usmananinu's Reading List
144 stories
NANA AMINATU 2022 by UmmuDahirah
UmmuDahirah
  • WpView
    Reads 15,672
  • WpVote
    Votes 914
  • WpPart
    Parts 56
Maganganun ta tamkar saukar kibiya take jin su a zuciyarta duk idan ta tuna, suna sukan ta su hana ta sukuni, suna tarwatsa ta su saka ta taji ita ƙasƙantanciya ce wacce bata kai ɗin ba kamar yadda take cewa, tana ganin baƙin kanta a koda yaushe a wacce bata kai ba, ko kaɗan bata taɓa saurara mata ba, ya za'a yi ta dena kallon kanta ta daban a cikin mutane yayinda take tuna duk wata kalma ta ɓatanci da take bin ta dasu a kullum ranan duniya? tun sanda ta buɗe idanuwanta da wayon ta take jin waɗannan munanan kalaman da ke tarwatsa mata duk wani farin ciki da jin daɗin ta. Sai dai kuma a duk sanda take jiyo kalaman sa sai ta ji ƙwarin gwiwa har ta kalli kanta a wacce ta kai kuma ta isa, ashe akwai ranan da zata yi farin ciki haka? Akwai ranan da wani zai iya yabon ta har ya nuna mata tana da matsayi fiye da sauran Mata? She can't believe that... Shi ne Mutum na farko da yake faɗa mata kalaman da idan ta ji su take ganin ta kai Mace, ta kai Mace cikakkiya ba wacce ta rako Mata ba, a kullum ganin kanta take yi a bata kai matsayin ba, ita bata kai Macen da zata iya fitowa ayi gwagwarmaya da ita a matsayin ta na ɗiya Mace ba. Shin wane ne shi wannan ɗin? Tabbas Ƙaddara kowa da irin tasa, wasu tana zuwar musu da sauƙi wasu kuwa akasin hakan, ba wai don wani ya fi wani bane a wurin Allah hakan ke faruwa, a'a, sai dai don Allah na gwada ko wanne bawa ta hanyar ɗaura masa tashi ƙaddaran, walau me sauƙi ko akasin sa, ko wanne bawa da tashi ƙaddaran kuma kowa yana fatan ace ya tsallake ƙaddaran da Allah ya ɗaura masa. Haka itama NAANA AMINATU tayi fafutuka a cikin rayuwar ta domin ta ga ta cinye nata ƙaddaran da ta kasance babba a gare ta. Na san Kuna so ku bibiyi labarin ta domin ku ji mene ne ya faru a rayuwar ta, to ku bi Ni sannu a hankali Zan warware muku komi a cikin sauƙi, ina fata labarin zai zame muku darasi a cikin rayuwa.
GIDAN GANDU by SAKHNA03
SAKHNA03
  • WpView
    Reads 38,260
  • WpVote
    Votes 2,460
  • WpPart
    Parts 39
Gidan gandu,haka kowa ke kiran gidan mu saboda yawan iyalan gidan tun daga kan iyaye da kakanni zuwa kan yaya duk muna zaune ne acikin gidan gandu. saidai abu daya shine, duk wani kalar hali da kake nema inkazo gidanmu to ka samu ,kama daga shaye shaye ,dabanci sata,koma dai menene,abinda zai baka mamaki shine duk iskancin mutum a gidan hatta dabbobin gidan suna shayin rashin mutuncina tun daga kan iyaye kuwa har yayansu babu wanda hantar cikinsa bata kadawa idan yasan ya shiga gonata ,nice nan SAMEEMAH!!!!...................Tofahh.
WASA FARIN GIRKI(cigaban gidan gandu) by SAKHNA03
SAKHNA03
  • WpView
    Reads 3,130
  • WpVote
    Votes 50
  • WpPart
    Parts 1
Paid book#200 naira ......Me baba yake nufi?,shikenan wai na hakura saina zauna lafiyah a gidan sameer?!! Inaaa hakan bazai taba yi wuwa ba,dan barikin sajojin dayake takama dashi saina maidashi tamkar kango,barekuma gidansa kam sai yayi daya sanin sakani a cikinsa. Domin natsani zama da dawani a rayuwata bare kuma aure.......hmmmm muje zuwa yanzu za'a fara wasan.
ƳAR ME MAGANI  by realfauzahtasiu
realfauzahtasiu
  • WpView
    Reads 3,527
  • WpVote
    Votes 75
  • WpPart
    Parts 13
labarin wata yarinya marainiya da danginta suka tsaneta saboda tunaninsu na itan ba mutum bace, ƙaddara ta sake haɗa ta da wani ɗan mafiya, shin yaya rayuwar Hindu zata kasance a hannu Imran?
RUƊIN DUNIYA! by UmmuDahirah
UmmuDahirah
  • WpView
    Reads 15,521
  • WpVote
    Votes 707
  • WpPart
    Parts 77
The lives of some sisters. Haƙiƙa Ina matuƙar son kuɗi, ji nake yi idan babu su kamar bazan iya rayuwa ba, ɗaukar da nayi musu su ne suke kare mutunci, sannan kuma su ne suke sa wa a yi maka soyayya, ashe ba haka ba... Tabbas kuskure. nayi su da dama, amma ina ganin kamar ana sake ba ma mutum damar sake kura-kuran sa, ban taɓa sanin wata soyayya ba, face soyayyar da na maka....
SIRRIN MIJINA by 68Billygaladanchi
68Billygaladanchi
  • WpView
    Reads 257,395
  • WpVote
    Votes 17,600
  • WpPart
    Parts 33
Ko kad'an Nafeesah bataso idanta yake shiga cikin na Dr. Hisham, takasa gane inda zuciyarta ta dosa, menene amfanin wannan baqar rayuwar datakeso ta jefa kanta aciki, menene amfani wannan baqar zuciyar tata, ina amfanin rayuwar da shed'an yayi qawanye acikinta,menene amfanuwar ta akasantuwar ta musulma indai har tana dauke danigiyar auren wani amma zuciyar ta na kwad'ayin waninsa!!! Runtse idanta tayi sannan ta sauke kanta a k'asa a sarari take furta "A uzu billahi mina shaid'anirrajeem" Dr. Hisham dake kan aikin shi na duba patients ya d'ago ya kalleta cikin mamaki,amma beyi magana ba kasancewar ya saba ganin hakan atare da ita...kokarin dauke idanta take daga bakinshi yanda yake wurgawa mara lapian tambaya bakin nashi na qara fixgar hankalinta ci takeyi tamkar ta manne bakinshi da nata wuri d'aya!!!!!!!!! Dafe kanta tayi dake barazanar tsage mata a zuci tace "Laifin zuhra ne data kame sirrin mijinta daga gareni dabata jefani cikin wannan tashin hankalin ba..inama ace banzo duniya ba.
Kaddarata by Z11AMN
Z11AMN
  • WpView
    Reads 3,820
  • WpVote
    Votes 76
  • WpPart
    Parts 16
labarin wata yariya Wanda iyayenta Suka bar duniya a sanadin wani saurayi da ya bige amminta ta mutu shima babanta bakin ciki ya kashe shi,akwai Wanda ya tsaya Mata a lokacin da take niman taimaka saidai kashe maihafiyarshi tayi sanadin rabuwarsu shi Kuma Habibilah ya dawo rayuwarta Amma Bata San shine ya kashe mahaifiyarta ba shin ya abin zai kasance ku biyoni a littafin kadarace inda Zaku karanta labari Mai tab'a zuciya soyyaya sadaukarwa,d'aukan fansa da nishadin
K'AZAMA SHALELE by mumies122
mumies122
  • WpView
    Reads 9,690
  • WpVote
    Votes 348
  • WpPart
    Parts 10
🎍🌹🎍 *K'AZAMA SHALELE* (Maman Mamy) *MARUBUCIYAN Raggon miji*📚FIKRAR📝MARUBUTA✍🏻* Gajeren Labari *Labari/Rubutawa:* HUSSAINI 80K 1⃣ Yarinya ce wadda bata wuce kimanin shekaru ashirin da biyu ba, fara, doguwa, kyakkyawa tak'in k'arawa, wuyanta kamar murk'in lema, gashin kanta har gadon baya. Ga duk wanda yaga irin zubin halittar da Allah yayi mata da iya kwalliyar da tayi sai yaji kamar ya sace ya gudu da ita, sunanta Shalele sunane wanda aka fi saninta da shi. Ta iya kwalliya, hakan yasa a duk sa'ilin data fita samari suke rige-rigen isa wajenta da zummar soyayya, tana da samari masu yawan gaske dan duk cikin fad'in unguwarsu babu wadda take da yawan samarin da ita take da su. Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, duk wannan kyawun da iya kwalliyar da take da shi a iya waje ne cikin gidansu kuwa ba'a cewa komai domin kuwa ta ciri tuta wajen k'azanta ta ko ina hakan yasa ta zama lamba d'aya a fagen k'azanta cikin 'yan uwanta, idan kuwa akace za'a had'a ta da k'azaman da suke waje to babu shakka tabbas nan d'in ma ita zata zama zakaran gwajin dafi dan ita zata lashe gasar. Shalele takan yi kwanaki uku zuwa hud'u jikinta be ga ruwa ba, dan ita da tayi wanka ta gwammace ayi mata duka tafi ganewa dak'ale a wanke fuska da hannu da k'afa koda kuwa ba lokacin sanyi ba, k'afafuwanta kullum da safa sabida tsabagen kaushi daya mamaye ko ina a tafin k'afarta har zuwa saman k'afar sai dai ba wanda yasan hakan face 'yan gidansu da kullum suke tare. Fad'an mahaifiyarta a kullum be wuce na "ki yiwa kanki karatun ta nutsu Shalele iya yina ina miki fad'a na gaskiya, k'azanta ba abar so bace ba komai ake miki gudu ba illah lokacin da kikai aure baki san irin gidan da Allah zai kaiki ba ta yu da wata matar zaki sha w
DR. HISHAAM   (Completed✍️) by safiyyaa_z
safiyyaa_z
  • WpView
    Reads 60,545
  • WpVote
    Votes 2,637
  • WpPart
    Parts 15
Strange Love story
ZAMAN HOSTEL by muneeraahh
muneeraahh
  • WpView
    Reads 58,531
  • WpVote
    Votes 1,030
  • WpPart
    Parts 25
Zaman hostel labari ne wanda yake nune ga yanda wasu yan mata ke lalaciwa sanadin zaman hostel ba'anan kadai ya tsaya ba yatabu wasu bangarori da yawa na rayuwa da yanda za'a ma'gance matsalarso