rahmakabir
Ga labarin SO DA MANUFA. Starring Fatima Batul, Nadiya da Sameera 'yar yayi uban gayya Adnan Husain. Sunan labarin kadai ya fallasa asirin hikayar sai dai sanin farko, tsakiya da karshe sai kun kasance cikin alkalamina. So shine tushen komai, sai dai Namiji shine tulabalin ginin matsalar, amma kuma mace itace samuwar ginin amma a bisa zamowar ita ce matsala ga mace 'yar uwarta har yake kaiwa matakin karashen ginin Namiji ya kuma tare a ciki bisa abinda so ya gina masa. Labarin a dunkule yake sai ku shirya dan akwai kalubale mai tsayawa a zuciya musamman ga macen da wannan kaddarar ta fada mata. Rahma Kabir MrsMG ce