakura naji abin ba mai yiwuwa bane matuƙar muka wayi gari a haka zamu iya samun matsala. daurewa nayi na tashi na don samo mana abinda zamu kai bakin salati, ko da kuwa hakan zai yi sanadiyyar korar mu daga gidan gaba daya. A hankali na lallabo na fito daga dakin innata saboda bana so ita kanta tasan zan fita, indai ta sani sai ta dakatar da ni saboda bata son abinda zai bata mata rai. Kasancewar innata mace ce mai saukin kai bata fiye son abinda zai kawo tashin hankali ba, wannan dalilin ya sanya aka mayar da ita bora saboda hakuri da kawar da kai irin nata. Inna salamatu da yayanta su suke juya gidan duk a abinda suke so shi ake yi. Bakin murhu na nufa a hankali na bude tukunya, tuwo miyar kuka na gani, ba karamin dad'i naji ba saboda rabon da na sanya wani abu a bakina tun abincin safe. tsugunnawa nayi tare da yin bismillah na fara cin tuwon, kafin kace me tuni naci rabinsa, daga nesa na hango ana haskani da fitila a raxane na mike tare da boye hannuna a bayana, sai da ta karaso daf da ni sannan na ga ashe innah salamatu ce, wani kallo ta sakar min wanda ya sanya jikina rawar ɗari, kafin tace min wani abu tuni hawaye sun cika idona, don na san na taro kwai tara tsinana, na janyo wa kaina da innata masifar da Allah ne ya san ƙarshen ta, tsungunawa nayi tare da rokonta ta yafe min
KUSKURENMU ( Completed ) by zulaihatualiyumisau
zulaihatualiyumisau
  • WpView
    Reads 186,997
  • WpVote
    Votes 13,438
  • WpPart
    Parts 95
Labari ne da ya kunshi ilmantarwa, fadakarwa, tare da nishadan tarwa. sannan yazo da sabon salon da yasha banban da sauran labaran da kika/ka taba karantawa.
Alqawarin Kakanni💞🤝 by AminatudearShehu
AminatudearShehu
  • WpView
    Reads 1,812
  • WpVote
    Votes 140
  • WpPart
    Parts 15
Labarin alqawarin kakanni labarine akan wata yarinya da akacika alqawarin aure da ita Ina matuqar godiya ga Allah🤲 da yabani damar wallafa littafinnan📝 Allah kasa ya karbugareku😀 idan kunga kuskure na kugafarceni shidama dan adan ajizine 😒wannan littafi qirairarrene daga zuciyata banyarda wani yajuyashiba😠 taku Amina shehu maman Sadiq.
NA TAFKA KUSKURE..! by Janafnancy13
Janafnancy13
  • WpView
    Reads 18,617
  • WpVote
    Votes 1,531
  • WpPart
    Parts 41
Safwan wai me ka maida ni ne...? na haihu kuma na koma ina maka Renon D"a...? baka isa ba wlh......
BABBAN KUSKURE NA H. @.S ❤️ by HaleemahAbdulah
HaleemahAbdulah
  • WpView
    Reads 742
  • WpVote
    Votes 14
  • WpPart
    Parts 2
Wannan labarin Yana cike da Salo, da yaudara TSAKANIN wata mata da driver ta, Wanda take neman sa ta karfi da yaji, it's short novel but it is full of lesson, Allah yabada ikon karantawa amin.
KADDARA KO SAKACI? by MssHussaynah
MssHussaynah
  • WpView
    Reads 32,880
  • WpVote
    Votes 1,354
  • WpPart
    Parts 19
Wannan kagaggen labari ne kan wata 'yar jami'a da tayi depending kan lecturers domin cin jarrabawarta. wannan ya zamo mata babbar kuskuren da yayi sanadiyar lalacewar rayuwarta........
KUSKURE by AysherAbbakar
AysherAbbakar
  • WpView
    Reads 57,154
  • WpVote
    Votes 2,959
  • WpPart
    Parts 50
Labarin wata yar fulani ce wanda ke rayuwa a cikin daji, na rugar hardo dake abuja, cikin ikon Allah duba da yanda nonon su ke da kyau mahaifinta yayiwa wata hajiya alkawari duk bayan kwana uku yarsa zata na kawo mata nono cikin garin Abuja. Ana haka a hanyarta ta dawowa rugarsu Allah ya hadata da wasu bayin Allah ta temakesu har suka aura mata dansu dake halin tasku da bakin asiri da matarshi ta mamaye shi dashi, ga shi Allah ya zuba mata mugun kishi, ko yaya zata kasance in taji labarin auren, ku biyoni dan jin karin bayani. Taku har a kullum (meerah).
KUSKURE NAH by Oum_Tasneeem
Oum_Tasneeem
  • WpView
    Reads 5,344
  • WpVote
    Votes 163
  • WpPart
    Parts 7
k'irk'irarren labari ne da ya k'unshi mafi akasarin kuskuren da 'yan mata da samari sukeyi na zama da abokan banza,da kuma cin amanar aure da sakayyar da zata biyo tun a duniya,ayi karatu lpy