Narrnarhhbukar001
_Ta ya kishiyar da ta shuka sharri ta yi tunanin girbar alkhairi_
_Ta ya kishiyar da ta tarwatsa farincikin abokiyar zamanta ta yi tunanin kwanciyar hankali zai aureta_
_HAFIZA natsattsiyar yarinya, mahaddaciyar Al'qur'ani da ta taso cikin kaɗaicin yayyenta uku da suke hannun kishiyar mahaifiyarsu,tana gana musu azaba sakamakon hatsabibiyar mallakar da ta yi ma Ubansu. Wani gigitaccen al'amari ya tilasta HAFIZA komawa wurin kishiyar mahaifiyarta sakamakon bangon da take kallo a matsayin majigini ya rushe. Kishiyar mahaifiyarta ta ci gaba ta soya musu tsakuwa a hannu yayin da ta keɓe yaranta tana shayar da su ruwan zuma. Sau biyu kishiyar mahaifiyarta na zama silar fasawan auranta ganin za ta fi yaranta jin daɗin gidan miji. Sai dai Ubangiji ya yi ikonsa,domin ta yi dacen miji ɗaya tamkar dubu wanda ya doke na sauran mazajen 'yan'uwanta,ya yi musu fintinkau a komai._
_A tunanin HAFIZA ta yada ƙwallon mangoro ta huta da ƙuda,sai dai bata sani ba tirka-tirkar da ke cin gidan auranta ya linka wanda ta baro a gidansu sau dubu. Bahagon gida ne mai cike da chakwakiya kala-kala masu matuƙar yawa da ban tsoro. Sai dai faɗin hausawa da suka ce WUYA BATA KISA. Silar zuwan HAFIZA gidan ɓoyayyun sirrikan da ke ɓoye sama da shekara ashirin da biyar sun bayyana a idon duniya. Kar na jaku da yawa🥰 ku biyo tsaftataccen alƙalamina don yi muku jagora zuwa duniyoyi biyun da tunaninku bai je ba🥰_