BiraihabibaUmar's Reading List
8 stories
GOBE NA (My Future) by KhadeejaCandy
KhadeejaCandy
  • WpView
    Reads 165,978
  • WpVote
    Votes 17,200
  • WpPart
    Parts 65
Babu mace da zata labarta yadda wata macen take ji har sai ta taba kasancewa a cikin halin da wacan macen ta kasance. Daga ni sai ire-irena mu ke iya labarta yadda mace ta ke ji idan aka keta haddin yarta ko kuma ita kanta! Ina ma ace yau haddina ni Halimatu aka keta ba na yata ba? GOBE NA... Zawarcin Halimatu... *** *** *** Babu wanda zuciyarsa ta raya masa sai matar nan, sosai ya maida hankali yana kallon gurin da take zaune tare da yaranta, the way ta take sharar hawaye ya kara karafafa zatonsa a kanta, labarin yarsa ya shigo ciki duk kuwa da bata fadi sunansa ba ko sunan yarsa sai dai ta fadi cewar mahaifin yar ya zargeta da kisan yarsa saboda kaddarar mutuwarta ya fada mata, kamar yadda kadarar gushewar hankalin abokin aikinta ya fada a kanta, an keta mata haddi an ketawa yarta, mijinta ya ci zarafinta, a kokarin kwatar hakkin yarta mijinta ya saketa, ga labarin samun aikin kamfanin da tai ya shigo ciki sai dai shi ma bata fadi sunan kamfanin ba..... Wani irin kallonta yake, har ya ji kamar gilashin dake idon sa ya tare ganinsa sai ta ya cireshi yana cigaba da kallonta, ita kuma ta soke kai kasa yana ta latsa waya tana sharar kwalla, wa akai wa fyade? Wacen karamar ko babbar? No wait mutunen da take bawa abincin a kusa da kamfaninsu abokin aikinta ne? Is that why take kokarin kula da shi? Waye mijin na ta? Waya ke bibiyarta? A lokaci daya ya jerowa kansa wadannan tambayoyin, da bashi da amsar su, and he can't take his eyes on her kamar his life defend on her.
Bakuwar Fuska by PrincessAmrah
PrincessAmrah
  • WpView
    Reads 41,672
  • WpVote
    Votes 3,871
  • WpPart
    Parts 50
"Babu wata mace da nake son kasancewa da ita bayan ke Boobah. Babu macen da zan iya rayuwar aure koma-bayanki. Ki amince ki share mini hawayena, na yi alkawarin share miki naki hawayen, na baya, na yanzu, da kuma na gaba wanda ba na ma fatansu, zan kokarta yaki da su ta yadda za su nisance ki, ke da hawaye sai dai na farin ciki, da izinin Ubangijin al'arshi mai girma." Cewar Ishraq Sulaiman, hannunshi dafe da zuciyarshi da ke bugawa da sauri.
ZABEN TUMUN DARE by maryamtalba
maryamtalba
  • WpView
    Reads 17,555
  • WpVote
    Votes 3,310
  • WpPart
    Parts 47
Mafi yawancin lokuta zabin zuciyarmu shi mukafi kanbamawa, Bama duba mai zaije yazo, a kasar Hausa mukan bawa abu guda shaida kuma haka zamuyi ta bibiyar abun nan da shaida marar kyau bazamu taba la'akari da bangare mai kyawu ba na abin, dayawa daga cikinmu kyau shine abin so , komi mai kyau mukeso ba ruwan mu da badinin abin, tuhume tuhume sunyi yawa kan ya'yan masu kudi, da dama ana ganin basu iya komi ba! Daga kan darajta dan adam, tsoron Allah su, zaman aurensu da mu'amalarsu da tarbiyarsu, ko kunsan dan talaka yafi Dan maikudi iya izza da wulakanta dan adam idan ya samu ko duniya a hannunsa, ba duk abinda ka gani bane yake zama dai dai da ko tunaninka. Dayawanmu ZABIN ALLAH bashi bane abinda mukeso, mukanso ra'ayin zuciya da abinda ta kullah, har ya kaimu ga ZABEN TUMUN DARE! Zabi mafi muni a rayuwa.......... Ku biyoni dn jin yadda ZABIN MUHAMMAD KABEER yake kasancewa cikin duniyar tunaninsa.
HANGEN DALA ba shiga birni ba by huguma
huguma
  • WpView
    Reads 85,636
  • WpVote
    Votes 7,227
  • WpPart
    Parts 21
TSUMAGIYAR KAN HANYACE,KAMA DAGA MATAN AURE ZUWA 'YAMMATA
ƘWAI cikin ƘAYA!! by BilynAbdull
BilynAbdull
  • WpView
    Reads 1,503,827
  • WpVote
    Votes 121,607
  • WpPart
    Parts 106
Turƙashi, wannanfa shine cakwakiyoyi ba cakwakiya ba, bamma san yanda zan musalta muku kitimurmurar dake cikin book ɗinnan ba sam, dan wani irin ruɗaɗɗen labarine mai cike da abubuwan mamaki da tarin al'ajabi harma da ban haushi, labarin ya taɓo wasu a cikin matsalolin zuminci, gidajen aurenmu, Tsaro, rikita-rikita, harma da ruguntsumi. Kai lamarinfa ba'a cewa komai, mai karatune kawai zai banbance tsakanin aya da tsakkuwar zancena bayan mun tsunduma cikin labarin tsundum
MARWAN COMPLETE by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 21,733
  • WpVote
    Votes 2,356
  • WpPart
    Parts 35
Safwan yace, " dama inasan ganin Nazir akwai muhimmiyar maganar dana zo da ita nake san mu tattauna " yana gama faɗa mahaifiyar su Nazir ta rushe da kuka sannan tace, " Nazir baya magana hasalima baya cikin hayyacinsa baisan waye ma akansa, kallan yayan Nazir tayi ta ce, " kai je kaxo mai da Nazir " nan take ya tashi ya fice sai gashi da wheel chair da Nazir aciki sai kallan mutane yake yana zubda hawu hannuwansa da ƙafafu gaba ɗaya sun shanye, Safwan na ganinsa cikin tashin hankali yace, " Wannan ne Nazir ɗin mai ya sameshi? " wani sabon kukan mahaifiyar su Nazir ta ƙara sawa, cikin ƙarfin hali yayan Nazir ya fara magana, " aranar da mahaifinmu ya rasu Nazir yace mana zaije gidansu Maryam, to bayan y dawo muna zaune sai gani mukayi ya zabura yana ihu yana cewa bazai kuma ba, sai kuma muka ga yana ta surutai daga haka kawai sai gani mukayi ya yanke jiki ya faɗi, shikenan har yau ka ganshi ahaka kullin magani ake bashi amma ba sauƙi kullin ciwon gaba yake yi. " gaba ɗaya jikin Safwan ne yayi sanyi cikin sumutar baki Safwan yace, " tabbas Marwan ne " karaf yayan Nazir yace, " wai waye Marwan ɗin nan naji lokacin da yake ta sumbatu yana cewa Marwan kayi haƙuri, ko kuma abokin aikinsu ne dan wannan ciwon ba tantama sihiri ne. " Safwan gaba ɗaya tausayi da tsoron halin da Nazir ke ciki ya kama shi.
Zanen Dutse Complete✓ by Aysha-Shafiee
Aysha-Shafiee
  • WpView
    Reads 185,276
  • WpVote
    Votes 25,414
  • WpPart
    Parts 35
#1 in Aure 19/09/2020 #1 in Sarauta 19/09/2020 #2 in Halal Romance 19/09/2020 Ta riga ta san duk wata tarin ma'ana ta k'addara, walau mai kyau ko akasinta. Kamar kowa abinda bata sani ba shine... Me cece tata k'addarar? Yaushe zata fuskance ta? A wane yanayi zata zo? Mai kyau? Ko akasin haka? Wad'annan tambayoyin suke yawo kullum cikin kanta, da su take kwana take tashi, cikin tsumayin lokacin da alk'alami ya bushe akansa. Don wata k'addarar tamkar ZANEN DUTSE ce... Babu wani abu da ya isa ya canja ta!