MaryamUsmanKogo's Reading List
20 stories
FATU A BIRNI (Complete) by suwaibamuhammad36
suwaibamuhammad36
  • WpView
    Reads 75,718
  • WpVote
    Votes 2,363
  • WpPart
    Parts 18
"I promise you Mami, zan nemo miki ƴar'uwarki a duk inda take a faɗin ƙasar nan. SULTAN promises you that." Sultan ya shiga ya fita, har ya aikata abunda ba'a tsammani domin ya cika wannan alƙawari da ya ɗaukawar mahaifiyarshi, aka yi dace ya gano inda take. Wani abun takaici shine a maimakon ya samu ƴar'uwar Maminshi kamar yanda ya ci buri, sai ya haɗu da ƴarta kwalli ɗaya tak da ta haifa a duniya ta bari cikin ƙauyanci da kuma rashin wayewa. Baƙin cikinshi bai tsaya a nan ba, domin dattijon da yake riƙe da ita a take ya aura masa yarinyar ba tare da ya iya kaucewa wannan mummunan ƙaddaran ba. Ya tafi ya barta ba tare da ya sake waiwayarta ba, ya kuma tafi da wani kaso na zuciyarta ba tare da ya sani ba. Fatu (Fatima) ta ji haushi, sannan tana cikin baƙin cikin tafiyar da mijinta yayi ya barta. Tun tana tsumayinshi tana fatan ya dawo ya ɗauketa, har zuciyarta ta daskare da tsantsar tsanarshi na wofintar da ita da yayi, da kuma banzatar da igiyar aurensa dake kanta. Tayi alƙawarin ɗaukan fansa, ta kuma yi alƙawarin raba tsakaninsu ko da duniya zasu taru su hanata. Sai ta nemo shi a duk inda yake. Ta shiga cikin Birni nemansa, a nan kuma ƙaddara ya gifta tsakaninsu suka haɗu a lokaci da kuma yanayin da basu yi tsammani ba. Shi kuma ganin kyakkyawar baƙuwar fuska mai ɗauke da kamala, ya sashi faɗawa cikin sonta dumu-dumu ba tare da ya shiryawa hakan ba, kuma ba tare da ya gane cewa Matarsa ce ta Sunnah ba, Halal ɗinsa. Me zai faru idan Fatu ta haɗu da mutumin da ta ƙullata tsawon shekaru a yayin da shi kuma yake jinta a zuciyarsa tamkar ruhinsa? Me kuma zai faru Idan wasu sirrikan suka bayyana a lokacin da ba'a shirya musu ba? Fatu mace ce ɗaya mai hali mabanbanta; Fatu- Matar Sultan. Fatima- Budurwar Sultan.
MAKAUNIYAR ƘADDARA!! by BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    Reads 12,905
  • WpVote
    Votes 298
  • WpPart
    Parts 9
MAKAUNIYAR ƘADDARA Labari mai cike da cakwakiyar rayuwa. Ta wayi gari da ƙaddarar da batasan mafarinta ba, batasan tushenta ba. Gata da ƙarancin shekaru, gata da ƙarancin gata. Labarin zai taɓo muku zamantakewa, Soyayya, harma da nishaɗi. Bama shiba, a wannan karon duka zafafa biyar sunzo mukune da sabon salo na musamman. Karku bari ayi babuku masoyan ƙwarai abokan tagiya😍😍😍😘🤗.
FURUCI NA NE by HauwaAUsmanjiddarh
HauwaAUsmanjiddarh
  • WpView
    Reads 55,425
  • WpVote
    Votes 3,770
  • WpPart
    Parts 37
"Baba meyasa kazama boka bokanci fa haramun ne kuma k'arya ne shirka ne Allah baya yafewa mushirki..... "ke Izza ki kiyayeni idan kika nemi d'agamin hankali abin bazai miki kyau ba dan ni zan iyayin komai akan cikar burina na kashe Faida ma balle ke zaki kawo min maganar banza yanzu kinga wani abin da ya Dan ganci bokan ci ne atare dani na dena aikin ki kad'ai zan cigaba dayi shima idan burin mu yacika kika auri daya daga ahalin gidan nan zan bari na tuba meye Allah baya yafewa nide nasan zai yafemin". shiru tayi can ta nisa tace'' to shikenan Baba ance idan zaka sha giya shata dubu ni megaba dayan nake so Nasuru din". dariya yayi yace"shegiya Naira ba babba ba yaro ni kai na naso haka naso ace Nasara kika mallaka amma sam taurari sun nuna ba al'kairi taurarin ku basu hadu ba ba aure a tsakanin ku da Nasara shine na hakura amma ina lefin Aiban ko Agrif din'." tace'' amma Baba nafison Agrif din dan shine akusa da Nasara kaga yafi sauran sanin sirrin komai na dukiyar ". murmushi yayi yace"yanda kike so haka za ayi wa gareni inba keba".
MEKE FARUWA by AyshaIsah
AyshaIsah
  • WpView
    Reads 90,350
  • WpVote
    Votes 3,695
  • WpPart
    Parts 30
Labarin wata budurwa ne wacce aure yayi mata wahala. Amira kenan 'yar kimanin shekara 24 da hud'u, tayi samari fiye da biyar amma dukkan su sai magana tayi nisa kwatsam sai a nime su a rasa. Amira na da kishir uwa wacce sam basu shi da ita. Ko meke faruwa dake sanadin rabuwan ta da masoya ta? Ku biyo ni don jin inda labarin zata kaya.
_Abinda Ke Cikin Zuciya_ by HafsatRano
HafsatRano
  • WpView
    Reads 1,964
  • WpVote
    Votes 74
  • WpPart
    Parts 6
Labarin kauna da sadaukarwa
SARAN ƁOYE by BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    Reads 39,157
  • WpVote
    Votes 991
  • WpPart
    Parts 9
Hummm!!. kowa yaji SARAN ƁOYE yasan akwai cakwakiya kam. SARAN ƁOYE littafine dake ɗauke da sabon salo na musamman da Bilyn Abdull bata taɓa zuwa muku da kalarsaba. yazo da abubuwan ban mamaki da tarin al'ajabi. tsaftatacciyar soyayya mai cike da cakwakiya. ya taɓo wani muhimmin al'amari dake faruwa a zahiri. labarine mai cike da makirci da kutunguylar cakwakiya. Aure tsakanin mabanbanta ƙabilu, ba yankinsu ɗaya ba, ba addininsu ɗaya ba. tayaya wannan aure zai kasance?. ku kasance da zafafa biyar 2021 ta hanyar biyan kuɗi ƙalilan domin samunsa da sauran ma. duk mai buƙata ya tuntuɓi wannan Numbers ɗin. +234 903 318 1070 & +234 903 234 5899.
AMFANIN SOYAYYA COMPLETE  by HauwaAUsmanjiddarh
HauwaAUsmanjiddarh
  • WpView
    Reads 110,250
  • WpVote
    Votes 4,507
  • WpPart
    Parts 31
Labari ne akan 'yan mata 3 wad'anda suka sha gwagwarmayar duniya suka ga bala'i a rayuwar su kala-kala, labarin ya gino ne akan makirci, yaudara, cin mana, fansa
DAMA TA COMPLETE  by HauwaAUsmanjiddarh
HauwaAUsmanjiddarh
  • WpView
    Reads 282,272
  • WpVote
    Votes 9,687
  • WpPart
    Parts 50
Labari ne da baku tab'a jin irin sa ba, matarsa ce bata haihuwa mahaifarta tana da matsana, sai ta sashi ya auri wata yarinya a b'oye babu wanda ya sani daga shi sai ita, akan yarinyar ta haifa musu yara sai ya sake ta, da yarinyar tayi ciki, itama sai ta fara cikin k'arya, suka nunawa duniya yaran nasu ne, ashe k'addara ta riga fata
DIYAR DR ABDALLAH  by Aynarh_dimples
Aynarh_dimples
  • WpView
    Reads 47,013
  • WpVote
    Votes 6,343
  • WpPart
    Parts 32
Zuciyar sa yana mashi wasiwasi, abinda yake gudu shi ke shirin faruwa dashi. Bai taɓa samun kansa cikin wannan yanayin ba. Yanayin da zai zama useless baida amfani. Sai yanzu ya lura da dalilin dayasa ya kasa barci. Ba komai bane illa wannan sabon shafin dake baƙunta sa. A hankali yake mamayansa, ya shammace shi cikin dare. Yanzu gashi yazo yayi kane kane yana kokarin gina muhalli cikin rayuwarsa. Tabbas zuciya batada ƙashi, kuma ba'a kwaɓanta. Amma idan tace zatayi mashi abinda yake tsammani bata kyauta mashi ba. Tayi mugun cutan sa. Ya kamata tayi tunani saboda abinda take so yafi karfin ta. Runtse ido yayi ransa yana mashi ɗaci. Shi dama dukansa akayi da itace zai fi jin daɗi akan raɗaɗin dayake ji cikin ransa. Akwai abubuwa da ke faruwa da bawa wanda baida ikon hanawa. Kamar yadda zuciyar sa take raya masa ga abinda takeso yanzu, idan kuma bata samu ba tabbas zatayi masa tijara. Toh tijara na yaushe kuma, fafur ta hanashi barci. Murmushi yayi na takaici, "akwai ƙura," yace a fili. Dimplicious Empire, ku biyoni sannu a hankali domin jin wannan labari. Love you Fisabillahi ❤️
ƘWAI cikin ƘAYA!! by BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    Reads 1,506,578
  • WpVote
    Votes 121,616
  • WpPart
    Parts 106
Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wasu a cikin matsalolin zuminci, gidajen aurenmu, Tsaro, rikita-rikita, harma da ruguntsumi. Kai lamarinfa ba'a cewa komai, mai karatune kawai zai banbance tsakanin aya da tsakkuwar zancena bayan mun tsunduma cikin labarin tsundum