shuraih99
Labari mai cike da ban al'ajabi, rudani, mamaki da almara
Labarin soyayya da aljana,
DANDANO
Ni da na kwanta cikin dakina kwatsam sai farkawa nai na tsinci kaina a tsakiyar kungurmin jeji
Babu gida gaba babu gida baya
Tsananin rudewar danayi ya sanya na zaci ko mafarki nake hakan yasa na dankarawa hannuna cizo
Radadi gamida zugin da suka ziyarci hannuna lokaci guda su suka tabbatarmin ba mafarki nake ba
Na mike a rude ina karewa jejin kallo
Tabbas wannan ba irin jejin garina bane na fadi a zuciyata
Domin kuwa irin wannan jeji shi nake gani a talabijin ................