zee zekari
8 stories
MAHREEN by pen_of_simplicity
pen_of_simplicity
  • WpView
    Reads 549
  • WpVote
    Votes 5
  • WpPart
    Parts 10
labarin MAHREEN labari ne na wata matashiya da aka kashe mata mahaifiyar ta da mahaifin ta tare da yayanta a Kan idon ta kuma qudiri cewa sai ta binciko Wanda ke da alhaki a kisan👇👇👇 *wani harsashin aka Kara harbowa saitin Maher dake kokarin sawa bindigar sa alburushi da wani irin gudu ta karasa gareshi tare da hankade shi da karfi yayinda ita kuma alburushin ya sauka saitin..........."
UMM ADIYYA (Read Full Book On okada) by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 109,676
  • WpVote
    Votes 2,946
  • WpPart
    Parts 7
#6 in Romance 14/04/2017 Tunda take bata taba ganin mugun mutum marar kunya irin Zaid Abdurrahman ba. Ta so ta juya amma ganin su Maami yasa ta fasa ta shigo falon ta gaishe su sama-sama don tare suke da yayanta Saadiq. Har ma yana tambayarta "Ummu A. da fatan dai wadannan basu baki wahala a wurin aikin?" Murmushi tayi har sai da kumatunta ya loba sannan tace "Mutanen da suka bini har da roko saboda na musu aiki ba sau daya ba ba sau biyu ba, ai kaga bazasuyi garajen bani wahala ba, don haka ina aikina cikin kwanciyar hankali with full amenities. Ko ba haka ba?" Ta fada cikin dai murmushinta hade da harde hannayenta saman kirjinta. Idanunsa ya zuba mata tamkar mai karantar duk wani motsi da ruhinta yakeyi, "Saadiq, dole mu kula da Adiyya, saboda ko ba komai ta san yanda take amfani da kwakwalwarta, she's very smart." Ya kare maganarsa cikin murmushi. Tsumewa tayi hade da aika masa kallon banza, "Dole kace kuna kula da Adiyya, banda dan karan wuyar da kuke bani me kuke yi? kullum nayi aiki sai an kwakulo kuskure a ciki, ko me ya kaishi daukana aikin ma tun farko oho." Barin falon tayi zuwa kicin inda tayi zamanta a can taci abincinta. Bata sake bi ta kan falon ba bare ta san lokacin tafiyarsa. Tana kwance kan gado sai aikin sake-sake takeyi abu daya ke yawo a kwakwalwarta, kuma hanya dayace da zata bi don magance wannan damuwar- itace ta bar aiki a AZ IT consultants. A karo na uku! Ko su kadai suke daukan ma'aikatan da suka karanta fagenta ta yafe wannan aikin da irin ukubar da take shiga kullum wayewar gari, "To ma wai aikin dole ne?" Ummu Adiyya ta tambayi kanta, ba tare da sanin dalili ba ta samu kanta tana tsiyayar hawaye. "Duk harda laifin Abba ma yaya za ayi bayan na fada masa komai kuma yace na ci gaba da aiki dasu?" ******
BEENAFAN by marteybee
marteybee
  • WpView
    Reads 24,203
  • WpVote
    Votes 1,065
  • WpPart
    Parts 22
Kamar ni Daddy wancan tsohon zai yi tunanin hadani aure da wancan yar kauyen, banza , shashashan, kwaila,bokanniya ,hatsabibiya,low class,poshless,kaxama,wawiya ,kuma wanda batasan ciwon kanta ba A tsawace daddyn sa yace kai meyasa baka da hankali ne yar tawa kake fadawa haka, kokuwa umarnin mahaifin nawa ne kake so na tsallake toh kasa a ranka auren nan babu fashi kamar ma anyi shi angama ne. Hmmm me kuke tunanin zai faru idan ka duba yanda wannan hadadden first class kuma cikakken likitan saurayi mai ji da kansa wai ake so ama wa auren dole kumama yar kauye and wai hadin kakansa ne. Kubiyo ni domin samun cikakken labarin!
MAIMAITA TARIHI (DANDANO) by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 130,738
  • WpVote
    Votes 6,326
  • WpPart
    Parts 14
***Wannan labarin somin tabi ne. Za a iya samun cikakken labarin akan manhajar Okada cikin watan Janairu, 2021. In sha Allah*** *** #1 aure 9th 01 2021 Tarihi yana kunshe da fuskoki da dama. Banda na wucewar abunda ya shude harda kasantuwar abunda ya shude a rayuwarmu ta yanzu. Sannan a duk lokacin da aka Maimaita tarihi, farashin yana karuwa ne fiye da kima. Hakan ne ya faru da Maryama-Siddiqa a lokacin da ta dauki alwashin bazata bari ta maimaita tarihi ba duk da kasancewa dukkan alamu sun nuna hakan ne yake shirin faruwa. Bayan zaman aure na tsawon shekaru ashirin tare da mijinta Sufyaan Barkindo Sajoh, sun gamu da kalubale wanda ya sa Sufyaan tono abunda ya dade da burnewa yayinda Siddiqah ta jajirce wurin neman 'yancinta daga rayuwar da ta samu kanta a ciki. Sai dai komai ya kwabe musu a lokacin da suka samu masu kalubalantar matakin da suka dauka. Siddiqa ta gamu da abokan hamayyar da suke neman rayuwarta wadanda bazasu tsaya ba har sai sun ga karshenta. Shin zata zakulo kanta daga wannan kangin, ta samu rayuwar da ta yi karfin halin mafarki wa kanta, ko kuwa za a maimaita tarihi ne? Shin wani bangare Sufyan zai zaba idan tura ta kai bango? ***
KE NAKE SO by ummyasmeen
ummyasmeen
  • WpView
    Reads 182,977
  • WpVote
    Votes 12,533
  • WpPart
    Parts 19
#1 sacrifice 21/08/2020 #5 in romance 27/09/2016 "Malam, ka yi kuskure, idan ka na tunanin zaka canza min ra'ayina a minti biyar". "Ko za ki gwada ki gani?" Ya tambaya, yana murmushi, ita ta rasa ma yadda aka yi ya iya murmushi, da dai ba ta ganin hakan a tare da shi. Ta kan dauka shi haka Allah ya halitto shi, duk lokacin da ta samu ganinsa a rayuwarta, sau daya ta taba ganin murmushinsa, ko ba da ita ba, idan tana wurin, baya yin murmushi da kowa. Ta danne zuciyarta, sannan ta zauna, don ita ko ganinsa ma ba ta son yi, bayan abin da ya yi jiya. "Tambaya na ke son na miki. Shin Alhaji Yusuf da ki ke son ki aura, kin tabbata ya damu da farin cikin ki, ko kuwa bacin ranki?" "Wace irin tambaya ce wannan?" Kallonta yake yi kamar zai hadiyeta "Ki amsa min, me ya sani game dake?" Kafin ta ba shi amsa ya ci-gaba. "Shin ya san cewa ba ki son turare mai karfi, saboda ki na da Allergy, ko kuwa ya san idan kin sha ruwan sanyi ciwon Agalawarki na tashi? Ko kuwa kin fi son kasancewa cikin mutane ki yi walwala. Ya san da cewa ba ki amfani da Salary dinki, sai dai ki yi hidima wa wadanda ki ke so?" Ya numfasa cikin murya kasa-kasa ya-ce. "Ya san cewa ba kya son shi?" This is the limit. Ya kai ta makura. "Yaya aka yi ka san duk wannnn a tare da ni?" "Saboda Jidda, na sanki. Na san komai game dake every. Little. Detail. na sani". Ya fada cikin wani yanayi mai tsinka jiyoyin jikin mai saurare. "Well, abinda ba ka sani ba, shi ne ka bata kan batun Alhaji Yusuf, domin kuwa SHI NA KE SO!
AJALIN SO by SURAYYAHMS
SURAYYAHMS
  • WpView
    Reads 625,919
  • WpVote
    Votes 32,416
  • WpPart
    Parts 49
Meet DR MOHAN...and his two weird wives. #Banafsha #mohan #nimrah
ILLAR RIK'O ('yar rik'o) by AyshaIsah
AyshaIsah
  • WpView
    Reads 26,561
  • WpVote
    Votes 1,619
  • WpPart
    Parts 56
Labarine wanda yake nuni da illolin da rik'o ya k'unsa. A b'angare guda akwai Luba wacce duk halacin da uwar rik'onta tayi mata amma taci amanar ta. D'ayan b'angaren kuma Bintu tare da Uwar rik'onta wacce ke gana mata azaba wanda ya kaiga har ta fara shaye-shaye. Ku biyoni don jin inda wannan labarin zata kaya.