Rafia
22 stories
BABBAN GORO by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 279,748
  • WpVote
    Votes 21,576
  • WpPart
    Parts 62
NOT EDITED ⚠️ "Kayi kuskuren fahimta Saif, babu soyayyarka a cikin zuciyata ko kaɗan" Kara matsowa yayi kusa da ita, ta yadda tana iya juyo bugun zuciyarsa, yace "Ki kalli kwayar ido na ki faɗa min baki sona ki karya ta kanki da kanki indai har da gaske babu sona a cikin zuciyarki!" Kasa ɗago kai tayi ta kalleshi balle har ta iya furta abunda ya bukace ta dayi. Hakan yasa shi yin murmushi mai sauti, "You see ba zaki iya ba, kin cutar dani Kairat da kika karkata zuciyata zuwa ga Minal bayan kinsan halinta kin kuma san bata dace dani ba, i hate you but i hate her more" Yana kaiwa nan ya kaɓe mata rigarsa ya juya a fusace ya bar mata falon, Sai da taji tashin motarsa sannan ta share hawayen dake idonta ta nufi kofar cikin gida, tana buɗe kofar taga Minal tsaye a bakin kofar da hawaye shaɓa-shaɓa a fuskarta. ®2017 ****************
MEKE FARUWA by AyshaIsah
AyshaIsah
  • WpView
    Reads 89,867
  • WpVote
    Votes 3,694
  • WpPart
    Parts 30
Labarin wata budurwa ne wacce aure yayi mata wahala. Amira kenan 'yar kimanin shekara 24 da hud'u, tayi samari fiye da biyar amma dukkan su sai magana tayi nisa kwatsam sai a nime su a rasa. Amira na da kishir uwa wacce sam basu shi da ita. Ko meke faruwa dake sanadin rabuwan ta da masoya ta? Ku biyo ni don jin inda labarin zata kaya.
Mace a yau!  by Shatuuu095
Shatuuu095
  • WpView
    Reads 215,374
  • WpVote
    Votes 20,609
  • WpPart
    Parts 59
The story is all about Sulaim and Kulthum who were the best of friends, intimate and bussoms. One is from rich family and the other from poor family which affording 3 square meal is a great problem, she has a high self esteem and high standards with lot of dreams which can be said building castle in the air! Let's embark on the journey together and see for ourselves..... It gonna be a good ride I promise. Shatuuu♥️
HIKMAH  by Shatuuu095
Shatuuu095
  • WpView
    Reads 131,453
  • WpVote
    Votes 13,935
  • WpPart
    Parts 51
HIKMAH.... The limping lady
WADATA by Shatuuu095
Shatuuu095
  • WpView
    Reads 116,636
  • WpVote
    Votes 12,637
  • WpPart
    Parts 40
The story of A'isha and Suleiman, the fated lovers who were born be each others company! Hausawa sunce mahakurci mawadaci ne tabbas Maganar take duk Wanda Yayi hakuri bazai Taba tabewa ba, labarin A'isha da Suleiman masoyan gaske Wanda kaddara ta dangi ta rabasu! Yaya labarin zai kasance? Meye zai raba masoyan nan. It's still that Shatuuu.... the writer of Mace A Yau!
Jarabtarmu Kenan by MaryamerhAbdul
MaryamerhAbdul
  • WpView
    Reads 1,526
  • WpVote
    Votes 77
  • WpPart
    Parts 25
"I missed you sister, wallahi duk kewarku nakeyi, mutumin nan kad'ai zai hanani zuwa, amma naji zai tafi umrah, dan Allah yana tafiya ki sanar dani ko ki sanar da Usama" hawayen da take k'ok'arin hanashi fitowa ne ya sauk'o, ta share da gefen mayafinta sannan tace "Jabir Baban kake cewa mutumin nan? Bazaka zo ka nemi afuwar mahaifinka ku rabu lafiya ba Jabir?". Dogon tsaki yaja sannan yace "wallahi wallahi kinga irin maganar nan naki kadai yake hanani d'auka wayanki, Usama da yake biye miki ma wallahi dan na rasa yanda zanyi dashi ne, but nikam hak'ok'ina nawa ya tauye bai nemi afuwata ba? Shine ni dan na tafi na barsa zan nemi afuwarsa? Tsaya ma in tambayeki, wani hak'k'i ne na mutumin nan a rayuwana na tauye ban bashi ba da har zan nemi afuwarsa?". Kai tsaye Maryam tace "kak'i bin umarninsa a lokacin da yace lallai ku dawo gida." dariya yayi yace "wannan kawai? Ni kuma fad'a min, hak'k'ok'i nawa Baba ya tauye min a matsayinsa na mahaifina? Bayan bak'in halin da yake nuna mana? A rayuwana ban taba ganin mai bak'in hali irin nashi ba wallahi, kuma bana fatan in sake had'uwa dashi har abada". Kuka mai k'arfi ne ya kubce wa Maryam na tsananin bak'in ciki da takaici, wannan wani irin rayuwa ne d'a ya siffanta mahaifinsa da kalma mafi muni?.
DUNIYA BIYU!!!  by jeeedorhh
jeeedorhh
  • WpView
    Reads 4,953
  • WpVote
    Votes 270
  • WpPart
    Parts 12
Gefen wasu samari uku da suke ta faman tada hayaki kamar tashin duniya ta rakube, ta mikawa Bangis -mai shagon- kudin hannunta. Tace, "magi mai tauraro zaka bani na talatin da aji-no-moto na ashirin". Ya zuba mata a leda fara ya mika mata. Ta juya, wani daga cikin matasan ya fesar da hayakin daya busa, ya sauka akan fuskarta. Ta sanya hannu tana kore hayakin, tana tarin daya sarketa sakamakon shakar tabar da tayi har cikin makoshinta. Ta bude idanunta dake mata zafi, babu mamaki ma sunyi ja, ta saukesu akan wanda ya aikata mata wannan ta'addanci. Babu abinda ya dauki hankalinta a tattare dashi sai idanunshi, irin idanun dake nuna wuya da tsananin duhun rayuwa da suka gani, suka kuma jure. Duk rashin kunyar mutum, karya yake yace zai tsaga tsakiyar idanun mutumin nan yace zai mishi rashin kunya. Don haka ne yasa ta kame bakinta, 'yar Allah Ya isa din data dauko daga cikinta zata yi, ta tsaya a makoshinta. Ta sadda kai ta kara rabawa ta gefensu ta wuce. Bata sani ba, wani abu game da wannan bakon mutumi da bata taba gani ba, seems nagging. Ta kasa fitar dashi daga cikin ranta. Dai-dai zata karya kwana, ta juya tana kara kallon tiredar. Yanzu ya fito daga cikin tiredar, yana tsaye daga waje. Sai dai kaifafan idanuwan nan nashi suna kanta kyam. Wata irin kunya da faduwar gaba suka rufeta, musamman dan guntun murmushin da taga yana yi mata. Tayi saurin yin kasa da kanta, wani dan karamin murmushi itama yana ziyartar bakinta, kafin ta juya da sauri ta karya kwanar.
A ZATO NA...!  by jeeedorhh
jeeedorhh
  • WpView
    Reads 10,423
  • WpVote
    Votes 255
  • WpPart
    Parts 5
Kallon Umar nayi ina murmushi, "handsome, bari mu wuce ko?". Ya gyada kai, "Ok Sweety, zamu yi waya ko?". Na jinjina kai, "in shaa Allah. See you!". Har ya juya ya tafi, sai kuma ya juyo da sauri, "hey, bari in miko miki fruits". Na daga baki da niyar cewa na gode, Yaya Bilal ya katse ni ta hanyar yiwa motar key. Ya kalli Umar, "ta gode, sauri muke". Da wannan yaja motar. Ina hango Umar ta cikin gilashi yana daga kafada. Munje main gate, na juya na kalleshi, nace "Yaya ko zaka ajiye ni anan kawai, sai in karasa ciki?". Yadda kasan bango, haka ya maida ni, ko kallon inda nake bai yi ba. Bai ma nuna alamun yaji abinda nace ba, sai ma ya karawa motar wuta ya shige cikin makarantar. A bakin hostel ya samu waje yayi parking din motar, na fara yunkurin bude kofar ina jera mishi godiya, "na gode Yaya, a gaida Anty Ameerah". Sai da na fita, ina kokarin maida kofar in rufe, naga yana miko min leda mai dauke da tambarin Bitmas, na kalleshi fuskata dauke da alamun tambaya, kafin inyi magana ya riga ni, "karbi mana, kina bata min lokaci!". Nasa hannu biyu na karba, nace "nagode, Allah Ya amfana". Yace "Ameen" a kaikaice, yawa motarshi wuta ya kara gaba. Ni kuma na shige cikin hostel. ~Wannan littafi tsakure ne kawai. Zaku iya samun cigaban shi a zaurenmu na WhatsApp. Ga duk masu bukatar shiga, akwai bayanan yadda zaku yi ku shiga a ciki.
TAK'ADDAMA by meenaslimzy
meenaslimzy
  • WpView
    Reads 43,068
  • WpVote
    Votes 2,798
  • WpPart
    Parts 46
Hilal Ina fatan wanan fadace fadacen da mukeyi a tsakaninmu ya zamo iyakarsa cikin gidan iyayenmu,baa gidan aurenmu ba saboda Ina matukar tsoron wanan fadan da mukeyi Kar ya kawo sanadiyyar tarwatsewar farin cikin mu,kada hakan ya kasance sanadiyyar rabuwarmu,domin hakan zai zamo sanadiyyar rabuwar mu,domin hakan zai Zama barazana da rayuwarmu domin mu din ruhi daya ne gangan jiki kowa da nasa Ina matukar kaunarka hilal....ta karasa maganar tanayi Masa wani narkakken kallo....
ASABE REZA by lamtana
lamtana
  • WpView
    Reads 73,615
  • WpVote
    Votes 2,369
  • WpPart
    Parts 5
'Kwallina!' Zuciyarta ta buga da wannan kalmar, jan jikinta ta fara yi tana son isa inda ta jefar da kwallin, ji take shi kaɗai ne Zai iya taimakonta, shi kaɗai ne zai iya hana HAMOUD aikata duk wani abu da yake hari. Dafe kwalbar kwallin ta yi tana ƙoƙarin ɗauka. Da shi da gabjejen takalmin ƙafarsa ya ɗora a hannun nata, ya murje, ya muttsike, ya ƙara murjewa har sai da sautin rugurgujewar kwalbar da yatsunta ya fita, ta kwalla gigitacciyar ƙara jin kwalaben sun lume a tafin hannunta, a haka ta ji sautinsa yana faɗa mata abin da ya dakatar da fitar numfashinta. "Idan akwai halittar da ba zan taɓa yafewa a duka duniyata ta ba, to ke ce Fakriyya. Ki yi zina da mahaifina, ki keta alfarmar mahaifiyata, ki zo kuma ki aure Ni? Wane irin kwamcala ce wannan? Ki faɗa mini me na miki a rayuwa da za ki min wannan hukuncin? Ta ya ya ma na aure ki, me ya sa na so ki? Me zan miki?... Lura: (Akwai tarin sarƙaƙiya a labarin, ku taho a sannu, kuna kiyaye duk wani motsi na jaruman)