UmmuDahirah
- Reads 6,790
- Votes 611
- Parts 55
Duk yanda zan fasalta muku yanda take ta wuce nan, yarinya ce sangartacciya da iyayen ta suka Ιata ta da gata tun tana tsumman goyo, sun Ιau son duniya sun Ιaura mata, ba sa son kukan ta bare fushin ta, hakan yasaka ta taso babu kwaΙa take yin duk abin da taso.
yarinya ce me bala'in taurin kan tsiya, idan har tace zata yi abu, to, babu wanda ya isa ya hana ta, idan kuma tace baza ta yi ba babu wanda ya isa yasa ta tayi, ko kaΙan bata damu da rayuwan kowa ba, rayuwan ta kawai ta sani, duk wanda ya taka ta, to, tana ΖoΖarin Ιaukan mataki, bata da sabo ko kaΙan idan har ba da mahaifin ta ko Yayan ta ba.
ku biyo NI ku ji me zai faru da rayuwan ta, yarinya me tsatstsauran ra'ayi.