princeessAfnan's Reading List
5 stories
JARIRI COMPLETE by AmeeraAdam60
AmeeraAdam60
  • WpView
    Reads 17,595
  • WpVote
    Votes 1,086
  • WpPart
    Parts 25
A daren ranar da suka koma da daddare kimanin karfe biyun dare Inno ce ta fito fitsari ahanyarta ta dawowa, ta hango ƙaƙanin abu na tafiya idan yayi gaba sai ya dawo baya ya rangwaɗa kai gefe. A ɗan tsoroce Inno ta ce, "Toooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani da tsohon daren nan" ta ƙarasa magana tana haskashi da ƴar fitilarta. A zabure ta ja baya ganin jaririn Nusaiba ne tumɓur ko wando babu, washe mata baki yayi ya dafe ƙeya yana wani irin layi kamar wanda yasha ya maku, cikin wata irin murya ya cafe irin maganar Inno yace, "Tooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani da tsohon daren nan" tana faɗa yana wani irin tsalle kamar zai faɗo kan Inno, wurgar da butar tayi saboda tsoro ta fara gudu. Tsalle yayi ya caɓe zanin Inno har ya taɗe ta ta faɗi da rarrafe ta dingan rarrafawa tana ƙwala ihu, lokacin da ta ƙarasa ɗakinsu tuni ta daɗe da wurgar da zani daga ita sai ɗan fatarinta.
FATAWAR MUSULUNCI by Yaqubbby
Yaqubbby
  • WpView
    Reads 15,213
  • WpVote
    Votes 438
  • WpPart
    Parts 183
• _*Makunnin Sha'awar 'Ya mace:*_ • _Matakin farko da Uwargida za ta bi don budo sha'awarta shi ne, ta fara yin zurfaffen tunani game da ita kanta, yanayin ta da yanayin halayen ta da yanayin shau'ukan cikin zuciyar ta. Ta yi kokari ta fahimci mene ne yake danne mata sha'awar ta? In da hali ta samu littafi ta rubuta dukkanin dalilin da take ganin su ne ka iya rufe mata makunnin sha'awar ta, da kuma abin da take ganin zai kawar da su har sha'awar ta ta bude. Na sha fada a cikin wannan fili cewa, ita 'ya mace dole sai tana cikin jin dadi da kwanciyar hankali da natsuwa daidai gwargwado sun saukar mata a zuciya kafin makunnin sha'awar ta ya iya kunnuwa.
THE FORTY RABBANA  by Oumzaynab
Oumzaynab
  • WpView
    Reads 480
  • WpVote
    Votes 181
  • WpPart
    Parts 40
بسم الله الرحمن الرحيم The Famous Duas from the Holy Quran 40 RABBANAH
DU'A AND AZKAR  by Oumzaynab
Oumzaynab
  • WpView
    Reads 8,483
  • WpVote
    Votes 420
  • WpPart
    Parts 10
Authentic Dua's from the Qur'an and sunnah for all occasions to be implement on our daily routine.
HISNUL MUSLIM  by Oumzaynab
Oumzaynab
  • WpView
    Reads 16,887
  • WpVote
    Votes 426
  • WpPart
    Parts 85
Littafin Hisnul Muslim, Addi'o'i da suka dace da Sunnar Annabi. FALALAR ZIKIRI Allah Madaukakin Sarki ya ce: Fazkuriniy Azkurkum Washkuruliy Wala Takfuruni. Ku ambace ni zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce mini" [Bakara, aya ta 152]. Ya'ayyuhallazina Amanuzkurullaha Zikran Kathiran. Ya ku wadanda suka yi imani ku ambaci Allah ambato mai yawa". (Ahzab aya ta 41). Wazzakirinallaha Kathiyran Wazzakirati A'addanlahu Lahum magfiratan Wa'ajran Aziyman. Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambatonsa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma". [Ahzab, aya ta 35] Wazkurrabbaka Fiy Nafsika Tadarru'an Wakhiyfatan waduwanaljahri Minal kawli Bil'guduwi Wal'asali Walatakun Minalgafiliyna. Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai kankan da kai da tsoro, ba da daukaka murya ba (saka-tsaki) tsakanin asirtawa, da bayyanawa, da safe da marece, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu". [A'araf, aya ta 205]. Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; "Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, kamar misalin rayayye da matacce ne". (Duba Sahihul Bukhari tare da Sharhinsa Fat'hul Bari (11/208). Muslim ya rawaito shi da lafazin; 'Misalin gida da ake ambaton Allah a cikinsa, da wanda ba a ambaton Allah a cikinsa kamar misalin rayayye ne da matacce". (1/539).) Kuma ya ce: "Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Srkin da yake mallakar ku, kuma mafi daukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku daga ciyar da zinariya da azurfa kuma mafi alheri gare ku da ku hadu da abokan gabanku ku rika dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? Suka ce ka ba mu labari. Ya ce: Ambaton Allah Madaukaki". (Tirmizi (5/459), da Ibn Majah (2/1245). Duba Sahih Ibn Majah (2/316). Da Sahihul Tirmizi (3/139).)