ahmadrahma200's Reading List
24 stories
WATA FUSKA by 68Billygaladanchi
68Billygaladanchi
  • WpView
    Reads 206,666
  • WpVote
    Votes 17,323
  • WpPart
    Parts 50
Sosai take a tsorace, ganin komai take tamkar a mafarki ji takeyi tamkar ma ace bata rayuwa a doron qasar, se zare ido takeyi tana kallon qungurmin dajin datake ciki, gata a d'aure ba hanyar guduwa, tayi iya kacin qoqarin taga ta qwace kanta amma sam abun ya faskara ya kuma tunzura, tunaninta d'aya yanzu idan wani naman daji yazo ya cinyeta ya zatayi kokuma wani mugun aljani gashi ko dankwali babu a kanta, babban tashin hankalinta shine sallar dabatayi ba, tun shekaranjiya da aka gudo da ita rabon datae sallah!!!! zata iya d'aukar kowane hukunci amma banda na hanata sallah!!! yaya zatayi da tulin sallolin dake kanta? batada halin yin koda taimamane sabida a d'aure tamau take to meye mafita?!!!!!!!
FATU A BIRNI (Complete) by suwaibamuhammad36
suwaibamuhammad36
  • WpView
    Reads 75,478
  • WpVote
    Votes 2,363
  • WpPart
    Parts 18
"I promise you Mami, zan nemo miki ƴar'uwarki a duk inda take a faɗin ƙasar nan. SULTAN promises you that." Sultan ya shiga ya fita, har ya aikata abunda ba'a tsammani domin ya cika wannan alƙawari da ya ɗaukawar mahaifiyarshi, aka yi dace ya gano inda take. Wani abun takaici shine a maimakon ya samu ƴar'uwar Maminshi kamar yanda ya ci buri, sai ya haɗu da ƴarta kwalli ɗaya tak da ta haifa a duniya ta bari cikin ƙauyanci da kuma rashin wayewa. Baƙin cikinshi bai tsaya a nan ba, domin dattijon da yake riƙe da ita a take ya aura masa yarinyar ba tare da ya iya kaucewa wannan mummunan ƙaddaran ba. Ya tafi ya barta ba tare da ya sake waiwayarta ba, ya kuma tafi da wani kaso na zuciyarta ba tare da ya sani ba. Fatu (Fatima) ta ji haushi, sannan tana cikin baƙin cikin tafiyar da mijinta yayi ya barta. Tun tana tsumayinshi tana fatan ya dawo ya ɗauketa, har zuciyarta ta daskare da tsantsar tsanarshi na wofintar da ita da yayi, da kuma banzatar da igiyar aurensa dake kanta. Tayi alƙawarin ɗaukan fansa, ta kuma yi alƙawarin raba tsakaninsu ko da duniya zasu taru su hanata. Sai ta nemo shi a duk inda yake. Ta shiga cikin Birni nemansa, a nan kuma ƙaddara ya gifta tsakaninsu suka haɗu a lokaci da kuma yanayin da basu yi tsammani ba. Shi kuma ganin kyakkyawar baƙuwar fuska mai ɗauke da kamala, ya sashi faɗawa cikin sonta dumu-dumu ba tare da ya shiryawa hakan ba, kuma ba tare da ya gane cewa Matarsa ce ta Sunnah ba, Halal ɗinsa. Me zai faru idan Fatu ta haɗu da mutumin da ta ƙullata tsawon shekaru a yayin da shi kuma yake jinta a zuciyarsa tamkar ruhinsa? Me kuma zai faru Idan wasu sirrikan suka bayyana a lokacin da ba'a shirya musu ba? Fatu mace ce ɗaya mai hali mabanbanta; Fatu- Matar Sultan. Fatima- Budurwar Sultan.
Khadija by hijja11
hijja11
  • WpView
    Reads 2,482
  • WpVote
    Votes 101
  • WpPart
    Parts 3
Fitowa tayi daga daki tana sakowa daga saman bene a hankali take tafiya sabida takalmin kafan ta nada dan santsi, wayan ta take dubawa tana murmushi cikin ta ta shafa tana cewa kamar ba 6 months ba cikin yayi kato ko yan biyu zan haifane, ji tayi santsi ya kwashe ta sauri tayi ta kike hannun matattakalan benan kanta daidai ta tsayuwan ta taji an han kado ta tabaya hantsilawa tayi takan cikin ta fado takuma gangarowa ta jiya takuma kifewa ta cikin hantsilawa tayi ta fado ta kanta, Ta dauki dan mintina bata motsa ba tana kwance anan hannun ta na dama ta fara motsawa ji tayi kaman an sa guduma ana buga hannu ji tayi ma gaba baya jikin ta ana kwankwatsa shi, cikin ta dataji yana wani irin juyawa, jinin daya zibo a idon ta daga goshin ta yasa ta kasa kude idon ta da kyar ta iya bude su dishi dishi take gani gashi ta kasa magana sabida a zaban da takeji rufe idon tayi ta kuma budewa kokari take taga ta daga koda hannun tane takasa da kyar ta iya jan hannun ta ta rike cikin ta. Daga nesa takeji ana cewa yima za ki goge man ki dauke takalmin kar agani Dagewa tayi iya karfin ta tana kiran habib, mama amma maryan yaki fitowa hannun data rike cikin ta daga shi tayi da kyar san nan ta dafa shi dagawa tayi zata juwa taji cikin ta ya murda kafan ta yayi kara Waiiiyooo Allah tace wani irin zafi taji daga kan ta har kafafuwan ta kasa juyawan tayi cikin ta kaman ana caccaka mata wuka jiyawa yake yana kullewa sabida azaban da take ji, Kantane ya fara jiyawa duhu ne ya rufa mata idon, sunan ta taji ana kira Kha..di..ja...Khadija............ kha...... kan ta kuma kokarin budewa ta suma.
AMRAH NAKE SO! (Completed✅) by PrincessAmrah
PrincessAmrah
  • WpView
    Reads 192,012
  • WpVote
    Votes 17,465
  • WpPart
    Parts 79
"Sickler gare ta, kuma ku kuka ja mata." Ta yi shiru daga nan, dafe da goshinta, tana jin yadda kanta ke sara mata. "A kullum dad'a wayar wa mutane kawuna ake game da awon genotype, amma wasu sun kasa ganewa, sun kasa sanin darajarsa."
SARKIN GARIN MU by ibraheemaysha20
ibraheemaysha20
  • WpView
    Reads 232
  • WpVote
    Votes 33
  • WpPart
    Parts 9
......What the? Ya fada ranshi a matukar bace yana kallon fuskar Computer da ke gaban shi "KING OF THE KINGS episode 10" baro baro aka rubuta ga wasu tarin bayanai a kasa"ya rasa yanda zai bullowa alamarin,yarinyar ta kunna shi da yawa..juyawa yayi da rinannun idon sa ya kalli fadawan sa da ke tsaye a falon suna masu jiran umarnin sa..daya daga cikin su ne yace 'Allah ya taimake ka ka bamu sati inshaAllah zamu nemo ta duk inda take a fadin kasar nan.. Tsawa ya daka mai "shut up damn it! Tun yaushe kuke binciken kun Kasa samo ta ..ni da kai na zan nemo ta and I promise sai ta gane kuskuren ta sai tayi Dana Sanin abun da take aikatawa...now get out of my sight old fellows" ya fada hade da tsawa again..da sauri suka watse suka bar mishi falon suna fadin 'Allah ya huci zuciyar ka' ya bi su da harara hade da dukan iska yana huci "wait and watch bitch I will make sure you regret this" .... Shin me yake faruwa ne haka? Waye wannan mai nuna isa da ikon? Shin yarinyar da ake nema wace ce? Ku biyo ni a wannan tafiya muji yanda abubuwan suke.. SARKIN GARIN MU Labari ne me taba zuciya da ya kunshi abubuwa da dama.. @Aysha Ibraheem
Qawaa Zuci......(Labarin Zuciya) by ummAssidiq
ummAssidiq
  • WpView
    Reads 848
  • WpVote
    Votes 38
  • WpPart
    Parts 3
Iyalan Professor AlMustapha Haske Ahali na hausawan usli me dauke da 'yan uwa masu tsantsar qaunar juna game da riqon Addini..Cikinsu kuwa akwai wata yarinya me dauke da raayi na musamman wanda yasha banban da na kowa.khadija tana da raayin riqo me karfi na ganin cewa dukkanin mafarkinta sun zamo gaskiya a matsayinta na mace me tsananin so da sanin 'yan cin kanta. A matsayinta na mace matashiya Khadeejah ita kadai ce tafara taka matsayin da wata 'ya mace ta taka a familynta...kuma a jajircewa da kuma nacin son ci gaba a rayuwa ne ya kawota ga matsayin da take kai a yanzu . Dai dai lokacin da ta kusa kai gaci wajen cimma burinta da zai Sadata da rayuwar data jima tana wa kanta mafarkin steps in a man who ruins everything that she built from all these years. Duk kuwa da irin tsantsar tsana da kiyyaya da takeyi masa a zuciyarta some how Qaddarar rayuwa brings them both together. A Nasa bangaren kuwa Engr Dr Habib ya sallamawa kansa wata rayuwa ta nishadi a tun bayan Rasuwar matarsa ta sanadiyyar cancer shekara guda kacal da aurensu.To wace rayuwa zeyi mai dadi bayan Maryam bata a duniya???? A beautiful tale of HausaFulani Unfulfilled love story. Stay tuned.
So, karya ne! (Love is a lie!) by Sheikhul-Zaman
Sheikhul-Zaman
  • WpView
    Reads 78
  • WpVote
    Votes 3
  • WpPart
    Parts 1
~Based on true life story~ Sabeeha da take zaune kan kujera cikin qunci da radadin zuciya tana kallonsa kawai tayi wuf ta miqe tare da furta: "Wai meh kake nufi ne? Are you trying to make mockery of my feelings for you ne?" Haneef yai dariya yace: "Relax Sabeeha babu wani love fah, duk haukane! Itama Ays...." Tas! Ta wankeshi da mari, dagowa yayi zai rama, cikin fushi amman a karo na farko a rayuwarsa, da idanuwansa suka sauka a fuskarta zuwa jikinta. Ya fara lura tabbas Sabeeha ba qaramar kyakyawar mace ba, ga uwa uba diri, Allah ya albarkace ta dashi. Nan take kuma ya tuna ah inda yake, tuni ya sauke hannunsa ya zuba mata na mujiya. Kallonsa kawai tayi tare da furta "Aysha din banza! Aysha din wofi komai aysha! Tohm, damn you and listen well to this, idan so karya ne, idan so haukane..." Bata qare kalamanta ba sukaji jiniya tare da jin anbude babban gate din gidan. Jerin convoy din motocin mijinta, Major General M.M Muqaddas suka shigo farfajiyar. "Wai daman yana gari? Ko daman gidan nan akwai CCTV cameras acikinsa" tambayar da tayiwa kanta kenan! Tare da umartar Haneef wanda yake qoqarin neman hanyar guduwa: " Sit down malam!!" Daram, Haneef ya zauna ba shiri tare da zancen zuci: "subhanallah! ni yau nakawo kaina mayanka ta. Shegu mata ashe su daman zasu kasheni!"...
AMSOSHIN TAMBAYOYINKU 2 by sameehasusman
sameehasusman
  • WpView
    Reads 59,980
  • WpVote
    Votes 1,381
  • WpPart
    Parts 200
JANABA TA SAME NI, BAN YI WANKA BA SAI HAILA TA ZO MINI, YA ZAN YI WAJEN YIN WANKA
SAKAMAKO.......THE OUTCOME by mrs_Avbdool18
mrs_Avbdool18
  • WpView
    Reads 19,628
  • WpVote
    Votes 1,242
  • WpPart
    Parts 39
Labarin husna, labari mai cike da darussa masu dinbin yawa, labarine na kaddarar wata yarinya Wanda mahaifinta shine yakashe mahaifiyarta a sanadiyar haka tagudu tabar gidan Dan itama yana barazana da Tata rayuwar, da tafiyarta tagamu da iftilai kala kala Wanda daga karshe tayi aure, kaddara da zuciya tasata takashe mijinta, ayayinda ta kamashi da mai aikinta suna aikata alfasha a karshe kuma taga SAKAMAKON abin da ta aikata...........THE OUTCOME Kukarata Don jin cikakken bayanin labarin da ke #ilmantarwa #fadakarwa #tunatarwa #nidashantarwa. It's a story of Destiny were tears are going to be shed. Asha karatu lpia.
A JINI NA TAKE by Aishatuh_M
Aishatuh_M
  • WpView
    Reads 70,289
  • WpVote
    Votes 3,093
  • WpPart
    Parts 12
Labari ne daya kunshi masarautu biyu; Masarautar Katsina, wacce take cikin Nigeria da kuma Masarautar Damagaran, wacce take cikin Kasar Niger. Labarin yayi duba ne da rayuwar Yarima Bilal, wanda rashin magana da miskilanci ya kanja ya shiga tarun matsaloli, wanda hakan yake haifar mashi da auren Zeenah Kabir Muhammad. Diyar Bafade da kuma baiwa. Me zai faru a rayuwar auren da aka hada miskili da kuma masifaffiya? Wanda dama tun farkon haduwarsu da masifa aka fara har yakai ga ya kure hakurinta ta sharara mashi maruka biyu? Shin ko zasu samu zaman lafiya kuwa? Bilal wanda ya kasance zuciyarshi a kulle take tun bayan rasuwar mahaifiyarshi zai bude ma Zeenah ita? Ya rayuwa zata basu bayan Zeenah ta fada soyayyarshi sai kwatsam Juwairiyya ta kunno kai? Wane hali Bilal zai shiga a lokacin da Fulani ta bankado wani tsohon sirri dake tsakaninsu? Fulani fah? Wacce take uwar gida kuma mai kula da hidimomin Masarautar Katsina gaba daya? Zata rufe sirrin data gano tsakanin Zeenah da Bilal dan gujewa tarwatsewar farin cikinsu? Abu daya ne zai kai ga na biyu, wanda har Bilal zai tsinci kanshi an mashi shamaki da Masarautar Katsina, hakan zai dangantashi da Masarautar Damagaran! Ku biyo Yar Malumfashi domin jin yadda labarin zai kasance.