TARKON AURE,,,!!!
jiddanberry
- مقروء 3,624
- صوت 128
- أجزاء 1
TARKON AURE...-1
Cikin sanda Jamila ta ke tafiya a soron gidan, rike da takalminta. Sannu a hankali kuma tana wuwwurga idanunta a zagayen gurin. Za ta shige kenan cikin gidan ba zato ba tsammani ta ji an riko mayafinta. Gabanta ya yi wani irin yankewa ya fadi. Ta kasa juyowa bare ta yi wani kwakkwaran motsi illa sauke numfashi da ta ke yi a jigace.
Birkito da ita ya yi suka fuskanci juna sosai.
"A tunaninki za ki iya yaudara ta Jamila? A tunaninki zan sha wahalar kaunarki a banza?"
Ya girgiza kai, "Ba zan iya ba! Ba zan iya wasa da wannan damar ba, domin ni ma Dan Adam ne da yake da jini tare da tsoka. Ban da haka tanadin da muka jima muna yi wa yaranmu ba zai tashi a wofi ba!"
Jamila ta kasa rike kukan da ya taho mata, duk da ba ta ba shi damar fitar da sauti sosai ba, amma tuni hawaye ya wanke kundukukin fuskarta.
"Ka yafe min Jamilu, ka yafe min... Ka yi hakuri mu karbi wannan nannauyar kaddarar.
Jamilu ya dinga irgiza kai har ta rufe baki, sannan ya ce, "Na ji... Na ji... Yanzu ya ki ke so a yi?"
Ta yi shiru tana sunkuyar da kanta kasa.
"Kina nufin na rabu da ke, na daina sonki? Na cire ki a matsayin da na ba ki na zamowa uwar 'ya'yana? Uhum Jamila kenan, kin san Allah daya kenan ko? To wallahi ba zan iya hakura da ke ba, don haka ya kamata ki sani idan ma kin manta ni Jamilu SadeeQ M ba irin wadannan ragwayen mazan nan ba ne da ake kwace soyayya a hannunsu ta ruwan sanyi ba".
Ya juya ya koma cikin dakinsa, ya barta tana share hawaye.
Ta jima a gurin, yana daga dakin yana jin sautin shesshekar kukanta, wani irin tausayinta yake ji har zuciyarsa, amma ba shi da yadda zai yi, dole ya zage damtse don mallakar makullin farin cikin rayuwarsa.
Motsin da ta jiyo daga cikin gidan ya sa ta saurin shanye sautin kukan nata sannan ta fara kokarin saisaita nutsuwarta.
"Ah Jamila? Ai gidanku zan je". Amina kanwar Jamilun ta fada bayan ta shigo soron ta ga Jamilar.