yusrayusiey's Reading List
3 stories
AUREN DOLE by Usman_Babura
Usman_Babura
  • WpView
    Reads 573
  • WpVote
    Votes 22
  • WpPart
    Parts 1
AUREN DOLE Zaune nake a katafaren falon gidansu wanda yake dauke da manyan kujeru na Alfarma . Tun karfe 4:30 Pm na yamma nake zaune a falon gidan na shafe kusan mintuna 30 bata fito ba , Ina zaune ina danna wayata saiga kanwarta maryam, ta shigo falon dauke da plate ruwa ne da kofuna akan plate din tace dani ina wuni gashi inji Aunty Aisha , cikin murmushi nace nagode kanwata,ta tashi zata fita nace ina antin taki haryanzu bata gama shirin ba , cikin yanayin murmushi maryam tace haryanzu kwalliya take, nace da ita shikenan nagode. Naci gaba da zama can saina farajin wani irin kamshi mai gusar da tunani , Ashe Gimbiyar tawa ce Aisha take tafe daga kaina da zanyi sai hada ido mukayi, Aisha farace doguwa, kyakykyawa ta sakko da gashi kanta har gadon bayanta , gata mai sanyin murya, ga dumple ta hada komai na kyau da ake bukata ga " ya mace, Cikin rangwada da salo na tafiya, Aisha ta karaso inda nake zaune cikin sanyayyiyar muryata tace yayana kayi hakuri na dade ko? , Cikin Annushuwa da farin ciki nace haba ni banga dadewa ba, tadan sadda kai kasa tayi murmushi, tace yayana amma baka sha ruwan nan ba , cikin shawagaba ta fadamin haka, a yanayi na shauki nace wanna ruwa zansha banga sarauniyar mata ba, muna cikin haka kwatsam saiga daddy dinsu ya shiga falon ganinsa danayi yayi matukar girgiza ni matuka saboda nasan halinsa baya kaunar talaka, hada ido mukayi dashi sai naga ya harare ni , na gaishe shi bai amsa ba, ita ko aisha binmu kawai take da kallo, tayi mamakin abunda mahaifinta yayi min , a lokacin tabi daddy din nata daki domin ta bashi hakuri ta kuma fada masa wanene ni a wajenta, ko saurarenta bai ba ya daka mata tsawa ! Ina falo amma tsawar ta gigita ni, saiji nayi yace wancan dan gidan uban waye kika kawomin cikin gida banace karki kara kawomin diyan talakawa gidan nan ba, kuma ki saurareni da kyau gobe dan Aminina , Zaizo gidan nan ku sasanta kanku,
YAR BABBAN GIDA by DeejahtAhmad
DeejahtAhmad
  • WpView
    Reads 33,819
  • WpVote
    Votes 2,324
  • WpPart
    Parts 29
Na tsaneki at thesame time ina sonki, inajin tamkar na cilla ki ta saman bene na garzaya na taro ki gudun karki fad'a kiji ciwo~ *Alee* ♡ yacce kake nuna min halin ko oho yana ba'kanta raina mutu'ka~pherty ♡ kin gusar da duk wani manufata a kanki~Alee ♡ Na tsaneka bansan sake saka ka a idona~pherty ♡ Ta ya zaka so mutum ka kuma 'ki shi a lokaci d'aya~Alee ku biyoni danjin labarin sar'ka'k'kiyar soyayyar masoyan biyu. 'yar babban gida; labarin yarinya d'aya tilo 'yar masu dashi wacce ta fad'a tarkon soyayyar Alee wanda ya kasance maraya ciki da waje ga uwa uba 'kazantaccen talauci.
MAGANIN MATA by eedatou
eedatou
  • WpView
    Reads 113,043
  • WpVote
    Votes 5,426
  • WpPart
    Parts 55
Labari ne akan wasu mata da suka maida maganin mata sadidan, suke cin k'aren su babu babbaka dan sun sa ka a ransu muddin maganin mata na duniya toh fa babu abunda zai hana su sace zuciyyoyin mazajen su, su maida su tamkar rakumi da akala, babu ruwan su da tsaftar gida da kula da mai gida idan ba anzo harka ba nan ne zaku ga kwarewar su, sun cikin hakan ne aka masu shigo shigo ba zurfi. Koh yaya zata kasance idan suka ankara a kurarren lokaci ?, ku biyo ni dan jin yanda zata kaya a tsakanin su.